Boko Haram 'ta kafa tuta' a wasu kauyuka uku a Borno

Asalin hoton, Getty Images
Wata majiyar soji da fararan hula na cewa mayakan Boko Haram sun kafa tutocinsu a wasu kauyuka uku a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Nigeria.
Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa mayakan sun yanka mutane takwas, ciki har da wani dagaci, a lokacin da suka hare-haren a yammacin ranar Litinin.
Kauyukan na Kubirivour, Boftari and Kuburmbalah na kusa da garin Chibok ne, inda aka sace 'yan makaranta fiye da 200 a 2014.
Akalla mutane 17 ne aka jikkata a hare-haren.
Wata majiya ta ce har yanzu mayakan Boko Haram na rike da garin Malam Fatori, wanda ke kan iyakar Najeriya da Nijar.
A ranar Lahadi ne, sojojin Najeriya suka kwato garin daga hannun mayaka.
Sai dai rahotanni sun ce sun sake damara inda suka sake kwace iko da garin.
Wakilin BBC a Najeriya ya ce hare-haren na baya-bayan nan na nuna yadda har yanzu kungiyar ta Boko Haram ke ci gaba da zama barazana ga kasar.










