Musulmai da Kirista na ce-ce-ku-ce kan batun saka hijabi a makarantun Kwara

Aworan ileewe Kristẹni ni Kwara
Lokacin karatu: Minti 4

Ƴan Najeriya da dama sun yi ta bayyana albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta da muhawara kan rikicin da ya ɓarke tsakanin Musulmai da Kiristoci kan batun saka hijabi a wasu makarantun jihar Kwara.

A ranar Laraba ne fada ya ɓarke tsakanin Musulmai da Kiristoci a Makarantar Sakandare Baptist da ke birnin Ilori na jihar Kwara, a yankin tsakiyar Najeriya kan batun barin ƴan makarantar su sanya hijabi.

An ƙaddamar da maudu'i mai taken #Kwara da #Hijab a shafin sada zumunta na Twitter inda aka yi amfani da su fiye da sau sama da 12,000 da kuma sau sama da 6,000.

Me ake cewa a Tuwita?

Ra'ayoyi sun sha bamban a shafin Tuwita, yayin da wasu ke ganin laifin hukumomin makarantun, wasu kuwa laifin iyayen yaran suke gani.

Masu ganin laifin iyayen yaran na cewa idan har tsarin makarantun bai musu ba to kamata ya yi su cire su, musamman tun da sun san cewa makarantun na mabiya addinin kirista ne.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Aisha Yesufu ta ce: "Me ya sa wani zai dage kan batun yadda ya kamata makarantar kuɗi ta yi tsarin kayan da ɗalibanta za su sa.

"Idan makarantar gwamnati ce to wannan wani abu ne daban. Idan har ba sa son ɗalibansu su sanya hijabi, ku a matsayinku na iyaye kuma kuna son ƴaƴanku su saka hijabi, sai kawai kar ku kai su can.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Shi kuwa wani tsohon sanata daga jihar Kaduna Shehu Sani cewa ya yi: "Ƴan gani kashenin addinin a Ilori da suke faɗa kan hijabi ya kamata su adana kuzarinsu da mayar da hankali wajen kare jiharsu daga ƴan bindiga da a hankali suke kutsawa daga jihar Neja.

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

@MFaarees_ cewa ya yi: "Ba na jin ya kamata a ce hijabi ya jawo faɗa tsakanin Musulmai da Kiristoci a Jihar Kwara, ya kamata a bar ƴaƴan Musulmai su saka hijabi idan har makarantar ba mallakin Kirista ba ce, sannan bai kamata a tursasa wa ƴaƴan kirista sa hijabi ba, hakan shi ne mafi sauƙi."

@SavvyRinu ta ce: "Bari mu waiwayi tarihi. Da yawa daga cikin iyayenmu da kakanninmu a makarantun ƴan mishan suka yi karatu, ko da kuwa Musulmai ne su. Shin suna sa hijabi a lokacin? Ko kuwa maza ne kawai suka halarci makarantun?

Me ya faru ranar Laraba?

mata dauke da rubutun zanga-zanga a Kwara
Bayanan hoto, Da alama an ja layi yanzu a jihar bayan da wata ƙubigyar malaman kiristoci ta dage cewa za su "kare addininsu idan har gwamnati ta ƙi bin doka da tsari@

Rahotanni sun ce mutane daga dukkan ɓangarorin biyu da suka gwabza da juna a ranar Laraba sun ji raunuka.

Sun yi ta jifan juna da duwatsu da kujerun roba a yayin rikicin, wanda ya faro sakamakon komawa makarantu da yaran suka yi, bayan da aka shafe kusan wata ɗaya suna rufe.

Ƴan sanda sun kuma dinga jefa barkonon tsohuwa bayan da wasu suka yi ƙoƙarin ɓalle allon da ke ɗauke da sunan makarantar.

Gwamnatin jihar Kwara ta bayar da umarnin buɗe makarantun 10 ne a yayin da ake tsaka da rikici.

Rikicin ya janyo an sake rufe makarantun.

Kiristoci ƴan mishan ne suke kafa makarantun shekaru da dama da suka gabata, amma gwmnati ta ce ita ce take kula da su.

Rikicin ya faro ne a watan da ya gabata inda mabiya addinin Kirista a fadin jihar ke cewa ba su yarda dalibai mata Musulmai su rika zuwa makarantunsu da hijabai ba, ko dai su daina ko kuma su nemi wasu makarantu na daban.

Gwamnatin jihar ba ta goyi bayan wannan mataki na hukumomin makarantun ba.

Wannan ya jawo sai da aka dangana da kotu, inda Babbar Kotu da Kotun Ɗaukaka ƙara suka bai wa gwamnati gaskiya kan batun, amma a yanzu wata ƙungiyar Kiristoci tana ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka ƙara a gaban Kotun Ƙoli.

An rufe makarantun mako uku da suka gabata bayan bayyanar wani bidiyo da ke nuna yadda aka hana ƴaƴan Musulmai sanye da hijabi shiga cikin makarantar.

BBC ta ziyarci biyu daga cikin makarantun da aka buɗe sakamakon umarnin gwamnati.

Sai dai ta ga yadda aka hana wasu ɗalibai masu sanye da hijabi shiga ciki.

Wasu mambobin wata ƙungiyar kiristoci da suka taru a gaban makarantar sun yi zanga-zanga cikin lumana inda suka dinga ɗaga kwalaye masu rubuce da adawarsu ta bari a sa hijabi da gwamnati ta yi.

Ilori
Bayanan hoto, Kiristoci ƴan mishan ne suke kafa makarantun shekaru da dama da suka gabata, amma gwmnati ta ce ita ce take kula da su

Makaranta ɗaya ce kawai daga cikin goman ta ECWA a Oja Iya ta bari ɗalibai masu hijabi su shiga.

Da alama an ja layi yanzu a jihar bayan da wata ƙubigyar malaman kiristoci ta dage cewa za su "kare addininsu idan har gwamnati ta ƙi bin doka da tsari."

"Ba za mu bari a sa hijabi a makarantunnmu ba, faƙat. Wannan makarantar kiristoci ce.

Daga baya a ranar Larabar dai ƙura ta lafa, amma za a zuba ido a ga ko gwamnati za ta tursasa makatantun bin dokar sannan ko za a koma a ci gaba da karatu.

Dama kafin wannan lokaci annobar cutar korona ta yi illa sosai da mayar da karatu baya.

Idan wannan rikicin ya ci gaba, ɗalibai ba za su samu damar shirya wa jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da ke gabansu ba a yanzu.

Amma wasu na ganin abu kaɗan ya kamata a yi don samar da zaman lafiya a jihar da ke alfahari da cewa ita ce Cibiyar Haɗin Kai.