Bai wa jihar Kogi kudi a yanzu rashin gaskiya ne - PDP

A jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, kudi ya haifar da takardama tsakanin jam`iyyar APC mai mulki da babbar jam`iyyar hamayya ta PDP.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya nemi biyan jihar Kogi wani tsohon bashi da take bin gwamnatin tarayya da ya kai naira biliyon goma na wasu ayyukan tarayya da gwamnatin jihar ta taiwatar.
Amma jam`iyyar PDP ta ce bai kamata a biya kudin a wannan gabar da ake shirin yin zaben gwamna a jihar ba, tana zargin cewa ana so ne a baiwa gwamna yahaya Bello kudin yin magudin zabe.
Tuni gwamnatin tarayya ta mika bukatar biyan wannan kudi gaban majalisar dattawan Najeriya, kuma wannan kudi da ake magana akai sun kai naira biliyon goma.
Wani jigo a jam'iyyar PDP a jihar Honarabul Baba Sule ya shaida wa BBC cewa idan APC ta taki gaskiya mai ya sa tuntuni ba a biya kudin ba.
Ya kara da cewa ''gwamnan da zai yi zabe nan da wata guda za a dauki wadannan makudan kudade a ba shi, wani salo ne a bashi kudin da za a yi maugudin zabe da bai wa 'yan bangar siyasa''.
Baba Sule ya ce a baya tsohon gwamnan jihar Kogi Idris Wada an taba batun ba shi kudi amma da ya ke lokacin zabe ne sai aka dakatar da nasa, dan haka idan gwamnati za ta yi adalci bai kamata a bada kudin ga gwamnatin Yahaya Bello ba.
Amma a nata bangaren gwamnatin jihar ta bakin sakataren yada labaran jihar Mohammed Onogwu ya ce sam kudin ba shi da alaka da zabe.
"A watan Janairun wannan shekarar , lokacin da aka gabatar da irin wannan bukatar domin jihar Bachi da Kogi su amfana ai babu zaben gwamna a jihar Kogi. Wasu `yan majalisa `yan jam`iyyar PDP ne suka hana ba da kudin."
Saboda haka idan muka samu kudi za mu samar da abubuwan more rayuwa ne'', inji Mohammed Onogwu.











