Nigeria: EFFC ta kama mutum 865 a Kaduna

Asalin hoton, EFCC
A Nigeria, ga alamu kokarin da hukumomin kasar ke yi na fadada yaki da cin hanci da rashawa zuwa matakin kasa ya fara tasiri wajen kama wadanda ake tuhuma da almundahana.
Misali a jihar Kaduna kadai, hukumar yaki da cin hanci da karbar rashawa ta EFCC ta ce ta kama mutum fiye da 860 da ake tuhuma da hannu a almundahana cikin 'yan watanni da bude ofishinta a can.
A cikin wata sanarwa, Shugaban Hukumar a shiyyar Kaduna, Ibrahim Baffa, ya ce an kakkama mutanen ne sakamakon koke-koke har 220 da aka shigar gaban hukumar tasa kan wadannan mutanen.
Ya ce kawo yanzu sun fara bincike kan koke-koke 130 daga cikinsu inda har suka shigar da kara kan koke-koke guda 10 a gaban kotu.
Ofishin inji sanarwar, ya samu kwato Naira miliyan 227 daga hannun wadannan mutanen cikin har da dalar Amurka dubu 17.
Da ma dai masu fafutukar yaki da almundahana a kasar sun jima suna shawarartar hukumomi da su ba za komarsu zuwa kasa domin ko can ma ana tafka ta'asa.







