Covid-19: An sallami ƙarin almajirai 44 a Gombe

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye kuma da dumi-duminsu game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya musamman masu alaka da annobar korona da ma karin wasu daban.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Rufewa

    A nan muka zo karshen labarai da rahotannin da muke gabatar muka gabatar a wannan rana.

    Sai ku tare mu gobe domi amun sabbin labarai. Kafin, za ku iya lekwa kasa don ganin wainar da aka toya a yau.

    Kada ku manta za ku iya bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta da muhawara inda za ku tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku.

    Mu kwana lafiya.

  2. Ibrahimovic ya ji rauni a ƙafarsa

    AC Milan ta ce dan wasanta Zlatan Ibrahimovic ya ji rauni a ƙafarsa lokacin da yake atisaye ranar Litinin.

    Rahotanni sun nuna cewa raunin da dan wasan mai shekara 39 dan kasar Sweden ya ji zai iya barazana ga sana'arsa ta kwallon kafa amma Milan ta shaida wa BBC Sport cewa za a yi masa gwaji ranar Talata.

    Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce "Za mu san girman matsalar a lokacin."

    Tsohon dan wasan na Manchester United Ibrahimovic ya koma Milan a watan Disamba a yarjejeniyar wata shida kuma ya zura kwallo hudu a wasa 10 da ya buga wa kungiyar.

    Zlatan Ibrahimovic

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Odion Ighalo yana shirin komawa China

    Odion Ighalo ya shirya komawa China idan zaman aron da yake yi Manchester United ya kare ranar 31 ga watan Mayu, domin har yanzu Shanghai Shenhua da United basu cimma matsaya kan tsawaita zamansa ba.

    United ta karbo aron dan wasan na Najeriya, mai shekara 30, a watan Janairu domin maye gurbin Marcus Rashford, wanda yake jinya.

    Sai dai saboda barkewar annobar korona, zaman aron da Ighalo yi zai kare kafin a kammala gasar Premier a watan Yuni, kuma a lokacin ne ake sa ran Rashford zai warke sosai ya koma tamaula.

    Da ma dai United ta riga ta yanke shawara cewa ba za ta sayi Ighalo dindindin ba, ko da yake bata yanke kaunar tsawaita zamansa na kankanen lokaci ba.

    Ighalo

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Shugaban Sudan ta Kudu 'bai kamu da cutar korona ba'

    Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir, ya musanta rahotannin da ake watsawa a shafukan sada zumunta cewa ya kamu da cutar korona kuma an fitar da shi kasar waje don yi masa magani.

    "Ba a sauya yadda shugaban kasa yake aiki ba. Bai kamata mutane su rika yarda da farfaganda ba," in ji Mr Kiir.

    Mako jiya, mataimakin Mr Kiir, Riek Machar da ministoci tara wadanda mambobi ne na kwamitin yaki da cutar korona, sun kamu da cutar.

    Tuni aka killace su.

    A jawabin da ya yi, Mr Kiir ya kuma yi gargadin kasar za ta fada "cikin mawuyacin hali" idan ba ta daike yaduwar cutar korona ba.

    Mr Kiir ya ce yanzu an tabbatar mutum 600 da suka kamu da cutar korona.

    Kiir

    Asalin hoton, AFP

  5. Najeriya ba ta da kuɗin da za ta shigo da kayan abinci daga waje - Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce dole manoman a kasar su kara dukufa wajen noma isasshen abincin da zai wadatar da kasar, saboda gwamnati ba ta da kudin da za ta iya shigo a abinci daga wajen.

    Shugaba Buhari ya ba da wannan shawarar ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a fadar gwamnatin kasar bayan idar da sallar Idi.

    Bayanin nasa na zuwa ne lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan karancin abinci da ake fama da shi a wannan lokacin a annobar korona, da kuma tashin farashin kayan abincin a kasar mafi yawan jama’a a yammacin Afrika.

    Buhari

    Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

  6. Covid-19: An sallami ƙarin almajirai 44 a Gombe

    Gwamnatin jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce ta sallami karin almajirai 44 daga wurin killace masu dauke da cutar korona bayan bincike ya nuna ba sa dauke da cutar.

    Sanarwar da Ismaila Uba Misilli, mai magana da yawun Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya aike wa manema labarai ranar Litinin, ta ce wadanda aka sallama suna cikin almajirai 64 da aka killace tsawon mako biyu a wurin killace masu cutar korona mai suna Amanda da ke jihar.

    "Yara arba'in da hudu da aka sallama yau suna cikin rukunin yara sittin da hudu da aka killace, yanzu sauran yara goma sha biyu suna jiran sakamako gwajin da aka yi musu wanda zai fito anjima a yau," a cewar Uba Misilli.

    Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bukaci 'yan jihar su daina tsangwamar su yana mai cewa "wadannan almajiran 'ya'yan jihar nan ne".

    Inuwa Yahaya

    Asalin hoton, Twitter

  7. Babu maganar nesa-nesa da juna a Amurka yayin bikin Memorial Day

    Amurkawa ba su kula da dokar nesa-nesa da juna ba a bakin ruwa yayin bikin ranar Memorial Day a ƙarshen makon nan, wanda ake yi a farkon shigowar yanayin bazara.

    Duk da hauhawar yawan adadin masu kamuwa da kuma mutuwa sakamakon cutar korona - miliyan 1.6 da kuma 97,722 - wasu Amurkawa sun yi cincifrundo a wuraren yin wanka.

    Wuraren na gaɓar teku a California sun dawo bakin aiki saboda hutun na ƙarshen mako

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Wuraren wanka na gaɓar teku a California sun dawo bakin aiki saboda hutun na ƙarshen mako
    Masu wanka a bakin ruwa sun yi wa Cocoa Beach tsinke da ke Florida

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Masu wanka a bakin ruwa sun yi wa Cocoa Beach tsinke da a Florida
    Mazauna California sun yi ta wasa a wasa a ruwa ranar Asabar

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mazauna California sun yi ta wasa a ruwa ranar Asabar
  8. Jam'iyya mai mulki ta lashe zaben shugaban kasa a Burundi

    Evariste Ndayishimiye

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Evariste Ndayishimiye Janar din soja ne mai ritaya

    Hukumomi a Burundi sun ce dan takarar jam'iyyar da ke mulki a kasar ne ya lashe zaben shugaban kasar.

    Hukumar zaben kasar ta ce Evariste Ndayishimiye ya yi nasara da kusan kashi 70 cikin 100 na kuri'un da aka kada makon jiya.

    Janar din soja mai ritaya zai maye gurbin Shugaba Pierre Nkurunziza, wanda yake shugabancin kasar tun shekarar 2005.

    Ana hasashen tsohon shugaban kasar zai rika juya akalar sabuwar gwamnati.

    Babbar jam'iyyar hamayya ta nuna shakkunta game da sakamakon zaben, wanda ya ce dan takararta, Agathon Rwasa, ya samu kashi daya bisa hudu na kuri'un da aka kada a zaben - galibi daga Yammacin kasar inda take da magoya baya sosai.

  9. 'Yar wasan Najeriya Asisat Oshoala na son zama 'Bahaushiya'

    'Yar ƙwallon Najeriya mai buga wa ƙungiyar mata ta Barcelona wasa, Asissat Oshoala ta nuna sha'awarta ta zama "Bahaushiya" a shafinta na Twitter ta hanyar amfani da maudu'in #ArewaTwitter.

    Hakan ya faru ne bayan tauraruwar 'yar wasan ta wallafa hotunan wasu 'yan mata sanye da kaya irin na Hausawa na kwalliyar Idi sannan ta maƙala maudu'in #ArewaTwitter tana cewa:

    "Ina da 'yan uwa masu kyau, 'yan Arewa muna son zama kamarku."

    Asisat Oshoala 'yar asalin Jihar Legas ce da ke kudancin Najeriya kuma Musulma.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. Mutum biyu sun kamu da korona a Mauritius karon farko cikin wata ɗaya

    Mauritius

    Asalin hoton, Seafarers in a Norwegian Cruise Line

    Bayan kwana 28 ba tare da samun wanda ya kamu da cutar korona ba, Mauritius ta bayar da rohon samun mutum biyu da suka harbu da ita ranar Lahadi.

    Mutum biyun na cikin 'yan ƙasar 149 da aka ɗebo daga Indiya ranar 9 ga watan Mayu, ciki har da jarirai uku.

    Wannan na zuwa ne mako biyu bayan Ministan Lafiya Kailesh Jagutpal ya ce sun kawo ƙarshen cutar a ƙasar da ke kan tsibiri, duk da cewa ya jaddada cewa ba a gama yaƙi da ita ba.

    A wannan makon ne Firaminista Pravind Jugnauth zai yi jawabi game da "matakan tsafta", waɗanda aka tsawaita zuwa 1 ga watan Yuni.

  11. An mayar da 'yan mata 50 da aka yi safararsu daga Najeriya zuwa gida

    'Yan Najeriya daga Lebanon

    Asalin hoton, @nidcom_gov

    Gwamnatin Najeriya ta kwaso 'yan ƙasarta 69 daga ƙasar Lebanon zuwa gida ranar Lahadi, a ci gaba da ɗebe mutanen da take yi sakamakon maƙalewa da suka yi saboda dokar kulle a wasu ƙasashe.

    Mutum 50 daga cikinsu, 'yan mata ne da aka yi safararsu da kuma 19 da suka kasa komawa gida daga ƙasar, kamar yadda Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyeama ya bayyana a shafinsa na Twitter.

    Onyeama ya gode wa jakadan Lebanon a Najeriya, Houssam Diad wanda ya ce da haɗin gwiwar gwamnatin ƙasarsa aka yi nasarar ɗebo su.

    Kazalika ya gode wa jakadan Najeriya a Lebanon, Goni Zannabura.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. Idris Elba zai haɗa casu ta intanet don taimaka wa talakawan Afirka

    Idris Elba

    Asalin hoton, Getty Images

    Tauraron fina-finai Idris Elba zai haɗa kan wasu shahararrun mawaƙan Afirka domin yin taron casu ta intanet a bikin Ranar Afirka, inda za a tara kuɗi domin kula da marasa ƙarfi a Nahiyar Afirka.

    Casun wanda gidan talabijin na MTV Base zai shirya mai taken MTV Base Africa Day Benefit Concert at Home, zai tara fitattun mawaƙa irinsu Burna Boy da Davido da Tiwa Savage da Angélique Kidjo da Diamond Platnumz da Sauti Sol.

    Za a nuna a shafin YouTube da kafar ViacomCBS.

    Idris Elba ya faɗa wa BBC cewa yana fatan wannan yunƙuri nasa zai taimaki Afirka.

  13. Indiyawa sun yi tururuwa zuwa filayen jirgi bayan dawo da zirga-zirga tsakanin jihohi

    India

    Asalin hoton, Getty Images

    Dogayen layuka da hayaniya sun mamaye filayen jirgin sama a Indiya, yayin da ƙasar ta buɗe zirga-zirga tsakanin jihohi bayan wata biyu da rufewa sakamakon annobar korona.

    Sai dai an soke gomman jirage daga tashi, abin da ya bar dubban fasinjoji zube ba su san na yi ba.

    Ƙasar ta ƙara tsaurara matakan kariya a shirin da take yi na buɗe harkoki.

    Ana gwada zafin jikin mutane a filin jirgi sannan jami'an tsaro suna dubawa ko mutane sun sauke manhajar bin sawun cutar a wayoyinsu, wadda gwamnati ta amince da ita.

    Sauran matakan sun haɗa da yin feshi a takalma da kuma jakar hannu.

  14. Za a iya barin tazara a sansanonin 'yan gudun hijra?

    'Yan gudun hijira

    Asalin hoton, EPA

    "Barin tazara ba zai yiwu ba idan mutanen da suka rasa muhallansu na rayuwa a sansanoni," in ji Marshal Makavure, jami'i a kungiyar IFRC ta Gabashin Afrika.

    "An tursasa wa mutane karya dokokin Covid-19 saboda halin da suke ciki."

    BBC ta yi Magana da mutanen da ke zaune a yankunan da ke fama da matsanancin yanayi.

  15. Za a sauya wa 'yan sanda masu tumbi wurin aiki a Tanzania

    Ɗan sanda

    Asalin hoton, @OlengurumwaO

    'Yan sandan da ke bayar da hannu masu tumbi a Tanzania za su fuskanci sauyin wurin aiki saboda suna kunyata aikin ɗan sanda, a cewar Ministan Cikin Gida, George Simbachewere.

    Wata kafar yaɗa labaran ƙasar ta ruwaito shi yana faɗa a ƙarshen mako:

    Mista Simbachewere ya umarci babban sufeton 'yan sanda da ya sauya wa 'yan sandan wurin aiki.

    Wani mai rajin kare haƙƙin dan Adam ya yi kira da kada hakan ya kai ga nuna musu wariya.

  16. Za a samu tsawa da hasken rana a Najeriya daga Litinin zuwa Laraba – NiMet

    Yanayin tsawa

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Hukumar Nazarin Yanayi ta Najeriya, Nigerian Meteorological Agency (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu hasken rana da kuma tsawa a faɗin ƙasar daga Litinin zuwa Laraba.

    A wani rahoton hasashen da ta fitar a Abuja ranar Lahadi wanda kuma kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito, NiMet ta ce za a samu yanayin hadari da kuma hasken rana a lokaci guda a sararin samaniyar yankin arewa daga Litinin zuwa Laraba.

    Kazalika akwai hasashen samun tsawa maras yawa a Kudancin Jihar Borno da jihohin Taraba da Bauchi da Kaduna da Adamawa.

    A jihohin tsakiyar Najeriya kuma, NiMet ta ce akwai yiwuwar samun tsawar da safe a Abuja da Nassarawa da Kogi.

  17. An buɗe manyan wuraren ziyarar addini a Iran

    Iran

    Asalin hoton, AFP

    Iran ta buɗe manyan wuraren ibada kamar ƙaburbura - ciki har da na Imam Reza Mashhad da Hazrat Masumeh da ke Qom - wata biyu bayan kulle su sakamakon annobar korona.

    Za a ƙyale mutane su shiga farfajiyar wuraren amma ban da cikin ɗakuna. Sannan kuma za a buƙaci su bi dokokin tsafta da na nesa-nesa da juna.

    Za a rika buɗe su ne sa'a ɗaya bayan asuba kuma a kulle su sa'a ɗaya kafin faɗuwar rana.

    Iran

    Asalin hoton, AFP

  18. Labarai da dumi-dumi, Japan ta ɗage dokar-ta-baci

    Shinzo Abe

    Asalin hoton, Japan Prime Minister's Office

    Firaministan Japan, Shinzo Abe ya ɗage dokar-ta-ɓaci a faɗin ƙasar, inda ya kawo ƙarshen dokar kullen da ke aiki a wasu sassa.

    "Mun shimfiɗa tsauraran sharuɗɗan ɗage dokar-ta-ɓaci. Mun yi amannar cewa mun cika waɗannan sharuɗɗa," in ji Shinzo Abe a wani jawabi da ya yi ranar Litinin.

    Firaministan ya ce sun samu ikon daƙile yaɗuwar cutar tun bayan saka dokar a wasu sassan kasar ranar 7 ga watan Afrilu.

    Japan ba ta samu yawan masu cutar korona ba idan aka kwatanta da sauran manyan ƙasashen duniya. Zuwa Litinin, mutum 820 ne suka rasu sakamakon cutar da kuma 16,550 da suka kamu da ita.

  19. Shin El Rufai ya tare a mashigar Kaduna daga Kano?

    Nasir El-Rufai

    Asalin hoton, @elrufai

    Malam Nasir Ahmad El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna, ya shafe ranakun Juma'a da Asabar a kan iyakar Kaduna da Kano domin tabbatar da dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi.

    Da ma El-Rufai ya lashi takobin cewa babu wanda zai shigar masa jiha daga Kano, biyo bayan matakin da Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya ɗauka na ci gaba da yin sallar Juma'a da kuma ta Idi a Kanon.

  20. Ganduje ya yi wa fursuna 300 afuwa a Kano

    Gwamna Ganduje

    Asalin hoton, @GovUmarGanduje

    Fursuna 300 ne Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa afuwa daga Gidan Gyara Hali na Goron Dutse da ke birnin Kanon domin rage haɗarin yaɗuwar cutar korona.

    Gwamnan ya bayyana hakan ranar Idin Ƙaramar Sallah, wanda aka gudanar ranar Lahadi, inda ya ce ya yi musu afuwar ne bisa umarnin Gwamnatin Tarayya na rage cunkoso a gidajen gyara halin.

    "Bisa umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar na rage cunkoso a gidajen gyara hali, na ziyarci Gidan Gyara Hali na Goron Dutse," in ji Ganduje, a wata sanarwa da ya wallafa a Twitter.

    "An saki fursuna 300 masu ƙananan laifuka, inda gwamnati ta biya tarar da aka yanke musu. Mun yi hakan ne domin rage girman haɗarin yaɗuwar cuta."

    Gwamnatin Tarayyar ce dai ta fara yin irin wannan yunƙuri, inda ta ce ta yi wa fursuna 2600 afuwa da nufin rage cunkoso, wanda ka iya haifar da yaɗuwar cutar korona a tsakanin ɗaurarrun.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X