Kwastam sun kama ɗaruruwan bindigogi a Lagos

Asalin hoton, AFP/GETTY
Hukumar hana fasa ƙwauri a Najeriya ta ce ta kama ɗaruruwan bindigogi da wasu mutane suka yi yunƙurin shiga da su ƙasar.
Hukumar ta tabbatarwa da BBC cewa bindigogin, waɗanda ta kama a Lagos, guda 661 ne.
Ta ce an kama mutum uku ciki har da jami'in fiton da ya shigo da kwantainar da aka ɓoye bindigogin a ciki
Jami'an kwastam sun kama makaman ne a wata unguwa mai suna Mile 2 da ke daf da gabar teku, yayin wani aikin sake tantance kayan da aka shigo da su.
Bindigogin na cikin wata kwantaina ce, wadda takardunta ke nuna cewa ƙofofin gida ne a ciki.
Najeriya dai tana fama da rikicin 'yan tayar-da-ƙayar-baya a yankin Arewa maso Gabashi da kuma ayyukan tsageru masu fasa bututan man fetur a yankin Neja-Delta mai arziƙin mai.







