Mataimaki na musamman kan kafafen yaɗa labarai ga Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, Salihu Tanko Yakasai ya ce gwamnatin Shugaba Buhari "ba ta tausayin 'yan Najeriya".
Salihu Yakasai na mayar da martani ne game da jan ƙafar da Buhari ya yi game da kiraye-kirayen da 'yan Najeriya ke yi na rushe rundunar SARS ta 'yan sanda sakamakon zargin cin zarafi da azabtarwa da ake zarginsu da yi.
Duk da cewa Buhari ya bayyana cewa ya gana da Sufeto Janar Mohammed Adamu a daren Juma'a tare da bayar da umarnin ɗaukar mataki, Salihu yana ganin ya kamata a ce Buhari ya yi wa 'yan Najeriya jawabi da bakinsa.
Fiye da mako ɗaya kenan da aka fara zanga-zanga da kiran rushe rundunar, sai a daren Juma'ar da ta gabata Buhari ya bayyana cewa ya gana da sufeto janar ɗin, yana mai cewa "wajibi ne a hukunta diuk ɗan sandan da ya aikata laifi".
Sai dai bayan sa'o'i, mataimakin na musamman ga Ganduje ya goge wasu daga cikin kalaman nasa amma mun samu hoton abin da ya goge ɗin.
"Ban taɓa ganin gwamnatin da ba ta tausayin al'ummarta ba kamar ta Muhammadu Buhari," in ji Salihu Yakasai a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Ya ci gaba da cewa: "A lokuta da dama ya gaza lallaɓa al'ummarsa [Buhari] da kwantar musu da hankali yayin da suke cikin tashin hankali.
"Ba za ka iya yi wa al'ummarka jawabi ba na minti biyar, waɗanda ka bi jihohi 36 kana barar ƙuri'unsu, ya zama kamar wata alfarma kake yi musu."
Ita ma Zahra Buhari da Kiki Osinbajo 'yar Mataiamkain Shugaban Ƙasa duk sun shiga fafutikar da aka fi yi a shafukan sada zumunta fiye da mako guda.
Gwamna Ganduje ya ci zaɓe sau biyu (2015 da 2019) a ƙarƙashin tutar jam'iyyar APC ta Buhari.