Takunkumin Amurka a kan Iran ya soma aiki

Iraniyawa na zanga-zangar nuna adawa da takunkuman Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Iraniyawa na zanga-zangar nuna adawa da takunkuman Amurka a Tehran

A yau takunkumin da Amurka ta sake kakaba wa Iran bayan janyewar shugaba Donald Trump daga yarjejeniyar nukiliyar kasar ke soma aiki.

Mista Trump ya ce takunkumin da suka kakaba wa Iran na da karfi sosai, kuma shi ne irinsa mafi karfi da aka taba kakaba wa wata kasa.

Sai dai duk da haka za a daga kafa ga wasu kasashe 8 domin su ci gaba da sayen mai daga Iran.

Kasashen dai irin su Burtaniya da Faransa da Jamus da kuma Rasha da China sun ce za su ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar kasar.

A jiya lahadi Iraniyawa sun fantsama a kan tittuna a wata zanga-zangar nuna adawa da takunkuman.

Kafar yadda labaran gwamnatin kasar ta ce sojin Iran din za su gudanar da atisaye kwanaki biyu ranar litinin da talata domin nuna irin karfin sojin kasarta.

A shafinsa na twitter, jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khameni ya ce wannan abin kunya ne ga Amurka da kuma tsari na demokradiyya na masu sassaucin ra'ayi.

Amurka dai na fatan ganin wannan takunkumi ya sake gurgunta tattalin arzikin Iran.

Jagoran addiniN Iran Ayatollah Ali Khameni ya ce Amurka ba za ta mamayesu ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jagoran addiniN Iran Ayatollah Ali Khameni ya ce Amurka ba za ta mamayesu ba