Kasuwar cinikin ‘yan kwallo: Makomar Mbappe, Fernandinho, Koulibaly, Ozil, Tomori

Asalin hoton, Reuters
Mai kungiyar Chelsea Roman Abramovich na duba yiwuwar mayar da tsohon kocin kungiyar Avram Grant Stamford Bridge domin ya taimaka wa Frank Lampard. (Sky Sports)
Real Madrid na shirin sayar da 'yan wasanta shida a bana domin ta sami kudaden da za ta dauko Kylian Mbappe, dan wasan gaba na PSG mai shekara 22. 'yan wasan sun hada da Gareth Bale, da dan kasar Brazil Marcelo, da dan kasar Serbia Luka Jovic da kuma 'yan Spaniya uku: Isco, da Dani Ceballos da Brahim Diaz. (AS - in Spanish)
Dan wasan Manchester United Timothy Fosu-Mensah mai shekara 23 ya shirya tsaf domin komawa Bayer Leverkusen kan fam miliyan 1.5 bayan da ya ki amincewa a tsawaita kwantiraginsa a Old Trafford. (Manchester Evening News)
Wolves sun ce ba za su ci gaba da neman su dauko Oliver Giroud, dan wasan gaba na Chelsea mai shekara 34 ba, da kuma Divock Origi, dan wasan gaba na Liverpool mai shekara 25 bayan da su ka sanar da kocinsu Nuno Espirito Santo cewa ba su da kudin kashewa kan sabbin 'yan wasa a wannan lokacin. (Mirror)
Bayern Munich ta kusa dauko dan wasan baya na Reading, Omar Richards mai shekara 22 yayin da ake sa ran kwantiraginsa za ta kare a karshen wannan kakar wasan. (Guardian)
Dan wasan tsakiya na Manchester City wato Fernandinho mai shekara 35 na iya tsawaita zamansa a kungiyar domin bai yanke hukuncin komawa wata kungiyar Turai ko Amurka ta Kudu ba. (Telegraph - subscription required)
Dan wasan baya na Napoli Kalidou Koulibaly, wanda ake rade-radin zai iya komawa Liverpool ko Manchester City ko Manchester United zai tafi ne kawai idan wata kungiya ta yi tayin fam miliyan 100 kan dan wasan dan asalin kasar Senegal wanda ke da shekara 29 da haihuwa. (Talksport)
Dan wasan tsakiya na Brazil Casemiro mai shekara 28 ya fi duk 'yan wasan Real Madrid da ke wasa a halin yanzu daraja, inji wani rahoto na kamfanin binciken kudade na KPMG. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Dan wasan baya na Barcelona Junior Firpo ya bayyana aniyarsa ta tsawaita zamansa a Nou Camp duk da yadda wasu kungyoyi ke nuna sha'awa kan dan wasan mai shekara 24 kuma dan kasar Spaniya. (Marca)
Kocin Tottenham Jose Mourinho ya gaya wa dan wasan tsakiya na Arsenal Mesut Ozil cewa ba ya bukatarsa a Spurs bayan da dan wasan ya wallafa a intanet cewa gara ya yi ritaya da ya buga wa Tottenham wasanni. (The Sun)










