'Yan Boko Haram sun kashe mutane 60 a Bama

Asalin hoton, AFP
'Yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane akalla 60 tare da bankawa gine-gine da dama wuta a garin Bama dake jihar Borno a arewa maso gabashin Nigeria.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Borno Lawal Tanko ya shaidawa BBC cewar an kai harinne a ranar Laraba.
A cewarsa, jami'an tsaro sun kawo dauki daga bisani inda suka kashe 'yan Boko Haram din ta hanyar luguden wuta ta sama.
A 'yan kwanakin nan 'yan Boko Haram sun tsannanta kai hare-hare, inda suka kashe kusan mutane kusan 300 a cikin wannan watan na Fabarairu.
A ranar Laraba, Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da bidiyo inda ya ce kungiyarsu ce ta kashe, Sheikh Muhammed Auwal Albani na Zariya.







