An sanya dokar takaita zirga-zirga a Kamaru

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Kamaru ta sanya dokar takaita zirga-zirga ta tsawon mako guda a bangaren da masu amfani da harshen ingilishi suke a arewa maso gabashin kasar suke.
Wata takarda daga ma'aikatar harkokin tsaron kasar ta ce an dauki matakin ne saboda fargabar kai hare-haren da 'yan tawaye daga makwabciyar kasar Najeriya ka iya kai wa.
Wani jami'i a kasar ya ce dokar takaita zirga-zirgar zata fara ne daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe.
An dai shafe watanni ana fama da tashe-tashen hankula a yankunan masu amfani da harshen ingilishi na kasar.







