Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Habasha da Eritrea sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya
Kasar Saudiyya ta taka rawar gani wajen kawo sulhu tsakanin makwabtan kasashe Habasha da Eritrea, wadanda suka shafe fiye da shekara 20 suna rikici tsakaninsu.
Firai ministan Ethipia Abiy Ahmed da takwaransa na Eritrea Isaias Afwerki sun sanya hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Jiddah.
Bikin ya faru ne a gaban Sarki Salman na Saudiyya da babban sakatare janar na MDD, Antonio Gutteresh da kuma Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman.
A wajen bikin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla, Sarki Salman ya karrama shugabannin Eritrea da na Ethiopia da lambar girmamawa ta Sarki AbdulAziz, lamba mafi daraja da daular Saudiyya ke bayarwa.
A makon jiya ne kasar ta sanar da wani shirinta na bunkasa rawar da ta ke takawa a nahiyar Afirka.
Kuma a dalilin haka ne ministan harkokin kasashen waje na Saudiyyar, Adel al-Jubeir ya ziyarci kasashe 18 na Afirka.
Saudiyya ta kuma dauki nauyin taron koli tsakanin kasashen Larabawa da na Afirka da zai gudana a 2019 bayan taro na musamman tsakanin Saudiyya da kasashen Afirka, duk a badi.
Wannan matakin na Saudiyya wani yunkuri ne da ta keyi domin rage karfin fada aji da kasashen Iran da Turkiyya ke da shi musamman a yankin arewa maso gabashin Afirka.