Nigeria: An tsaurara tsaro a zaben jihar Anambra

An dai tsaurara matakan tsaro a jihar Anambra domin zaben ya gudana cikin lumuna

Asalin hoton, WhatsApp

Bayanan hoto, An dai tsaurara matakan tsaro a jihar Anambra domin zaben ya gudana cikin lumuna

An gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya cikin tsauraron matakan tsaro.

Babu wurin da aka samu rahoton tashin hankali, yayin da jama'a suka kada kuri'unsu a ranar Asabar.

Jami'an tsaro sun yi sintiri a duk fadin jihar musamman a garin Onitsha, inda kungiyar da ke fafutikar ballewa daga Najeriya IPOB da kuma kungiyar MOSSOB suke da karfi.

Jam'iyyu 37 ne za su fafata a wannan zabe mai cike da cece-ku-ce, ko da yake 'yan takarar jam'iyyu biyar ne suka yi fice wato:

  • Tony Nwoye na APC
  • Gwamna Willie Obiano na APGA
  • Oseloka Obaze na PDP
  • Godwin Ezeemo PPD
  • Osita Chidoka na UPP

Wasu mazauna garin Akwa babban birnin jihar Anambra su sun ce shirye-shirye sun kammala ta fuskar gudanar da zaben da batun sha'anin tsaro da dai sauransu.

Sai dai sun ce IPOB ta rika yada takarda da ke cewa "zabe ba zai gudana ba" .

Kugiyar ta kuma nemi mutane akan su zauna a gida, kada su fita.

Anambra

Asalin hoton, WhatsApp

Wakilin BBC ya ce zaben zai kasance zakaran gwajin dafi ga jam'iyyar APC mai mulki a yankin kudu maso gabashin kasar.

A farkon makon nan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara yankin inda ya kaddamar da wasu ayyuka.

Anambra

Asalin hoton, WhatsApp