Sai da safe
Nan za mu gintse rahotonnin a wannan shafi na labarai kai-tsaye na ranar Talata.
Za mu kawo muku wasu rahotonnin da suka shafi rayuwarku gobe da safe a wani shafin.
Umar Mikail ke yi muku fatan mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/09/2024
Daga Aisha Babangida, Buhari Muhammad Fagge, Haruna Kakangi, da Umar Mikail
Nan za mu gintse rahotonnin a wannan shafi na labarai kai-tsaye na ranar Talata.
Za mu kawo muku wasu rahotonnin da suka shafi rayuwarku gobe da safe a wani shafin.
Umar Mikail ke yi muku fatan mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Hukumomin Ukraine sun ce sama da mutum 50 ne aka tabbatar da mutuwarsu, kuma wasu fiye da 200 suka jikkata bayan wani harin makamai masu linzami da Rasha ta kai.
Hukumomin Ukraine sun ce hare-haren sun faɗa kan kwalejin soji da kuma wani asibiti da ke kusa da birnin Poltava.
Wata ƴarmajalisar dokokin Ukraine - Inna Sovsun - ta ce dole ne Ukraine ta samu damar kai hari cikin kasar Rasha domin kawo ƙarshen asarar rayukan da take yi.
"Ba za mu iya tunanin za mu yi nasara a wannan yaƙin ba, ko kuma cewa za mu iya dakatar da duk waɗannan kashe-kashen da muke gani kowace rana a nan Ukraine na tsawon shekaru biyu da rabi ba idan har ba za mu kai hari cikin Rasha ba," in ji ta.

Asalin hoton, Reuters
Daya daga cikin hari mafi muni da ya janyo mutuwar darururwan mutane a Burkina Faso, ya janyo fushi daga yan kasar da ke ganin gazawar gwamnatin soji, da ta lashi takobin kawo karshen matsalolin tsaron da kasar ke fama da su.
Masu dauke da makamai ne suka kashe mutanen sama da 400 a ranar 24 ga watan Agustan nan a wani kauye da ake kira Barsologho, da ke arewa maso tsakiyar kasar, lokacin da suke haka ramukan buya, da sojoji suka basu shawarar samarwa.
Wannan mummunan hari mai tayar da hankali, a iya cewa shine mafi muni, tun bayan da kungiyar da ke da alaka da alkaida ta yadu daga Mali zuwa Burkina Fason, a wajajen shekarar 2015.
Wannan mummunan kaye ne ga gwamnatin soja ta Ibrahim Traore, wadda ta ce za ta kawo karshen kungiyar ko ana há maza há mata. Bayan wannan hari, gwamnatin tabatarrar da lallai na rasa rayuka, to amma ta ki bayar da adadin wadanda suka mutun.
Babban limamin cocin Katolica mafi girma a kasar da ke birnin Wagadugu Jean Emmanuel Konvolbo, ya yi Allah wadarai da gwamnatin sojin, yana mai bayyana martaninta a matsayin borin kunya.
A cewarsa ‘’Rashin daukar mataki game da irin wadannan kashe kashe da ake samu dai dai yake da taimakawa masu yunkurin karar da bani adama, dole ne kowa ya nuna takaicinsa’’.
Wata kungiyar yan uwan wadanda harin ya rutsa da su dai ta ce adadin wadanda suka mutum ya haura mutum dari hudu.
Kunigyar ta zargi gwamnatin soja da kokarin rufe bakin duk wanda y aso nuna damuwa ko bacin rai game da abubuwan da ke faruwa a kasar, alhalin su kuma sun lullube komai.
Ta ba da misali da wani yunkuri da sojoji suka yi na kama wani dan gwagwarmaya da sautins aya yadu yana sukar sakacin da aka yi har aka kai harin.
Har ta kai ga jama’a suka shiga lamarin suka hana sojojin tafiya da shi ta karfi da yaji.

Asalin hoton, Channels TV
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago a Najeriya ta Nigeria Labour Congress (NLC) ta zargi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da karya yarjejeniyar da suka ƙulla kafin sanar da ƙarin farashin man fetur ranar Talata.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a yammacin yau Talata ta ce ɗaya daga cikin dalilan da suka sa suka amince da naira 70,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi a watan Yuli shi ne ba za a ƙara kuɗin fetur ba.
"Muna sane da zaɓin da shugaban ƙasa ya ba mu cewa ko dai a ba mu N250,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi [amma a ƙara farashin fetur zuwa N1,500 ko N2,000] ko kuma N70,000 [a bar farashin yadda yake]," a cewar NLC.
"Mun zaɓi na biyun saboda ba za mu juri a cigaba da azabtar da 'yan Najeriya ba. Amma...yanzu ga shi ko sabon albashin ba a fara biya ba an sake zuwa mana da abin da ba za mu iya fahimta ba."
Ƙungiyar ta bayyana ƙarin a matsayin "abin takaici" kuma "mai banhaushi".
Da safiyar yau ne dai kamfanin mai na NNPCL na gwamnatin Najeriya ya sanar da sauya farashin daga N617 zuwa N897 kan kowace lita, abin da ya sa 'yan Najeriya da dama suka nuna ɓacin ransu.

Asalin hoton, Katsina State Government
An gudanar da janai'zar Hajiya Fatima Ƴar'adua, mahaifiyar tsohon shugaban Najeriya, marigayi Umaru Musa Ƴar'adua yau Talata a birnin Katsina.

Asalin hoton, Katsina State Government
Manyan jami'an gwamnati da ƴan siyasa na cikin waɗanda suka halarci jana'aizar, ciki har da mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima.

Asalin hoton, Katsina State Government
Haka nan akwai jagoran ƴan adawa a Najeriya, Atiku Abubakar da kuma ɗan takarar jam'iyyar LP a zaɓen shekara ta 2023.

Asalin hoton, Katsina State Government
Hajiya Dada ta rasu ne a jiya Litinin, 2 ga watan Satumba, 2024 a birnin Katsina tana da shekara 100 a duniya.
Hukumomi a jihar Yobe da ke arewa masu gabashin Najeriya sun tabbatar da cewa an kashe mutum aƙalla 81 a harin da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai a garin Mafa da ke ƙaramar hukumar Tarmuwa.
A ranar Talata, mai magana da yawun ƴansanda a jihar Yobe, Abdulkarim Dungus ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "mayaƙan da ake zargin ƴan Boko Haram ne kimanin 150 a kan babura ne suka dirar wa garin na Mafa, ɗauke da manyan makamai a ranar Lahadi."
Ya ƙara da cewa maharan sun "kashe mutane da dama da ƙona shaguna da gidaje, sai dai har yanzu ba mu kammala tattara ɓarnar da suka yi ba."
Sai dai wani jami'i, Bulama Jalaludden ya bayyana cewa "mun tabbatar da cewa an kashe aƙalla mutum 81 daga lissafin da muka yi.
A yau Talata ne aka gudanar da jana'izar wasu daga cikin mutanen da suka rasu a harin na ranar Lahadi.

Asalin hoton, STATE HOUSE
A ci gaba da ziyarar da yake yi a ƙasar China, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wata ganawa da shugaban ƙasar China Xi Jinping a yau Talata.
Ganawar ta wakana ne a Beijing, babban birnin ƙasar ta China.
A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun shugaba Tinubu, Ajuri Naglale ya ce shugabannin biyu sun amince da yauƙaƙa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu zuwa matakin amintaka.
A cikin bayaninsa, shugaba Tinubu ya ce "Wannan ziyara ce mai matuƙar muhimmanci ga Najeriya da kuma Afirka baki ɗaya, kasancewar na zo nan ne a matsayi na na shugaban ƙungiyar haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasashen Afirka (Ecowas)."
"Dangantakar da ke tsakanin Najeriya da China ta daɗe, kimanin rabin ƙarni, saboda haka akwai buƙatar a ƙara ƙarfafa wannan dangantaka domin bunƙasa harkar kasuwanci da ci gaban tattalin arziƙi," in ji Tinubu.
Ya ƙara da cewa akwai damarmaki sosai a Najeriya kasancewar ta ƙasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, wadda kuma ke da ɗinbin matasa da za su taimaka wajen ciyar da tattalin arziƙi gaba.
Tinubu na ziyara ne a China a domin halartar taron bunƙasa hulɗa tsakanin ƙasashen Afirka da China.

Asalin hoton, STATE HOUSE

Asalin hoton, PRESIDENCY
Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata zargin da ake na rashin jituwar da ke tsakanin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, inda ta bayyana cewa dangantakar shugabannin biyu na nan da ƙarfinta.
Babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa ga mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a bikin cika shekaru 58 na mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima.
Nkwocha ya bayyana zargin a matsayin "makirci mara tushe waɗanda ba su nuna gaskiyar lamari a Aso Rock".
Sanarwar ta jaddada cewa Shettima wani muhimmin ɓangare ne na gwamnatin Tinubu inda yake bai wa Tinubu cikakken goyon baya da kuma ƙwarin gwiwa.

Asalin hoton, Alamy
Hoton ne ya sa da gani za a gane cewa jirgin na Titanic ne- jirgin ya ƙara tunsurewa yana ƙara bayyana daga cikin duhun tekun.
Sai dai wani sabon bincike ya gano yadda zagwanyewar jirgin ke tafiyar hawaniya, inda har yanzu mafi yawansa ke zirya a ƙarƙashin tekun.
An gano wasu sassan jirgin ne- wanda aka fim wanda Jack da Rose suka taka rawa a ciki- bayan wasu masu bincike sun kai ga wajen da jirgin ya maƙale a bana. Hotunan da suka ɗauko sun nuna yadda jikin jirgin ke canjawa bayan sama da shekara 100 a ƙarƙashin ruwa.
Jirgin ya kife ne a Afrilun 1912 bayan ya ci karo da ƙanƙara, inda mutum 1,500 suka mutu.

Asalin hoton, Getty Images
A jihar Kano, ana fargabar mutum fiye da 20 sun mutu sakamakon ɓarkewar cutar kwalara a wasu ƙauyuka.
Bayanai na cewa lamarin ya auku ne sanadiyyar gurɓacewar ruwa sakamakon ambaliyar ruwa kuma kawo yanzu mutum fiye da ɗari ne suka kamu da cutar a ƙauyuka biyu, inda wasu ke karɓar magani.
Bayanan da BBC ta tattaro daga kauyukan Mikiya da Ballagaza cikin karamar hukumar Gabasawa a jihar Kano na cewa mutanen garin sun fara ganin waɗanda suka harbu da cutar amai da gudawar ne bayan da aka yi mamakon ruwan sama tun a makon jiya.
Baya ga larurar amai da gudawar dai yanzu haka hukumomi a Kanon, sun ce suna bin diddigi da bincike bayan mutuwar fiye da mutum 40 sakamakon kamuwa da cutar mashaƙo akasari ƙananan yara.

Asalin hoton, Ministry of defence
Ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle tare da Babban Hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa sun isa jihar Sokoto domin ba da gudummawa wajen murƙushe ƴan fashin daji da ke addabar yankin arewa maso yammacin ƙasar.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne ya bai wa ministan da manyan hafsoshin tsaron ƙasar umarnin mayar da ayyukansu zuwa Sokoto bayan ƙaruwar ayyukan ƴan fashin daji a baya-bayan nan.
Duk da dai iƙirarin da gwamnatin Najeriya ke yi na cewar tana samun nasarori wajen yaƙi da matsalar tsaro da ake fama da ita a sassan ƙasar da dama, har yanzu dai ana ci gaba da samun kai hare hare.

Asalin hoton, Ministry of defence

Asalin hoton, Ministry of defence

Asalin hoton, Getty Images
Najeriya na ci gaba da fama da matsalar karancin abinci, yayin da sabbin bayanai daga cibiyar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEOC) suka nuna cewa ambaliyar ruwa ta lalata gonaki sama da hekta 115,000 a faɗin ƙasar.
Jihohi 29 da ƙananan hukumomi 154 ne abin ya shafa, inda sama da mutum 611,000 lamarin ya shafa kai tsaye, mutum 225,169 suka rasa matsugunansu, gidaje 83,457 ne suka lalace, mutum 201 ne kuma suka rasa rayukansu sannan mutum 2,119 kuma suka samu raunuka a bana.
Wannan bayanin na ambaliya ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da ƙarancin abinci da kuma ƙaruwar hauhawar farashin kayan abincin, wanda hukumar kididdiga ta Najeriyan (NBS) ta bayyana ya hau sama da kashi 40 cikin 100.
Wani sabon bincike da babban bankin Najeriya CBN ya gudanar daga ranar 22 zuwa 26 ga Yulin 2024 ya nuna cewa, hauhawar farashin kayayyaki zai tilastawa magidanta a Najeriya kashe mafi yawan kuɗaɗen shigarsu kan abinci nan da watanni shida masu zuwa.

Asalin hoton, Reuters
Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce shawarar Burtaniya ta dakatar da sayar wa da kasarsa wasu makamai abin "kunya" ne.
"Maimakon kasancewa tare da Isra'ila, abokiyar dimokraɗiyya da ke kare kanta daga dabbanci, goyon bayan Hamas da Burtaniya ta yi zai ƙara wa ƙungiyar ƙwarin gwiwa ne", kamar yadda ya faɗa a shafinsa na soshiyal midiya.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan da sakataren tsaron Burtaniya, John Healey ya tsaya kai da fata cewa Burtaniya za ta ci gaba da kasancewa "ƙawa ta ƙut" ga Isra'ila, inda ya ƙara da shaida wa BBC cewa tsaron Isra'ila ba zai raunana ba ta hanyar dakatar da sayar da makamai kaso 30 daga cikin 350.
Ministocin sun ce za a iya amfani da makaman a Gaza wajen ketaƙa'idojin ƙasa da ƙasa. Sai dai kuma ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International a Burtaniya ta ce matakin da aka ɗauka "bai taka kara ya karya" ba.
Sauran sun yi kakkausan suka dangane da lokacin da aka sanar da dakatar da sayar da makaman wanda ya zo daidai da ranar da ake binne mutane shida da Hamas ta yi garkuwa da su waɗanda aka samu damar mayar da gawarsu gida a makon da ya gabata.

Asalin hoton, Getty Images
Yarjejeniyar soji tsakanin Somaliya da Masar ta haifar da fargabar yiwuwar rikici kai tsaye a yankin Afirka, yayin da Alkahira ke kara matsa kaimi ga Habasha kan rikicin madatsar ruwan Nilu.
Tashin hankali ya ɓarke ne a cikin watan Janairu lokacin da Habasha ta sanar da aniyar amincewa da Jamhuriyar Somaliland da ta ayyana kanta a matsayin kasa mai cin gashin kanta domin samun damar shiga teku.
Wannan matakin ya firgita Masar, wacce ke taka-tsan-tsan da shirin Habasha na kafa sansanin sojin ruwa a mashigin tekun Aden.
A martanin da ta mayar, Somaliya ta yi Allah wadai da yarjejeniyar, yayin da Masar ta yi amfani da damar da ta samu wajen kalubalantar Habasha a rikicin da ke tsakaninsu na madatsar ruwan Nilu inda ta aika da jiragen yaƙi guda biyu zuwa Mogadishu a ranar 26 ga watan Agusta, abin da ya kara tayar da hankula a Addis Ababa.
Habasha ta yi gargadin cewa, ba za ta “tsaya tana kallo ba yayin da sauran masu ruwa da tsaki ke daukar matakan da za su dagula al’amura a yankin.
Habasha ta kuma ta fara tattara sojoji a kan iyakar Somaliya, lamarin da ke ƙara nuna fargabar ɓarkewar rikici a yankin.

Asalin hoton, EPA
Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya kai ziyararsa ta farko zuwa Mongolia, wata ƙasa da ke memba a kotun ƙasashen duniya ta ICC tun bayan da kotun ta bayar da sammacin kama shi a bara.
Duk da wannan sammacin, wanda ke zargin Putin da korar yaran Ukraine ba bisa ka'ida ba, fadar Kremlin ba ta nuna damuwa game da yuwuwar kama shi ba a yayin tafiyar.
Shugaban ƙasar Mongoliya ne ya tarbe shi a wani gagarumin biki da aka yi a Ulaanbaatar babban birnin ƙasar Asiya a ranar Talata.
Sojoji a kan dawakai sun yi jerin gwano a dandalin Genghis Khan na babban birnin ƙasar, yayin da wata tawagar makaɗa ke rera waƙoƙin yaki domin tarbar shugaban na Rasha,
Sai dai a ranar Litinin da yamma, wasu tsirarun gungun masu zanga-zanga sun taru a dandalin, ɗauke da alamomin da ke cewa "Ku fitar da Putin daga ƙasarmu, mai laifin yaki."
Ana kuma shirin yin wata zanga-zanga da tsakar ranar Talata a wurin tuna wa da waɗanda ake dannewa a siyasance a Ulaanbaatar, wurin da aka keɓe ga waɗanda suka sha wahala a ƙarƙashin mulkin gurguzu na Tarayyar Soviet ta Mongoliya.
Jami'an tsaro sun hana sauran masu zanga-zangar kusanci da Putin a lokacin da ya isa ƙasar.
A baya dai Ukraine ta buƙaci Mongoliya da ta tsare shugaban na Rasha gabanin ziyarar tasa.

Asalin hoton, ERIC PIERMONT
Mai kamfanin Matatar man fetur ta Dangote, Aliko Dangote ya sanar da cewa da zarar kamfaninsa ya kammala wasu muhimman abubuwa da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), man fetur ɗin kamfanin nasa zai shiga kasuwa.
Hamshakin ɗan kasuwar ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a ranar Talata, biyo bayan kaddamar da kason farko na man daga matatar kamfanin mai ganga 650,000 a kowace rana.
Dangote ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za su iya sa ran samun man fetur mai inganci da daɗewa
"Ba za ku ƙara fuskantar matsalolin da injinan motoci ke baku ba," in ji Dangote.
“Man fetur ɗin mu zai yi daidai da na kowace ƙasa a duniya; babu wanda zai wuce mu ta fuskar inganci,” in ji shi.
Dangote ya jaddada fa'idar tattalin arzikin da ayyukan matatar kamfanin ke da su, inda ya bayyana cewa za ta taimaka wajen farfado da masana'antu a Najeriya tare da daidaita darajar naira da kuma taimakawa wajen rage hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa,” in ji shi.
Matatar mai ta Dangote da ke Legas ta dala biliyan 20, ta fara aiki a watan Disambar da ya gabata.

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan gaban Urguay Luis Suarez ya yi ritaya daga bugawa ƙasarsa kwallo.
Dan wasan mai shekara 37 ya ɓarke da kuka lokacin da yake sanar da cewa wasan da zai bugawa ƙasarsa a ranar Asabar na neman gurbi a kofin duniya da Paraguay zai zama na ƙarshe a tarihi.
Tsohon ɗan wasan Liverpool da Barcelona wanda kuma shi ne ya fi kowa cin kwallo a tarihin Urguay inda ya ci kwallo 69 a wasa 142 da ya buga, ya kuma fara bugawa Uruguay wasa ne a 2007 a wasan Urguay da Colombia.
"Na yi ta tunanin kan wannan matakin ina ta hasashen yadda za a yi. A ganina wannan ne lokacin da ya kamata," in ji Suarez.
"Ina son hutawa idan na gama wasana na ƙarshe. Ina son jin dadin wasan irin wanda na ji ranar da na fara buga wasa a 2007," in ji shi.

Asalin hoton, NNPCL
Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya sanar da sabon farashin litar man fetir. A wata sanarwa da kamfanin ya aike wa manema labarai, kamfanin ya ce daga yau ranar 3 ga watan Satumban 2024, kamfanin ya ƙara kuɗin litar man fetir daga naira 617 zuwa 897.
Tuni dai wasu gidajen maI a Najeriya suka sauya farashin litar zuwa sabon da kamfanin ya sanar a ranar ta Talata.
Wannan dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan da kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa yana fuskantar matsalar ƙarancin kuɗi, wani abu da ya sa ƴan Najeriya hasashen kamfanin na koƙarin sanar da sabon farashi ne.
Da ma dai kafin sanar da sabon farashin na ranar Talata, dogayen layukan ababan hawa sun mamaye gidajen mai a biranen Abuja da Legas.
Tun dai bayan da gwamnatin shugaba Tinubu ta sanar da janye tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ƴan Najeriya ke fuskantar sauye-sauye a farashin man wanda kuma ke taɓa sauran sassan rayuwa.
Sai dai kuma, gwamnatin tarayya ta musanta bai wa kamfanin umarnin ƙara farashin litar mai ɗin.


Asalin hoton, Fabrizio
Dan wasan gaban Napoli Victor Osimhen ya koma ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya a matsayin aro.
Dan wasan mai shekara 25 an ta yaɗa cewa zai koma ƙungiyar Chelsea da ke buga Premier Ingila.
Kazalika an riƙa alaƙanta shi da Al-Ahli ta Saudiyya har zuwa ranar Juma'a ranar ƙarshe ta rufe kasuwar musayar 'yan wasa a Turai.
Sai dai har aka rufe kasuwar duka bai tafi ko wacce ƙungiya ba daga cikinsu.
Dan wasan Najeriyan ya ci kwallo 76 a wasa 133 da ya buga wa Napoli, kuma ya taka muhimmiyar rawa a Nasarar da ta samu ta lashe Serie A a 2022-23, inda ya ci kwallo 26.

Asalin hoton, X
Sai dai a bara ya gaza kai wa inda ake tsammani a matsayin ɗaya daga cikin 'yan wasa mafi ƙoƙari a Turai, inda ya ci kwallo 15 kacal.
Antonio Conte wanda shi ne kocin Napoli na yanzu, ya ɗauki dan wasan gaban Belgium da Chelsea, Romelu Lukaku mai shekara 31 kan kuɗin fan miliyan 30.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
An samu rashin jituwa tsakanin Victor Osimhen da kungiyarsa ta Napoli, abin da ya kai ga cire sunansa daga cikin tawagar 'yan wasan da za su buga musu kakar Serie A ta bana.

Asalin hoton, PRESIDENCY
Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata zargin da ake na rashin jituwar da ke tsakanin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, inda ta bayyana cewa dangantakar shugabannin biyu na nan da ƙarfinta.
Babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa ga mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a bikin cika shekaru 58 na mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima.
Nkwocha ya bayyana zargin a matsayin "makirci mara tushe waɗanda ba su nuna gaskiyar lamari a Aso Rock".
Ci gaban labarin - https://www.bbc.com/hausa/articles/c0mn2d7d792o