Ana zaben shugaban kasa a Mali

Asalin hoton, Reuters
'Yan kasar Mali za su kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa da ake fatan zai kawo karshen rikicin siyasa da na masu tada kayar baya da aka shafe shekara shida ana yi.
Shugaba mai ci, Ibrahima Boubacar Keita, mai shekara 73 da haihuwa, wanda ya dare karagar mulki shekara biyar da ta gabata da Soumaila Cisse ake sa ran za su fafata cikin 'yan takara 24.
Za a bude rumfunana zabe daga karfe 8 na safe, a kuma rufe su da karfe 5. Akwai akwatunan zabe fiye da 23,000 a fadin kasar, kuma mutum fiye da miliyan 8 ne ke da rajistar yin zaben.
Ranar 4 ga watan nan kotun tsarin mulkin kasar ta amince da 'yan takara 24 su tsaya a wannan zaben na yau, amma kotun ta hana wasu 'yan takara su shida tsayawa.
Rikicin masu ikirarin kishin Islama a arewacin kasar, da rikicin kabilanci tsakanin Abzinawa da Fulani ne ya mamaye yakin neman zaben, kuma shi ne dalilin raba 'yan kasar masu yawa da muhallansu.
Gwamnatin kasar ta tura fiye da jami'an tsaro 30,000 domin su tabbatar da tsaro a rumfunan zabe har ma da kare lafiyar 'yan takara, a yayin dazaben ke gudana.
Fiye da masu sa ido 80 daga Tarayyar Turai ake sa ran za su duba yadda zaben zai kasance.







