Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsawa ta hallaka mutum 10 a Mozambique
A kalla mutum 10 sun mutu bayan da tsawa ta fada kansu a yankin tsakiya da arewacin kasar Mozambique.
Wannan lamarin ya biyo bayan mamakon ruwan sama da tsawa da ta hada da iska mai karfi da aka yi a kasar ne.
Yawancin mace-macen sun auku ne a karshen makon jiya, musamman a lardunan Sofala da Zambeziya da Manica da tete da kuma Niassa.
Fiye da iyalai 500 sun rasa muhallansu bayan da ruwan ya tafi da gidajen nasu da aka gina da kayan da basu da nagarta.
Augusta Maita ce shugabar cibiyar bayar da agajin gaggawa ta Mozambique, ta ba mutane shawara su rika daukar matakan rigakafi:
A lokacin da ake tsawa da walkiya, bai kamata mutane su fake a karkashin bishiyoyi ba, kuma wadanda ke cikin ruwa sai su yi hanzari su fice.
Damina kan fara daga watan Oktoba a Mozambique, kuma ba ya karewa sai an kai karshen watan Maris.
A shekara ta 2000 ne kasar ta fuskanci matsalar ambaliyar ruwa mafi muni a sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya zuba.
Lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum 700, kuma fiye da mutum miliyan daya suka rasa muhallansu.