Ranar Yoga ta Duniya: Bahaushiya mai baiwar lanƙwasa jiki

Latsa hoton sama ku kalli yadda Khadijah ke lanƙwasa jikinta

Litinin 21 ga watan Yuni, ita ce ranar lanƙwasa jiki ta duniya wato Yoga.

Albarkacin wannan rana, mun tattauna da Khadijah Taheerah Mahamood, wata matashiya mai baiwar lanƙwasa jiki.

Khadija ta shaida wa BBC cewa mutane da dama sun sha yi mata gargaɗi cewa "ke kar ki karye fa", alhalin ita kuma targaɗe ba ta taɓa yi ba.

Ta ce an haife ta da baiwar lanƙwasa jiki amma ba ta fahimci hakan ba sai da ta girma.

Ta ƙara da cewa tana tunanin nan gaba za ta iya koyar da Yoga a matsayin sana'a amma a yanzu ba ta koyar da kowa.

Labaran da za ku so ku karanta: