Buhari ya ce zai hukunta masu daukar ma'aikatan boge da cushen albashi

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Badariyya Tijjani Kalarawi

  1. Rufewa

    A nan za mu rufe wannan shafi na kai-tsaye. Sai ku tare mu gobe da afe domin samun sabbin labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku.

    Kada ku manta za ku iya ci gaba da karanta labaranmu a bbchausa.com ko kuma ku tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta.

  2. , An yanke wa dan IS da ya kashe 'yar Yazidi a Iraqi daurin rai-da-rai

    Talal ya kare fuskarsa da wani littafi a lokacin zaman kotun,inda ya ke magana da lauyansa

    Wadda ta lashe lambar yabo kan zaman lafiya ta Nobel, Nadia Murad ta mika godiyarta ga kasar Jamus bayan da wata kotu a birnin Frankfurt ta yanke wa wani mutum da aka samu da hannu wurin kisa da kuntata wa mabiya addinin Yazidi, hukuncin daurin rai-da-rai a gidan maza.

    Nadia Murad, wadda ita ma ta tsira da kyar daga kashe-kashen da aka yi wa Yazidawan ta ce wannan hukunci da aka yanke wa Taha Al-Jumaily abin tarihi ne, kuma nasara ce ga daukacin mabiya addinin. Aljumaily dai ya some nan take, jim kadan bayan karanta masa hukuncin.

    A shekarar 2015 ne a wani yanki da kungiyar IS ta mamaye, Taha Al-Jumaily ya bautar da wata mata da diyarta, mabiya addinin Yazidi, inda daga baya 'yar ta mutu bayan ya daure ta kan ta na kallon kasa, kafafunta a sama cikin tsananin zafin rana.

    Sama da Yazidawa dubu 3 ne aka kiyasta cewa IS ta kashe, da bautar da wasu matan da yara dubu 7 a cikin shekarun 2014 da kuma 2015.

  3. Ana zargin tsohon Firaiministan Lesotho da kisan tsohuwar matarsa

    Thabane ya halarci bikin shan rantsuwar kama aiki da mata shi ta yanzu, kwanaki biyu bayan kisan Lipolelo

    Ana zargin tsohon firai ministan Lesotho Thomas Thabane da kisan tsohuwar matarshi Lipolelo Thabane a shekarar 2017.

    A shekarar da ta gabata ne aka tuhumi matar shi ta yanzu, Maesaiah, da laifin irin wannan.

    Ta na zaune a gidan Thabane a lokacin da aka aikata kisan, ana kuma zarginsu da biyan maharan da suka kahe Lipolelo, amma sun musanta zargin.

    A shekarar da ta gabata ne Mista Thabane ya sauka daga mukamninsa, bayan shafe watanni ana matsa masa lamba a lokacin da aka sanar da sunansa a cikin wadanda ake zargi da hannu a mutuwar tsohuwar matarsa.Wannan labari ya girgiza 'yan kasar, da rikita-rikitar siyasa a 'yar karamar kasar da Afirka ta Kudu ta kewaye.

    Mai dakinsa Maesaiah Thabane, ce ta raka Mista Thabane mai shekara 82 zaman kotun. A shekarar da ta gabata an tsare ta amma daga bisani aka ba da ita beli, duk dai kan zargin hannu a kisan Lipolelo.

  4. Buhari ya ce zai hukunta masu daukar ma'aikatan boge da cushen albashi

    Shugaba Buhari

    Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya sha alwashin gwamnatinsa za ta hukunta duk jami'in da aka samu da daukar ma'aikata ba bisa ka'ida ba, da ma'aikatan boge da cushen albashin ma'aikata.

    Shugaban ya yi kalaman ne a ranar Talata, lokacin da ya bude babban taro karo na uku kan yaki da rashawa a ma'aikatun gwamnati da ofishin sakataren gwamnatin tarayya ke shiryawa.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar yaki da rashawa ta kasar ICPC, ta yi bayani a kan yawan kudaden da gwamnati ke batarwa, da karuwar daukar ma'aikata ba bisa ka'ida ba, da karin albashin babu gaira bare dalili da wasu ma'aikatun gwamnati ke yi ga ma'aikatan da a zahiri babu su.

    Da kudaden da ake kashewa na tafiye-tafiye a ciki da wajen Najeriya, da karuwar bukatun 'yan siyasa da aka nada mambobin wasu kwamitoci, ba tare da bincikar inda aka kwana kan hakan ba, sai uwa uba danbarwar cushe a kasafin kudi da sauransu.

    Shugaba Buhari ya yi gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci hakan ba, za kuma ta hukunta duk wanda aka samu da laifin aikata hakan.

    ‘‘Mun rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa ta hanyar cika alkawarin da muka dauka na karasa ayyukan da sauran gwamnatocin da suka gabata sukai watsi da su, da tabbatar da ma'aikatu ba su yi shelar sabbin ayyuka ba har sai an kammala wadanda ke kasa,'' in ji Buhari.

  5. Jami'an tsaron Najeriya 'sun kashe mutum 13,241 cikin shekaru 10'

    Endsars

    Asalin hoton, AFP

    Cibiyar bunkasa Dimukradiyya da ci gaban kasa ta Afirka ta ce jami'an tsaron Najeriya sun kashe sama da farar hula 13,000 cikin shekaru 10.

    Cibiyar ta ce ba bakon abu ne ganin jami'an tsaro suna azabtar da mutane, ko tsarewa ba bisa ka'ida ba, da kashe-kashe a shekaru goman da suka gabata.

    Kawo yanzu hukumomin Najeriya ba su mayar da martani kan rahoton ba.

    Masu bincike sun ce sun yi nazari kan dimukradiyyar Najeriya cikin shekaru 20, a fannoni da dama kama daga kare hakkin dan adam, 'yancin fadar albarkacin baki, da shiga da 'yan kasa cikin harkokin gwamnati.

    Rahoton da kungiyar ta fitar a ranar Talata, ya soki matakin gwamnati kan abin da ya kira amfani da karfi fiye da kima domin magance tayar da kayar bayan 'yan aware, da 'yan ta'adda da masu zanga-zangar lumana.

    Rahoton ya kuma yi misali da yadda jami'an tsaro da gwamnati suka tunkari zanga-zangar adawa da cin zarafin 'yan sanda aka yi a shekarar da ta gabata wato #EndSARS.

    Cibiyar ta ce lamarin ya sanya tsoro da fargaba a zukatan 'yan Afirka kan makomar dimukradiyya a yankin.

    A karshe, cibiyar ta ce kamata ya yi a bai wa jami'an tsaro horo kan hakkin bil adam, da hukunta wadanda suka take doka, a kuma bar 'yan kasa su shiga a dama da su a fagen siyasa domin ci gaban kasa.

  6. CAN ta yi watsi da rage wa ma'aikatan Kaduna lokacin aiki

    Gwamna Nasiru El-Rufa'i

    Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Kaduna, CAN, ta yi watsi da matakin gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufa'i na rage kwanakin aiki ga ma'aikatan gwamnati daga biyar zuwa hudu.

    A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da wannan mataki, wanda ta ce zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Disambar shekarar da muke ciki.

    A wata sanarwa da shugaban kungiyar Rabaran Joeshep Hayaf ya aike wa manema labarai a ranar Talata, CAN ta ce kada ma'aikatan gwamnati su yadda da wannan batu, domin kada a yi musu sakiyar-da-ba-ruwa sai nan gaba a fito da wani abu da ba su san da shi ba.

    ''Ta yaya jihar da ke fama da matsalar tsaro, za a zo ace wai mutane su koma gona, alhalin gonakin a wajen gari suke, Mai zai faru idan su na gonar 'yan bindigar suka far musu a gona, ko kuma aka shiga gidajensu?

    Ma'aikata su tabbatar ba wani salo aka bullo da shi, sai nan gaba a shayar da su mamakin an rage musu albashi tun da ba aikin kwanaki biyar a mako kamar yadda aka bisa al'ada ake yi,'' in ji Hayaf.

  7. Yadda kotu ta ruguza zaben bangaren Ganduje na jam'iyyar APC

    Ganduje

    Asalin hoton, Kano State Government

    Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.

    Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da aka yi Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jihar da ma dukkan shugabannin da bangaren Ganduje ya gudanar.

    Kazalika kotun ta ce bangaren shugabannin da aka zaba a bangaren Sanata Malam Ibrahim Shekarau su ne halastattun shugabannin APC na jihar.

    Da ma dai ana takun-saka tsakananin bangaren Ganduje da na Shekarau kan shugabancin jam'iyyar ta APC.

    Kotun ta ce bangaren Shekarau, wanda ya zabi shugabanni 17,908, shi ne na hakika.

    Banagren na Shekarau ya zabi Alhaji Haruna Ahmadu Danzago a matsayin shugaban APC na jihar Kano, yayin da bangaren Ganduje ya zabi Alhaji Abdullahi Abbas a zabukan da suka gudanar daban-daban ranar 16 ga watan Oktoba.

  8. Chadi ta yi wa ɗaruruwan ƴan tawaye afuwa

    Mahamat Deby

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin sojin Chadi ta yi wa ƴan tawayen ƙasar kusan 300 afuwa da wasu ƴan siyasa, domin cika ɗaya daga cikin buƙatun ƴan adawa da aka gayyata taro kan makomar ƙasar.

    Waɗanda aka yi wa afuwar 296 an ɗaure su ne kan laifuka da suka zafi na ta’addanci da kuma laifukan da suka shafi saɓawa ƙasa, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na AFP ya ruwaito.

    Ƴan tawayen sun ce yin afuwar zai share fagen tayin tattauna da shugaba Mahamat Idriss Deby ya yi wanda ya karɓi shugabancin Chadi bayan mutuwar mahaifinsa da aka kashe a fagen daga a watan Afrilu.

    Mahamat mai shekara 37 ya rusa gwamnati da majalisa tare da sauya kundin tsarin mulki inda ya yi alƙawalin gudanar da zaɓe cikin wata 18.

    Baya ga yin afuwa, buƙatun ƴan tawayen sun ƙunshi yin afuwa ga dukkanin shugabannin siyasa da na soja da kuma dawo da ƙadarorin da gwamnati ta ƙwace.

  9. “Ba lalle rigakafi ta yi aiki ga sabon nau’in cutar korona na Omicron ba”

    Stephane Bancel

    Asalin hoton, OTHER

    Shugaban kamfanin magunguna na Moderna na Amurkaya yi gargadin cewa rigakafin da ake amfani da su yanzu na cutar korona da wuya idan za su iya yin tasiri a kan nau'in Omicron na cutar.

    Kamfanin ya ce rigakafin ba za su yi aiki ba kamar yadda suka yi tasirin a kan nau'in Delta ba.

    Stephane Bancel ya shaida wa Financial Times cewa ba a tantance iya yadda zai iya aiki ba

    Amma abin da masana kimiyyar da ya tuntuba ke cewa shi ne labarin ba mai dadi ba ne.

    Hukumar yaki da cutuka ta tarayyar Turai ta ce yanzu haka mutune 42 ne aka samu suna dauke da sabon nau'in cutar Korona da ake kira Omicron a kasashe 10 na yankin.

    Andrea Ammon, wadda ita ce shugabar hukumar, ta ce ana kuma duba wasu mutum shida da ake zargin cewa su ma suna dauke da sabon nau'in cutar.

    Tun farko dai kasar Netherlands ta ce ta gano mutum biyu da ke dauke da nau'in cutar ta Omicron, kafin daga baya aka gano wasu mutanen 14dauke da ita wadanda suka fito daga kasar Afirka ta kudu.

    Yanzu haka dai manyan kamfanonin hada rigakafin korona uku sun ce za su ga yadda za su inganta rigakafin domin aiki a kan sabon nau'in cutar.

  10. An gurfanar da mutumin da ke tallar fara a cikin jirgin sama

    fara

    Asalin hoton, Getty Images

    An gurfanar damutumin da ake zargi yana tallar soyayyiyar fara ga fasinjojin da ke cikin wani jirgin samana Ugandan Airlines da kuma wanda ake zargi ya dauki hotonsa na bidiyo.

    An ta yaɗa bidiyon a kafofin sadarwa na intanet tun a ƙarshen mako

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    An kama Mubiru Paul da Hajib Kiggundu ranar Litinin lokacin da suka sauka daga Dubai kuma an gurfanar da su a ranar Talata kan laifuka uku -haifar da hargitsi da ƙin bin umarnin ma'aikatan jirgin da yin sakaci da ka iya haifar da yaduwar cuta.

    Tuhumar laifin yaɗa cuta na iya sa a zartar wa mutum ɗaurin kusan shekara bakwai, kamar yadda jaridar Daily Monitor ta ruwaito.

    Jigrin Uganda Airlines ya yi Allah wadai da abin da kamfanin ya kira abin takaici kuma kafofin yada labarai na cikin gida sun ce an dakatar da wasu ma’aikatan kamfanin.

  11. Kwalera ta kashe mutum 156 a Nijar

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce cutar kwalera ta kashe mutum 156 daga cikin mutum 5,400 da suka kamu da cutar a ƙasar.

    Hukumar ayyukan jin-ƙai OCHA ta ce yankin Maradi ne matsalar ta fi shafa.

    Hukumar ta yi gargaɗin yaɗuwar cutar saboda shige da fice da ake kan iyakar Najeriya da Nijar.

    Mutum 31,425 aka bayyana sun kamu da cutar a jihohi 22 na Najeriya.

    Tun a ranar 10 ga watan Agusta Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da rahoton ɓarkewar kwalera a Nijar.

  12. Taliban ta kashe tsoffin sojojin Afghanistan da dama – HRW

    Taliban

    Hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta Human Rights Watch ta ce Taliban ta kashe ko kuma ta tursasa ɓacewar jami’an tsaron Afghanistan da dama tun lokacin da ta ƙwace iko a watan Agusta.

    Ƙungiyar ta ce alƙawalin afuwa da Taliban ta yi bai hana wa kwamandojinta kama tsoffin sojoji da jami’an ƴan sanda da kuma jami’an leƙen asiri ba.

    Human Rights Watch ta ce ta samu hujjoji na kisa sama da 100 a cikin yanki huɗu kawai daga cikin 34 na Afghanistan.

    Taliban ta yi watsi da rahoton.

  13. Batun cin karo da maciji a banɗaki na jan hankali a Najeriya

    Ƴan Najeriya na nuna ƙarin fargaba kan yadda macizai ke shiga cikin gidaje har ma cikin wajen yin tsugunno a banɗaki.

    A baya bayan nan, rahotanni sun cika gari na wata sojar saman Nijeriya da ta rasu a Abuja, sanadin saran maciji bayan ta shiga yin tsugunno a banɗakin gidanta.

    Tun daga lokacin mutane a kafofin sada zumunta suke ta yaɗa hotuna da bidiyon da ke nuna maciji a cikin matsugunan bahaya, a ƙoƙarin wayar da kai don a yi hattara.

    Ku saurari rahoton wakiliyar BBC Bilkisu Babangida

    Bayanan sautiRahoton wakiliyar BBC Bilkisu Babangida
  14. Abin da Ronaldo ya ce kan hamayyarsa da Messi

    Cristiano Ronaldo ya karyata ikirarin cewa burinsa ya sha gaban Messi a yawan samun nasarori musamman kyautar gwarzon ɗan wasan duniya.

    Ronaldo na mayar da martani ne ga Editan mujallar Kwallo ta France Football Pascal Ferre wanda ya ce burin Ronaldo shi ne ya zarta Messi.

    Ɗan wasan na Manchester United ya ce “Ferre ya ƙirƙiri labarin ne kan wata manufarsa kan kyautar gwarzon ɗan wasan duniya da ba a bayar ba a 2020 saboda annobar korona.”

    A sakon da ya wallafa a shafukansa na Facebook da Instagram kafin sanar da Messi a matsayin wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or a ranar Litinin ya ce “Pascal Ferré ya yi ƙarya ne ta hanyar amfani da sunana domin tallar kansa da kuma tallar jaridar da yake yi wa aiki.

    A cikin saƙon, Ronaldo ya ce yana taya duk wanda ya lashe kyautar murna.

    Messi, wanda ke taka leda yanzu a Paris St-Germain, a ranar Litinin ya lashe kyautar Ballon d'Or karo na bakwai, yayin da Ronaldo wanda ya karbi kyautar sau shida ya ƙare a matsayi na shida a duniya a bana.

  15. Barbados ta zama Jamhuriyya

    Barbados

    Asalin hoton, Reuters

    Barbados ta samu ƴancin kai daga Ingila inda Dame Sandra Mason ta maye gurbin sauraniya Elizabeth a matsayin sabuwar shugabar ƙasa.

    Barbados ta zama sabuwar ƙasa da ta samu ƴancin kai a duniya.

    An rantsar da, Dame Sandra Mason a matsayin sabuwar shugabar ƙasa a bikin da aka gudanar a Bridgetown babban birnin ƙasar.

    Yariman Wales da kuma mawaƙiya Rihanna ƴar asalin ƙasar sun halarci bikin.

    A cikin jawabinsa Yarima Charles ya amsa abin da ya kira ayyukan cin zali na ɓautarwa da ƙasar da ke tsibirin Caribbean ta fuskanta.

    Yanzu Barbados ta kawo ƙarshen ƙarfin ikon Birtaniya, wanda ya hada da sama da shekaru 200 na ƙasar ta kasance mashigin fataucin bayi.

    Sarauniyar Ingila ta aika da fatan alheri da farin ciki da zaman lafiya mai ɗorewa ga makomar ƙasar, tare da cewa ƙasar, “tana da tasiri a zuciyarta.”

  16. Tambuwal ya haramta ayyukan ƴan sa-kai a Sokoto

    Gwamna Tambuwal

    Asalin hoton, Other

    Gwamnatin Sokoto ta haramta ayyukan ƴan sa-kai a faɗin jihar tare da ƙarfafa aikin ƴan banga.

    Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal wanda ya sanar da ɗaukar matakin a ranar Litinin a wani taron tsaro na jihar, ya ce sha’anin yan sa-kai shi ya ƙara haifar da matsala a Zamfara da jihohin da ke maƙwabtaka da ita.

    Ya ce suna yin gaban kansu ba tare da bin doka da oda ba. “Ba za mu ci gaba da kyalewa ba domin mun san illar hakan.”

    “Mun fito da doka da ta haramta ƴan sa-kai kuma duk wanda ke son taimakawa jami’an tsaro, to ya shiga aikin banga,” in ji gwamna Tambuwal.

    Sanarwar da ofishin gwamnan ta fitar ta ce duk wanda aka kama zai sha ɗaurin shekara 14 ko biyan tara ta naira 500,000.

    Dokar ta kuma ce duk wanda aka kama da makami a jihar zai sha ɗaurin shekara bakwai a gidan yari ko ya biya tarar naira 200,000.

    Gwamna Tambuwal ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakin ne domin magance matsalolin tsaro da ke damun jihar.

    Kuma matakan hanyoyi ne na inganta sha’anin aikin ƴan banga don taimakawa jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

  17. Ma’aikata na rige-rigen yin rigakafin korona a Najeriya

    Domin tabbatar da an yi wa ma’aikata rigakafin korona kafin cikar wa’adin gwamnatin Najeriya, rahotanni sun ce ma’aikata na rige-rigen yin rigakafi musamman a hukumomi da ma’aikatun gwamnati a Abuja.

    A ranar 1 ga watan Disamba gwamnatin Najeriya ta ce za a hana wa ma’aikatan da ba su yi rigakafin korona ba zuwa wurin aiki.

    Wannan ya sa ma’aikata da dama ke rige-rigen domin yin rigakafin korona kafin cikar wa’adin na gwamnati.

    Hukumomin Lafiya a Najeriya sun ce sun fara bi ofis zuwa ofis domin yi wa ma’aikatan gwamnati rigakafi.

    Wannan na zuwa yayin da hankalin duniya ya karkata kan barazanar sabon nau’in cutar korona da ake kira Omicron mai hatsari.

    Rigakafin Kano

    Asalin hoton, Reuters

  18. Ƴar majalisar da ta kai kanta asibiti a keke tana naƙuda

    JULIE ANNE

    Asalin hoton, JULIE ANNE GENTER FACEBOOK

    Wata ƴar majalisa a New Zealand ta kai kanta aisbiti saman keke a lokacin da take cikin naƙuda.

    Ta haihu bayan sa’a ɗaya da isa asibitin.

    “Ban yi tunanin zan yi amfani da keke ba ina naƙuda, amma hakan ta faru,” kamar yaddaJulie Anne Genter ta bayyana a Facebook.

    Ba wannan ne karon farko da ta yi haka ba – ta taɓa yi sherkaru uku da suka gabata.

    Ta yi suna wajen sha’awar tseren keke.

  19. Amurka za ta ruɓanya sojojinta da ke sa ido kan China da Rasha

    Sojojin Amurka

    Asalin hoton, EPA

    Ma'aikatar tsaro ta Amurka Pentagon ta ce Amurka za ta kara ruɓanya yawan sojojinta da ke sa ido kan China da Rasha, a ci gaba da yin garambawul ga tsarin tsaro da gwamnatin Joe Biden ke yi.

    Za a tura sojojin ne zuwa Guam da Australia.

    Sai dai wani jami'in gwamnatin Amurka ya ce ana yin yunƙurin ne da manufar tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro musamman bisa la'akari da dangantakar Amurka da China da kuma Koriya ta Arewa.

    Har wa yau, sabon tsarin zai yi zama kariya ga yiwuwar kai wa Turai hari daga Rasha da kuma aike da ƙarin sojoji zuwa Gabas ta Tsakiya domin kariya daga Iran da masu ikrarin Jihadi.

  20. Lionel Messi ya lashe Ballon d'Or karo na bakwai a tarihi

    Messi

    Dan kwallon tawagar Argentina mai taka leda a Paris St Germain, Lionel Messi ya lashe kyautar Ballon d'Or ta bana, karo na bakwai kenan a tarihi