Ramalan Yero: Gwamnatin Nasir El-Rufa'i ta gaza a fannin tsaro da walwalar jama'a

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya soki gwamnatin Malam Nasir El-Rufa'i ta da ta gaje shi da cewa ta gaza a fannin tsaro da walwalar jama'a.

Tsohon gwamnan ya kuma soki gwamnatin mai ci kan korar ma'aikata, inda ya ce matakin ya kara ta'azzara kuncin rayuwa a jihar ta Kaduna.

Ya kuma mayar da martani ga masu cewa gwamnatinsu ba ta yi aiki ba idan aka kwatanta da ayyukan da ake yi yanzu haka a wasu biranen jihar.

Wasu bidiyon da za ku so ku kalla