Tsananin zafi ya sa 'yan wasa janyewa a Qatar

Sama da kashi uku na matan da suka shiga gasar tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya, sun gagara kammala gudun yada kanin wani sakamakon tsananin zafin da ake yi a kasar Qatar.
Duk da cewa da tsakar dare ake gudanar da wasan, amma yanayi ya kai maki 32 a ma'aunin Selshiyos.
Tuni ashirin da takwas daga cikin mata 'yan wasan sittin da takwas sun sanar da janyewa daga gasar, ya yin da mai horas da 'yan wasan kasar Habasha ya ce babu wani gudun yada kanin wani da za a yi a kasarsa cikin wannan tsananin zafin.
Cikin 'yan wasan da suka fice daga gasar akwai 'yar Birtaniya Charlotte Purdue, ya yin da wadanda suka shirya gasar suka yanke shawarar ci gaba duk da fargabar da aka nuna kan yanayin bai dace da masu gudun yada kanin wani ba.
'Yar wasan tsere ta Kenya Ruth Chepngetich ce ta zo na daya, duk da cewa da sassarfa ta kai bantenta da karin rabin sa'a saboda tsananin zafin da ya so karya lagonta.







