Zaɓen Anambra: Tarihin sabon gwamna Charles Chukwuma Soludo

Charles Chukwuma Soludo

Asalin hoton, FACEBOOK/CHARLES CHUKWUMA SOLUDO

A yau Alhamis ne aka rantsar da zaɓaɓɓen Gwamnan Anambra Farfesa Charles Chukwuma Soludo bayan ya yi nasara a zaben da aka gudanar a watan Nuwamban 2021.

Mun yi nazari kan tarihinsa.

Soludo ba baƙo ba ne a harkokin mulki bayan ya shafe shekara biyar a matsayin gwamnan Babban Bankin Najeriya na CBN.

Farfesa Soludo ya riƙe muƙamin gwamnan CBN daga 29 ga watan Mayun 2004 zuwa 29 ga Mayun 2009.

An haife shi ranar 28 ga watan Yuli, 1960, a Ƙaramar Hukumar Aguata ta Jihar Anambra.

A ranar 23 ga watan Yuni ne aka bayyana Farfesa Soludo a matsayin ɗan takarar APGA sannan kuma gwamna mai-ci Willie Obiano ya ba shi tutar takara ranar 25 ga Satumba.

Neman ilimi

Bayan kammala karatunsa na sakandare, ya wuce Jami'ar Najeriya da ke Nsukka, inda ya kammala digirinsa na farko a fannin tattalin arziki da daraja mafi girma. Ya kuma yi digirinsa na biyu da na digirgir a fannin tattalin arziki a jami'ar ta Nsukka.

Farfesa Soludo ya samu horo na shekara huɗu na gaba da digiri a wasu manyan cibiyoyi na duniya, ciki har da: Cibiyar Brookings da ke Washington, DC; Jami'ar Cambridge da ke Birtaniya; Damar ƙaro karatu a Smuts Research Fellow; Damar ƙaro karatu a Kwalejin Wolfson.

Sauran wuraren da zaɓaɓɓen gwamnan ya je sun haɗa da; Hukumar Tattalin Arziki ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Afirka; Jami'ar Warwick a matsayin Masanin Bincike mai Ziyara a Cibiyar Tattalin Arzikin Afirka; Jami'ar Oxford (tare da tallafin kwamitin Rhodes).

Ya kuma halarci kwasa-kwasai na musamman sama da 12 kuma ya yi aikin bincike da koyarwa da tuntuɓar juna a ɓangarori daban-daban na tattalin arziki.

Rayuwarsa ta aiki

CHARLES CHUKWUMA SOLUDO

Asalin hoton, Getty Images

Ya yi aiki a Bankin Duniya a matsayin mai bayar da shawara na gajere da dogon zango a 1993 da kuma a Hukumar Tattalin Arziki ta Majalisar Dinkin Duniya na Afirka a birnin Addis Ababa.

Kazalika, ya yi aikin mai ba da shawara ga hukumomin; UNCTAD; Tarayyar Turai (EU); Ƙungiyar Haɗin Kan Tattalin Arziƙi da Ci Gaba (OECD); Majalisar Dinkin Duniya (MDD) New York; Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID); Bankin Raya Afirka (AfDB); Kasuwar gama-gari na Gabashi da Kudancin Afirka (COMESA); Tarayyar Afirka (AU);

Majalisar Binciken Ci gaban Ƙasashen Duniya (IDRC) Canada; Majalisar Ci gaban Nazarin Kimiyyar zamantakewa a Afirka (CODESRIA); Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS); da sauransu.

Farfesa Soludo ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara da kuma masanin mai ziyara a hukumar ba da lamuni ta duniya (IMF) a 1994, sannan kuma ya koyar da darasin tsare-tsare na IMF ga manyan ma'aikatan Babban Bankin Afirka ta Yamma da sauran yankuna masu tasowa.

Ya yi aiki a matsayin: Memba, kwamitocin fasaha waɗanda suka tsara manufofin tattalin arziki da kasuwanci ga gwamnatin tarayyar Najeriya; da Babban Darakta na Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki ta Afirka (AlAE).

Farfesa Soludo ya shiga gwamnatin tarayyar Najeriya ne a watan Yulin 2003 a matsayin mai bai wa shugaba Obasanjo shawara kan tattalin arziki da kuma shugaban hukumar tsare-tsare ta kasa (NPC).

Ya kasance shugaban tawagar da ta tsara shirin gyara tattalin arziki da zamantakewar Najeriya (2003-2007), National Economic Empowerment and Development Strategy (NEEDS), sannan kuma ya jagoranci tsare-tsare na hadin gwiwa kan tsarin tarayyar Najeriya ta hanyar taimaka wa gwamnatin jihohi wajen tsara dabarun bunkasa tattalin arzikinsu (SEEDS).

Nasarorin da ya samu

Farfesa Soludo da matarsa

Asalin hoton, FACEBOOK/CHARLES CHUKWUMA SOLUDO

A matsayinsa na Gwamnan Babban Bankin Najeriya daga watan Mayun 2004, Farfesa Soludo ya sake mayar da Babban Bankin a matsayin hukumar kudi mai inganci kuma ya samu nasarar aiwatar da wani muhimmin tsari wanda ya kai ga kyautata tsarin bankin Najeriya wanda ba a taba yin irinsa ba.

A saboda haka ne aka bayyana tsarin bankin Najeriya a matsayin wanda ya fi girma a Afirka ɗaya daga cikin mafi girma a duniya.

Ya kuma yi nasarar kafa hukumar hada-hadar kudi ta Afirka (AFC), wato bankunan nahiya masu zaman kansu kuma na zuba jari.

Shi ne kan gaba a shirin inganta tsarin dabarun hada-hadar kudi na 2020 (FSS 2020), tsarin da zai bunkasa tsarin hada-hadar kudi na Najeriya don zama cibiyar hada-hadar kudi ta Afirka da kuma fitar da tattalin arzikin Najeriya cikin jerin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na duniya zuwa shekarar 2020.

Farfesa Soludo ya samu lambobin yabo daga ƙungiyoyin jama'a da na masu zaman kansu da na addini da na sana'a da na ɗalibai da jami'o'i da sauransu.

Jaridar Financial Times ta Landan ta bayyana shi a matsayi na musamman mai laƙabin 'Ita Great Reformer'.

Mamba ne na Ƙungiyar Ba da Shawara ta Duniya, UK-DFID; mamba na Babban Mashawarcin Masana Tattalin Arziki na Bankin Duniya da Ƙungiyar Ba da Shawarwari ta Ƙasashen Duniya na Ma'aikatar Raya Ƙasa ta Burtaniya (DFID).

Farfesa Soludo na da riƙe da lambar yabo ta gwamnatin tarayyara Najeriya, Commander of the Order of the Federal Republic (CFR).

Farfesa Soludo ya auri Nonye kuma sun samu albarkar yara.