Yakin Ukraine: Fitattun mutanen da ake amfani da hotunansu wajen goyon bayan Putin

Fitacciyar mai amfani da shafukan sada zumunta ER Yamini a Indiya

Asalin hoton, ER Yamini

Bayanan hoto, Fitacciyar mai amfani da shafin sada zumunta ER Yamini, ta kasance yar ba-ruwanmu kan yakin da ake tsakanin Rasha da Ukraine, amma a shafin Twitter an samu wani dandali da aka bude da ake wallafa hotunanta a ciki a kan goyon bayan Vladimir Putin
    • Marubuci, Daga Juliana Gragnani, Medhavi Arora, da Seraj Ali
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, World Service Disinformation Team

Fitacciyar mai amfani da shafukan intanet, ER Yamini a Indiya, ba ta taba wallafa komai a shafinta na Twitter ba, maimakon hakan ta fi wallafa na manyan mutane musamman na Instagram da YouTube.

Sai dai a farkon watan Maris, an samar da wani shafin Twitter da ke amfani da hotonta tare da maudu'in: "#IStandWithPutin. True Friendship" ma'ana ''Ina goyon bayan Putin. Abota ta gaskiya,'' an kuma wallafa wani bidiyon maza biyu sun rungume juna, daya na wakiltar Indiya dayan kuma Rasha.

Yamini ta bayyana cewa ba ta goyon bayan dukkan bangarorin biyu da ke yaki da juna Rasha da Ukraine, damuwarta a kan masoyanta take.

"Idan suka ga wannan abin da aka wallafa, me za su yi tunani a kaina?" ta tambaya, "Ina ma ba su yi amfani da hotona wajen bude shafin ba."

Shafin Twitter na bogin, wani bangare ne na wata kungiya da ke goyon bayan shugaban Rasha, Vladimir Putin, wanda ke amfani da maudu'in #IStandWithPutin da kuma #IStandWithRussia a ranakun 2 da 3 ga Maris aka kirkiro su.

Wannan ya bude kafar tattaunawa kan halin da ake ciki a Rasha musamman daga mabiya addinai da dama musamman daga kudancin duniya kamar Indiya da Pakistan, da Afrika ta Kudu har da Najeriya, yawanci dai na goyon bayan yakin da Rasha ke yi ne da Ukraine.

Shugaban Rasha Vladimir Putin, ranar 9 ga watan Mayu 2022 a dandalin Red Square da ke Moscow, lokacin faretin sojoji na tunawa da nasarar da suka samu da ake yi wa lakabi da Victory Day

Asalin hoton, EPA/Mikhail Metzel/Kremlin Pool/Sputnik

Bayanan hoto, An bude shafukan Twitter daga sassa daban-daban na kudancin duniya domin goyon baya ga Shugaba Putin daga 2 zuwa 3 ga watan Maris

Yawancin abubuwan da ake wallafawa a shafukan su ne hotuna, wanda mutane ke sanyawa da nunawa karara suna bayan Mista Putin da Rasha kanta.

Sai dai daga bisani an gano akwai shafukan boge a cikinsu, suna sake wallafa sakonnin tare da yi masa kwaskwarima da daukar ido, da kara wasu bayanai, da a baya-bayan nan aka samar da su.

"Muna kyautata zaton an samar da su ne domin nuna Putin na samun daukaka, ta hanyar wallafa sakonnin goyon baya na karya da nuna kwarin gwiwa ga Putin daga wadannan kasashen," in ji Carl Miller, shugaban kamfanin fasaha na CASM Technology, wanda ke bincike kan abubuwan da ake wallafawa masu cutar da mutane da labaran karya.

CASM, ya gano shafuka kusan 1,000 da ke tun daga sunan da hoton bude shafin ake nunawa karara ana goyon bayan Rasha, kuma sabbin shafuka ne da aka kirkire su tsakanin ranakun 2-3 na watan Maris, an kuma wallafa sakonnin da harsuna daban-daban.

Binciken BBC kan daruruwan shafukan boge irin wannan, ya tabbatar da haka. Bincikenmu ya tabbatar da abin da Mista Miller ke tunanin, sun kuma tabbata na boge ne.

Mawakin salon raf, Nipsey Hussle ranar 10 Disamba 2018 a Atlanta, Georgia

Asalin hoton, Prince Williams/Getty Images

Bayanan hoto, A shekarar 2019 aka kashe ba'Amuruken mawakin raf, Nipsey Hussle, 2019, shi ma an yi amfani da hotonshi a daya daga cikin shafukan da aka bude na goyon bayan Putin a 2022

Duk da cewa idan aka kara nazari kan hotunan da aka wallafa, mun gano an wanko irin hotunan ne daga shafukan fitattun mutane, da masu fada aji, wadanda ba su san abin da ke faruwa ba, ba su san ana amfani da hotunansu domin jinjina wa Rasha da goyon baya kan yakin da take yi da Ukraine.

Mun kasa gano wadanda suka samar da shafukan, da sanin ko suna da alaka da gwamnatin Rasha.

Misali shafin da aka bude da sunan Preety Sharma, an rubuta bayanan da ake cewa ta fito daga Indiya amma yanzu tana zaune a Miami. Ranar 26 ga watan Fabrairu aka bude shi, kwanaki biyu bayan Rasha ta mamaye Ukraine. Sakon da aka wallafa na cewa "Putin mutumin kirki ne".

Sai dai matar da aka sanya hotonta wajen bude shafin ta na can wata duniyar. Nicole Thorne 'yar Australia da ta yi fice a shafukan sada zumunta, tana da mabiya miliyan 1.5 a shafin Instagram, ba kasafai take amfani da ainahin hotonta a shafin Twitter ba.

Wani shafin da aka bude shi ne na mawakin nan dan Indiya Raja Gujjar. Sakon farko da aka wallafa an yi shi ne ranar 24 ga watan Fabrairu, rana ta farko da fara mamayar.

Kuma dukkan wadanda suka yi martani a kai su 178, sun wallafa sakon a shafinsu, abin da ke nuna tabbas wani ke aikata hakan.

BBC ta tuntubi Ms Thorne da Mr Gujjar, dukka sun tabbatar mana wadannan shafukan ba na su bane, ba ma su san da su ba.

Wani guda da aka bude a watan Fabrairu 2022, da wallafa sako a rabnar 2 ga Maris, ba shi da mabiya sam. da BBC ta yi kokarin duba bayanan da ke ciki, sai muka gano asusun matashin ba'Indiyen a LinkedIn.

Amma komai da komai an bude ne da bayanan Senthil Kumar, fitaccen injiniya a kasar. Mun tambaye shi me ya sa ya samar da wani shafin kawai domin ya dinga wallafa wannan goyon baya ga Putin.

"Na kan shiga Twitter domin ganin abin da ake tattaunawa a wannan rana. Sai na ga waɗannan sakonnin, kawai ni ma sai na sake wallafawa," in ji shi.

Ya yi amanna Rasha ta taimaka wa Indiya a shekarun baya, don haka Indiyawa ya kamata su mara wa Rasha baya a halin da take ciki. Kuma sabon shafi da suna ya bude, ya ce saboda ya manta da lambobin sirrin tsohon shafinsa.

Babu ruwan kasashen yamma

Samun wadannan shafuka ya janyo suka yi Allah-wadarai kan hakan a kasashen Turai, saboda ana wallafa sakonnin da ke sukar matakin kasashen Turai, da nuna boyon baya ga kasashen da ake kira Brics wato, Brazil, Rasha, Indiya, China, da Afirka Ta Kudu, tare da bayyana goyon baya kai tsaye ga Shugaba Putin.

"Mun yi zaton za a nuna goyon baya kai tsaye ga kasashen Turai, da gangami kan hakan. Amma sai muka lura sam babu wanda ya yi wani batu ko ikirarin daga Turai yake," in ji Mr Miller.

Taswirar da ke nuna shafukan da aka bude 1,128 cikin 'yan kawanaki wanda CASM su ka gano.

Rashin takamaiman hotuna na daya daga cikin abin da ya kara dagula lissafi.

Cikin shafuka 100 da CASM suka gano, BBC ta gane ba a wallafa hoto a bayanan shafuka 41 da aka kirkira ba. Wasu shafukan 30 kuma an yi bayani ko wallafa hotunan Mista Putin yadda ake kambama shi, ko hotunan shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg.

Daidaiku ne kadai suke da wasu hotunan da suka shafi wasu mutanen kuma yawanci an sato su ne a wasu shafukan.

Twitter ta haramta ikirarin zama wani ko kwaikwayon wani babban mutu, ko kungiya, domin wallafa labaran karya saboda yaudarar wani ko wasu ko kulla wa wani ko wasu sharri da bata musu suna.

Twitter ya shaida wa BBC cewa kawo yansu, ya goge sama da shafuka 100,000, wadanda suka take dokokin kamfanin, da suke yaudara da tunzura mutane aikata ba daidai ba, ciki har da dakatar da gwamman shafukan bogi da ke wallafa cin mutunci da kambama abin da Rasha ke yi a Ukraine, da suka hada da shafukan masu maudu'ai kamar #IStandWithRussia da #IStandWithPutin.

Hoton shafin da aka bude da sunan 'yar wasan kwakwayo Nazriya Nazim a Tiwita

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto, Twitter ya cire shafuka 11 cikin 12 wadanda BBC ta nuna da ke amfani da hotunan fitattun mutane, ciki har da fitacciyar 'yar wasan kwaikwayon Indiya Nazriya Nazim

Shi ma Twitter din ya ce yana gudanar da bincike da dakatar da daruruwan shafukan da aka bude na boge, wanda binciken kamfanin fasaha na CASM, da 11 cikin 12 da BBC ta gano, da suke amfani da bayanan wasu.

'Sai dai Twitter ya ce, babu wata shaida da ta nuna akwai alakar aiki ko kwangilar nuna goyon baya ga Rasha kan yakin da take yi a Ukraine.