Hadiza Gabon ta fara fitowa a fina-finan Nollywood

Hadiza Gabon da Mike Ezuruonye

Asalin hoton, InSTAGRAM/HADIZA GABON

Bayanan hoto, Hadiza Gabon ta gaya wa Mike Ezuruonye cewa ba za ta fito a yanayin da zai saba da addini ko al'adarta ba

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Gabon ta soma fitowa a fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya.

Jarumar ta shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa ta fara gwada sa'arta a fina-finan Nollywood ne domin ta nuna basirar da take da ita ta yin fina-finai a bangarori daban-daban.

A cewarta, "Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a wani gajeren fim na turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a fina-finan Nollywood.

"Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna 'Lagos real fake life'.

"Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a matsayin 'yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a fina-finan Kannywood irinsu nake sa wa a wannan fim".

Hadiza Gabon ta ce ta fito ne a matsayin 'yar arewa

Asalin hoton, InSTAGRAM/HADIZA GABON

Bayanan hoto, Hadiza Gabon ta ce ta fito ne a matsayin 'yar arewa

Hadiza Gabon ta kara da cewa "Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim dinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saba da addini da al'adata ba".

Jarumar ta ce babu wani "bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finan Kannywood da na Nollywood idan ban da bamabancin harshe. Don haka na ji dadin soma fitowa a fina-finan Nollywood".