Fursuna 300 ne Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa afuwa daga Gidan Gyara Hali na Goron Dutse da ke birnin Kanon domin rage haɗarin yaɗuwar cutar korona.
Gwamnan ya bayyana hakan ranar Idin Ƙaramar Sallah, wanda aka gudanar ranar Lahadi, inda ya ce ya yi musu afuwar ne bisa umarnin Gwamnatin Tarayya na rage cunkoso a gidajen gyara halin.
"Bisa umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar na rage cunkoso a gidajen gyara hali, na ziyarci Gidan Gyara Hali na Goron Dutse," in ji Ganduje, a wata sanarwa da ya wallafa a Twitter.
"An saki fursuna 300 masu ƙananan laifuka, inda gwamnati ta biya tarar da aka yanke musu. Mun yi hakan ne domin rage girman haɗarin yaɗuwar cuta."
Gwamnatin Tarayyar ce dai ta fara yin irin wannan yunƙuri, inda ta ce ta yi wa fursuna 2600 afuwa da nufin rage cunkoso, wanda ka iya haifar da yaɗuwar cutar korona a tsakanin ɗaurarrun.