Najeriya ce ta hudu a yawan kashe al'umma

Sojijin Najeriya
Bayanan hoto, Rikicin Boko Haram da na barayin shanu ya haddasa asarar rayuka da dukiya a Najeriya

Kasashen Najeriya da Syria da Afghanistan da Iraki da kuma Yemen su ne a sahun gaba a jerin kasashen da aka fi samun kashe-kashen al'umma sanadiyyar rikice-rikice a cikin shekara biyar da suka gabata.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wani rahoto na cibiyar bincike ta Brookings Institute da ke Amurka.

Rahoton ya sanya Najeriya a matsayi na hudu, da yawan mutane wadanda aka kashe da suka kai 20,497.

A baya-bayan nan dai Najeriya ta fuskanci karin hare-hare da ake zargin kungiyar Boko Haram da kai wa, da fadan da ake bayyanawa a matsayin na manoma da makiyaya.

Barista Audu Bulama Bukarti, malami ne a jami'ar Bayero da ke Kano, kuma manazarci a gidauniyar Tony Blair Foundation da ke birnin Landan ya ce rahoton ya na yi wa Majalisar Dinkin Duniya hannun ka mai sanda ne.

Kan kasashen da ya kamata su mayar da hankali a kai dan ceto al'ummarsu, maimakon wasu kasashen na daban da suke gudanar da aiki.

Bukarti ya kara da cewa, ita kanta gwamnatin Najeriya babban tashin hankali ne a gare ta a ce cikin shekara biyar an kashe sama da mutane 20,000 a kasar, inda nan ma ya kamata ta zage damtse dan ganin ta bai wa 'yan kasar kariyar da ta dace.

Rikicin Boko Haram, da na barayin shanu, na daga cikin matsalolin da Najeriya ke fama da su a dan tsakanin nan wanda kuma ke janyo mutuwar fararen hula da asarar dukiya.