Saura kwana 27 zaben 2019: Bayani kan 'yar takara Obiageli Ezekwesili #BBCNigeria2019

Obiageli Ezekwesili tsohuwar mataimakiyar shugaban Bankin Duniya ce, sannan kuma ta rike mukaman ministan ilimi da kuma ma'adanai a Najeriya.

Sabanin sauran manyan 'yan takara, Mis Ezekwesili kirista ce wadda ta fito daga yankin kudancin Najeriya, kuma jam'iyyar da take yin takara a karkashinta karama ce idan aka kwatanta da tasu.

Ta jagoranci kamfe na Bring Back Our Girls wanda ya ja hankalin duniya baki daya bayan da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace 'yan mata dalibai 300 daga garin Chibok na jihar Borno da ke Arewa maso gabshin Najeriya.

Masana na ganin cewa kwarewarta kan tattalin arziki baiwa ce ga Najeriya sai dai rashin goyon baya daga manyan 'yan siyar kasar ka iya kawo mata tsaiko.

Ta yi alkawarin cewa in dai aka zabe ta za ta sauya fuskar tattalin arzikin Najeriya daga dogaro da man fetur da kuma samar wa matasa aikin yi.

"Yar shekara 55, Mis Ezekwesil tana hankoron zama shugabar kasa mace ta farko a Najeriya duk da cewa abu ne mawuyaci a kasar da maza suka yi kaka-gida.

  • An haife ta ran 28 ga watan Afrilun 1963
  • Ta rike mukamin babbar ministar sufuri daga Yuni 2005 zuwa Yunin 2006
  • Ta rike mukamin babbar ministar Ilimi daga Yuni 2006 zuwa Afrilu 2007
  • Ta yi mataimakiyar shugaban Babban Bankin Duniya bangaren Afirka daga 1 ga watan Maris din 2007 zuwa 2012
  • Ta jagorancin kamfe din nan na Bring Back Our Girls don kwato 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace
  • Mijinta fasto ne a babban Cocin Redeemed Christian Church of God