A kama 'yan aware da sojojin da ke kisa a Kamaru - Amnesty

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Kamaru da ta kama sojoji da mayakan 'yan aware da ke aikata laifuka a yankunan raino Ingilishi na kasar.
Tashin hankali a yankunan rainon Ingilishi a arewa maso yammaci da kudu maso yammacin kasar ya yi kamari shekaru biyun da su ka gabata bayan zanga-zanga da mazauna yankunan su ka yi kan nuna bambanci da hukumomi ke yi musu.
Kungiyar Amnesty ta ce ta na da shaidar cewa sojoji sun hallaka kauyuka kuma sun azabtar da wadanda a ka tsare, ta kuma yi zargin 'yan aware da kashe sojoji da kokarin kai wa malamai da dalibai hari.
Tun a shekarar da ta gabata, rashin zaman lafiya ya tsananta a yankin arewaci, da masu turancin Ingilishi ke da rinjaye a Kamaru, bayan da 'yan tawaye suka dau doka a hannu su.
Akwai mutane da dama da suka rasa rayukansu, wasu dubbai kuma sun yi gudun hijira.







