Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita
Rufewa,
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Litinin idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau:
An sanar da sakamakon ƙaramar hukuma 18 cikin 18 a zaɓen Ondo
Buhari ya taya Akeredolu murnar lashe zaɓen Ondo
Nadal ya lashe gasar French Open karo na 13
Yadda gwamnan Ondo Akeredolu ya fita murnar lashe zaɓe
'Yan bindiga sun kashe wani basarake a Kaduna
Shafin Twitter ya yi gargaɗi kan kalaman Trump
Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai
Sama da mutum miliyan tara na buƙatar agajin gaggawa a Sudan – MDD
Asalin hoton, EPA
Hukumar samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutum miliyan tara a Sudan na buƙatar agajin gaggawa sakamakon mummunar ambaliya.
Wannan adadiin na nufin kusan kashi ɗaya cikin huɗu na yawan al’ummar ƙasar ke cikin wani hali.
A wata hira da BBC, jami’in hukumar a Khartoum (Babagana Ahmadu), ya ce ambaliyar ta yi ɓarna sosai ga fannin noma inda ya ce ta lalata gonaki hecta miliyan uku da sama da miliyan na ton ɗin hatsi.
A watannin da suka gabata, sama da mutane ɗari suka mutu sakamakon ambaliyar wacce kuma ta lalata amfanin gonar da ake nomawa don fitarwa ƙasashen waje.
Sudan kuma na fuskantar matsalar tattalin arziƙi tare da ƙarancin man fetur.
Shafin Twitter ya yi gargaɗi kan kalaman Trump
Kamfanin Twitter ya yi gargaɗi ga masu amfani da shafin kan wani saƙon da Trump ya wallafa inda shafin ya ce saƙon na ƙunshe da bayanai da ke illa ga yaɗuwar cutar korona.
Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa ya samu cikakken tabbaci daga likitocinsa cewa ba zai iya sake kamuwa da cutar korona ba saboda yana kariya.
Trump ya shaida wa kafar watsa labarai ta Fox News cewa ba ya ɗauke da cutar bayan likitansa ya ce yanzu ba ya barazanar yaɗa cutar.
Mista Trump dai ya yi iƙirarin samun maganin korona inda kuma ya yi alƙawarin cewa zai raba wa Amurkawa maganin kyauta.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
'Yan bindiga sun kashe wani basarake a Kaduna
Asalin hoton, TWITTER/@ELRUFAI
Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe Mai Garin Runji Alhaji Musa Abubakar.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun afka gidansa ne da sanyin safiyar Lahadi a garin na Runji da ke Ƙaramar Hukumar Ikara ta Jihar Kaduna.
Jaridar ta ruwaito cewa ɗan mai garin, Suleiman Musa wanda shi ma mai gari ne a ƙauyen Rafin Rogo, shi ya tabbatar musu da wannan labari.
Haka zalika Kantoman Ƙaramar Hukumar Ikara, Salisu Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka kai jami'an tsaro ƙauyen na Runji tare da tabbatar da cewa za a gano waɗanda suke da hannu a kisan mai garin kuma a hukunta su.
Yadda gwamnan Ondo Akeredolu ya fita murnar lashe zaɓe
Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu, ya fito murna tare da magoya bayansa, jim kaɗan bayan hukumar INEC ta tabbatar masa da samun nasara.
Wannan ne karo na biyu da Mista Akeredolu ke lashe zaɓen gwamnan jihar ƙarƙashin inuwar Jam'iyyar APC.
Mista Akeredolu ya samu nasara ne kan babban abokin hamayyarsa na PDP wato Eyitayo Jegede.
Nadal ya lashe gasar French Open karo na 13
Asalin hoton, EPA
Rafael Nadal ya lashe gasar kwallon tennis ta French Open ta bana, bayan da ya doke Novak Djokovic ya kuma yi kan-kan-kan da Roger Federe wajen lashe manyan gasar tennis 20 jumulla.
Dan kasar Sifaniya wanda yake na biyu a jerin wadanda ke kan gaba a wasan a duniya, ya doke na daya wato Djokovic da ci 6-0, 6-2, 7-5 kuma karo na 13 da yake zama zakara a gasar.
Wannan ne karon farko da Djokovic, mai shekara 33 ya yi rashin nasara a dukkan fafatawar a kakar 2020.
Tun farko, Djokovic wanda ya lashe manyan gasar tennis 17, ya yi kokarin neman na 18 a Paris, hakan bai yi wu ba, bayan da Nadal ya yi nasara ya kuma lashe babbar gasa ta 20 kenan.
Nadal ya yi nasara ne bayan awa biyu da minti 41.
Matar da ta haihu sau biyu cikin wata biyar a Legas
Bayanan sautiLatsa alamar da lasifikar da ke sama domin sauraren shirin
Buhari ya taya Akeredolu murnar lashe zaɓen Ondo
Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi wa Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu murnar lashe zaɓen jihar.
Mai taimaka wa shugaban kan kafofin sada zumunta na zamani Bashir Ahmed ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce shugaban na taya Mista Akeredolu murnar sake zaɓensa na wasu shekaru huɗu.
A yau Lahadi ne dai hukumar zaɓe ta INEC a Najeriya ta bayyana Rotimi Akeredolu a matsayin ɗan takarar da ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Ondo a ranar Asabar.
Mista Akeredolu ya samu kuri'a 292,830, yayin da ɗan takarar jam'iyyar PDP, Mista Eyitayo Jegede yake biye masa da kuri'a 195,791, sai kuma dan takarar ZLP, Agboola Ajayi, wanda ya samu kuri'a 69,127.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Mahangar kimiyya da addini kan bangon duniya
A duk lokacin da aka ambato kalmar bangon duniya, abu na farko da ke faɗo wa mutane da dama a rai shi ne ƙasar China, wasu kuma sai su fara tunanin wani dogon bango da ya raba duniyar da muke ciki da wata duniyar ta daban.
A addinin Musulunci an yi batun wasu halittu da ake kira Yajuju wa Majuj da za su shigo daga bayan wata katanga, wadda mutane da yawa suka ɗauka cewa katangar ce bangon duniya.
Shin yaya abin yake? Haka kuma shin akwai bangon duniya a zahiri da gaske?
An sanar da sakamakon ƙaramar hukuma 18 cikin 18 a zaɓen Ondo
INEC ta sanar da sakamakon zaben karamar hukuma 18 cikin 18, abin da ya nuna cewa APC ta lashe karamar hukuma 15, yayin da PDP ta yi nasara a guda uku.
Gwamna Rotimi Akeredolu shi ne kan gaba a zaben yayin da dan takarar jam'iyyar PDP Eyitayo Jegede ke biye da shi.
Yanzu ana jiran INEC ta sanar da jumillar sakamakon tare da bayyana wanda ya lashe zaɓen.
APC ta lashe Ilaje
Ƙaramar Hukumar Ilaje
Adadin masu katin zaɓe: 134674 - Waɗanda aka tantance don kaɗa ƙuri'a: 44624
APC - 26657
PDP - 11128
ZLP - 4405
Labarai da dumi-dumi, An soke 'yan sandan SARS a Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta sanar da rushe rundunar SARS ta 'yan sandan Najeriya.
Sufeton 'Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu ne ya bayyana hakan a yau Lahadi yayin wani jawabi a Abuja, babban birnin ƙasar.
Gwamnatin Buhari ba ta da tausayin al'umma - Mai Bai wa Gwamna Ganduje Shawara
Asalin hoton, @dawisu
Mataimaki na musamman kan kafafen yaɗa labarai ga Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, Salihu Tanko Yakasai ya ce gwamnatin Shugaba Buhari "ba ta tausayin 'yan Najeriya".
Salihu Yakasai na mayar da martani ne game da jan ƙafar da Buhari ya yi game da kiraye-kirayen da 'yan Najeriya ke yi na rushe rundunar SARS ta 'yan sanda sakamakon zargin cin zarafi da azabtarwa da ake zarginsu da yi.
Duk da cewa Buhari ya bayyana cewa ya gana da Sufeto Janar Mohammed Adamu a daren Juma'a tare da bayar da umarnin ɗaukar mataki, Salihu yana ganin ya kamata a ce Buhari ya yi wa 'yan Najeriya jawabi da bakinsa.
Fiye da mako ɗaya kenan da aka fara zanga-zanga da kiran rushe rundunar, sai a daren Juma'ar da ta gabata Buhari ya bayyana cewa ya gana da sufeto janar ɗin, yana mai cewa "wajibi ne a hukunta diuk ɗan sandan da ya aikata laifi".
Sai dai bayan sa'o'i, mataimakin na musamman ga Ganduje ya goge wasu daga cikin kalaman nasa amma mun samu hoton abin da ya goge ɗin.
Asalin hoton, Twitter
"Ban taɓa ganin gwamnatin da ba ta tausayin al'ummarta ba kamar ta Muhammadu Buhari," in ji Salihu Yakasai a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Ya ci gaba da cewa: "A lokuta da dama ya gaza lallaɓa al'ummarsa [Buhari] da kwantar musu da hankali yayin da suke cikin tashin hankali.
"Ba za ka iya yi wa al'ummarka jawabi ba na minti biyar, waɗanda ka bi jihohi 36 kana barar ƙuri'unsu, ya zama kamar wata alfarma kake yi musu."
Ita ma Zahra Buhari da Kiki Osinbajo 'yar Mataiamkain Shugaban Ƙasa duk sun shiga fafutikar da aka fi yi a shafukan sada zumunta fiye da mako guda.
Gwamna Ganduje ya ci zaɓe sau biyu (2015 da 2019) a ƙarƙashin tutar jam'iyyar APC ta Buhari.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Ozil na goyon bayan masu fafutikar rushe 'yan sandan SARS a Najeriya
Asalin hoton, @MesutOzil1088
Tauraron ɗan wasan Arsenal Mesut Ozil ya mara wa masu fafutikar ganin bayan rundunar SARS ta 'yan sandan Najeriya baya.
Taurarin fina-finai da mawaƙa da 'yan ƙwallo ne suka bayyana goyon bayansu ga masu fafutikar da ke son a rusa rundunar SARS da ke yaƙi da 'yan fashi da manyan laifuka a Najeriya sakamakon zargin cin hanci da cin zarafi da azabtarwa da ake yi musu.
"Abin da ke faruwa a Najeriya abin tashin hankali ne," in ji Ozil a wani saƙon Twitter. "Ya kamata mu yi ta kwarzanta maganar a ko'ina da ina."
'Yar gidan Shugaban Najeriya Zahra Buhari da 'yar Mataiamkain Shugaban Ƙasa Kiki Osinbajo duk sun shiga fafutikar da aka fi yi a shafukan sada zumunta fiye da mako guda kenan.
Kazalika, mutane sun fita zanga-zanga a kan tituna, inda har aka kashe mutum ɗaya a Jihar Oyo da ke kudancin ƙasar a jiya Asabar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
APC ta lashe Odigbo
Ƙaramar Hukumar Odigbo
Adadin masu katin zaɓe: 134674 - Waɗanda aka tantance don kaɗa ƙuri'a: 43250
APC - 23571
PDP - 9485
ZLP - 6540
Ku kalli tattara sakamakon zaɓe kai-tsaye
Ku kalli tattara sakamakon zaɓen kai-tsaye a Facebook.
Mutum biyar sun mutu bayan jirgi biyu sun yi arangama a sama
Asalin hoton, Getty Images
Wasu ƙananan jirgi biyu sun yi arangama a sama sannan suka faɗo ƙasa a Faransa, abin da ya yi sanadiyyar rasa ran mutum biyar da ke cikinsu, a cewar hukumomi.
Haɗuwar jiragen ta auku ne a kudu maso gabashin birnin Tours da misalin ƙarfe 4:30 na ranar ƙasar - ƙarfe 3:30 agogon Najeriya da Nijar - ranar Asabar.
Ma'aikan agaji da kuma na kashe gobara kusan 50 ne suka isa wurin. Babu wanda ya jikkata bayan jiragen sun faɗo ƙasa.
Mafi ƙanƙantar jiragen wanda ke ɗauke da mutum biyu, ya faɗo ne a kan wayar da ke zagaye da wani gida a garin Loches.
Wani da ya shaida hatsarin ya faɗa wa AFP cewa jirgin ya kama da wuta jim kaɗan bayan ya faɗa kan mitar wutar lantarki ta gidan.
Ɗaya jirgin kuma ya faɗo da tazarar mita 100 tsakaninsu a wani fili. Yana ɗauke da mutum uku.
APC ta lashe Ondo West
Ondo West
Adadin masu katin zaɓe: 174104 - Waɗanda aka tantance don kaɗa ƙuri'a: 39890