Cibiyar bunkasa Dimukradiyya da ci gaban kasa ta Afirka ta ce jami'an tsaron Najeriya sun kashe sama da farar hula 13,000 cikin shekaru 10.
Cibiyar ta ce ba bakon abu ne ganin jami'an tsaro suna azabtar da mutane, ko tsarewa ba bisa ka'ida ba, da kashe-kashe a shekaru goman da suka gabata.
Kawo yanzu hukumomin Najeriya ba su mayar da martani kan rahoton ba.
Masu bincike sun ce sun yi nazari kan dimukradiyyar Najeriya cikin shekaru 20, a fannoni da dama kama daga kare hakkin dan adam, 'yancin fadar albarkacin baki, da shiga da 'yan kasa cikin harkokin gwamnati.
Rahoton da kungiyar ta fitar a ranar Talata, ya soki matakin gwamnati kan abin da ya kira amfani da karfi fiye da kima domin magance tayar da kayar bayan 'yan aware, da 'yan ta'adda da masu zanga-zangar lumana.
Rahoton ya kuma yi misali da yadda jami'an tsaro da gwamnati suka tunkari zanga-zangar adawa da cin zarafin 'yan sanda aka yi a shekarar da ta gabata wato #EndSARS.
Cibiyar ta ce lamarin ya sanya tsoro da fargaba a zukatan 'yan Afirka kan makomar dimukradiyya a yankin.
A karshe, cibiyar ta ce kamata ya yi a bai wa jami'an tsaro horo kan hakkin bil adam, da hukunta wadanda suka take doka, a kuma bar 'yan kasa su shiga a dama da su a fagen siyasa domin ci gaban kasa.