Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 27/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 27/11/2025

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Faransa na buƙatar ƙarin sojojin sa-kai - Macron

    Shugaba Emmanuel Macron ya ce Faransa na shirin samar da karin sojojin sa-kai domin cike wani muhimmin gibi a fannin tsaro.

    Mista Macron ya bayyana shirin samar da sojoji har dubu goma a kowace shekara, wadanda za a horas na tsawon watanni goma, kuma kasar na muradin cimma adadin dakarun soji dubu hamsin nan da shekarar 2035.

    Wakilin BBC ya ce a yanzu ana bukatar matasa maza da mata ne a aikin sojin saka-kan da su su taimakawa kwararrun dakarun Faransa wajen kare ta daga duk wata barazanar tsaro.

    Shugaban Faransar ya ce sojojin za su gudanar da aikin samar da tsaro ne kawai a cikin kasar. Kuma matakin na alaka da abin da Faransa ta kira sabuwar barazanar da Rasha ke yi wa kasashen Turai.

  2. Ƴansanda na binciken satar karnuka huɗu a fadar shugaban Malawi

    Ƴansanda a Malawi na gudanar da bincike kan yadda karnukan ƴansanda huɗu suka ɓace daga fadar shugaban ƙasa a Lilongwe babban birnin ƙasar a lokacin da ake gudanar da sauye-sauyen siyasa a watan Satumba.

    An kama Godfrey Arthur Jalale, wanda ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin ƙasar a zamanin tsohon shugaban ƙasar Lazarus Chakwera, bisa zarginsa da satar karnukan jinsin 'German Shephard' guda huɗu.

    Chakwera ya bar fadar ne bayan da ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa Peter Mutharika.

    Da yammacin ranar Laraba, ƴansanda sun musanta rahotannin da ke cewa an kama Chakwera, amma sun tabbatar da samun sammacin bincikar gidansa bayan bayanan da suka nuna cewa ana ajiye karnukan da aka sace a wurin.

    Chakwera, wanda ya zo na biyu da kashi 33% na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen na watan Satumba, na fuskantar zarge-zarge da dama na karkatar da dukiyar al’umma, musamman a lokacin miƙa mulki.

  3. Rasha ta ɗaure mutum takwas bisa laifin dasa bam

    Kafar watsa labaran Rasha ta ce wata kotu ta yankewa wasu mutum takwas ɗaurin rai da rai bayan samun su da laifin dasa bam a gadar yankin Krasnodar da ta haɗa Rasha da Crimea.

    Harin da aka kai a bara ya yi sandiyyar mutuwar mutum biyar tare da lalata gadar wadda sojojin Rasha ke amfani da ita wajen kai hari Ukraine.

    Daga baya hukumar leƙen asiri ta Ukraine ta ɗauki alhakin kai harin.

    Lauyan mutanen takwas ya ce zai ɗaukaka kara akan hukuncin da aka zartas musu.

  4. Majalisar Tarayyar Turai za ta dakatar da tallafin da EU ke bai wa Tanzania

    Majalisar Tarayyar Turai ta amince da wani kuduri da ke kira ga Hukumar Tarayyar Turai da ta dakatar da tallafin kuɗi kai tsaye ga gwamnatin Tanzania, inda ta yi nuni da kisan gillar da aka yi bayan zaɓe da kuma take haƙƙin ɗan adam.

    A wani kuduri daban da ba lallai ne ya yi wani tasiri ba, Ƴan Majalisar sun bukaci Hukumar da ta janye daftarin shawarar da ta yanke don ba da kuɗi ga wani shirin samar da ci gaban kasa na shekara-shekara na EU na 2025 ga Tanzania.

    Ƴan Majalisar sun yi Allah wadai da abin da suka bayyana a matsayin amfani da ƙarfi kan masu zanga-zanga bayan zaɓen shugaban kasar na watan Oktoban da ya gabata, tashin hankalin da aka ruwaito ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaruruwa da kuma jikkatar wasu da dama.

    An ayyana Shugaba Suluhu a matsayin wadda ta lashe zaɓen da kashi 98% na ƙuri'un da aka kaɗa, wanda hakan ya sa 'yan adawa suka ƙi amincewa da shi, tare da bayyana shi a a matsayinwani "izgili ga dimokuraɗiyya."

    Yanzu dai, Majalisar Tarayyar Turai ta yi kira ga hukumomin Tanzania da fara gudanar da tattaunawar siyasa da 'yan adawa, da ƙungiyoyin fararen hula da wakilan waɗanda abin ya shafa don ƙoƙarin warware rikicin da kuma shirya wani zaben da za a yi adalci.

    Ƴan Majalisar sun ƙara yin Allah wadai da "tsare shugaban 'yan adawa Tundu Lissu da aka yi bisa dalilai na siyasa" inda ake tuhumarsa da laifin cin amanar ƙasa, laifin da idan aka same shi da shi, zai iya fuskantar hukuncin kisa.

    Ƴan majalisar sun kuma matsa lamba kan a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma ba tare da nuna son kai ba kan zargin kashe-kashen da ake yi, bacewar da aka tilasta wa mutane, azabtarwa da sauran cin zarafi.

    Jam'iyyun adawa da Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan adam sun yi zargin cewa jami'an tsaro sun kashe ɗaruruwan masu zanga-zanga kuma sun kwashe gawawwakin mutane zuwa wurare da ba a bayyana ba.

  5. Sheikh Ɗahiru Bauchi dattijo ne mai son zaman lafiya - Kwankwanso

    Tshon ɗan takarar shugaban Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana jimaminsa tare a miƙa ta'aziyya ga iyalai da ƴanuwan da makusantan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi bisa rasuwar malamin.

    Kwankwaso ya bayyana malamin a matsayin uba, kuma babban malami wanda koyarsa ta zama madubi ga ɗimbin al'umma.

    "Ta hanyar karantarwa, Sheikh Ɗahiru taɓa rayuwar al'umma da dama tare da jan hankalinsu wajen koyi da halaye masu kyau da kuma ƙaunar Alqur'ani da sunnar manzon Allah."

    Kwankwaso ya ce shehin mutum ne mai son zaman lafiya kuma dattijo mai ƙoƙarin haɗa kan ƴan ƙasa, "wanda kuma ba za mu manta da shi ba, kuma ƙasarmu ba za ta manta da shi."

    "A madadin iyalina da ni kaina, ina miƙa ta'aziya da iyalansa da ɗalibansa da gwamnati da al'ummar Bauchi bisa wannan rasuwa. Allah ya saka shi a aljanna."

  6. Mun janye ƴansanda 11,500 daga gadin manyan mutane - IG Egbetokun

    Sufeto Janar na 'Yansandan Najeriya Olukayode Egbetokun ya ce sun aiwatar da umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na janye dakarunsu daga gadin ɗaiɗaikun mutane da ake kira VIP.

    Yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, IG Egbetokun ya ce zuwa yanzu sun janye dakaru 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Najeriya.

    "Wannan karon za muj aiwatar da umarnin da kyau saboda umarnin shugaban ƙasa ne," in ji shi.

    "Babu wani gwamna, ko minista, ko abokaina da za su kira su takura min saboda sun san cewa umarnin shugaban ƙasa ne. Ina da tabbacin ba za su uzura wa kwamashinonin 'yansanda ba ma."

    Ya ƙara da cewa za su tura jami'an da aka janye zuwa "wuraren da aka fi buƙatarsu, musamman a wannan lokaci mai muhimmanci".

  7. Fafaroma Leo ya ce makomar bil'adama na cikin haɗari

    Paparoma Leo na 14 ya yi gargaɗin cewa bai kamata duniya ta shiga cikin "matsayin tashin hankali irin wanda ake fuskata yanzu ba", a ziyararsa ta farko zuwa ƙasashen ƙetare a Turkiyya.

    "Makomar bil'adama tana cikin haɗari," in ji Paparoma, yana mai kira ga shugaba Recep Tayyip Erdogan da ya mai yunƙurin tabbatar da zaman lafiya a kodayaushe.

    Paparoma zai yi bikin zagayowar ranar tunawa da kiristoci ziyarar da ya ke kai wa Turkiyya, kafin ya wuce zuwa Labanon ƴan kwanaki kaɗan bayan hare-haren da Isra'ila ta kai a Beirut babban birnin ƙasar.

    Marigayi Fafaroma Francis ne ya shirya ziyarar, amma Paparoma ya karɓin ragamar yunƙurin inganta zumunci tsakanin ƙasashe da al'ummomi tun lokacin da ya hau barandar St Peter's Basilica bayan zaɓensa a watan Mayu.

    A Turkiyya fafaroma zai ziyarci Masallacin Blue Mosque, kamar yadda waɗanda ya gada fafaroma Francis da Fafaroma Benedict na 16 suka yi.

  8. Makamashi mai ɗorewa zai inganta tattalin arzikinmu da samar da aikin yi - Dikko Radda

    Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya ƙaddamar da shirin makamashi mai ɗorewa na Safe Space Energy, wanda a ƙarƙashinsa yake sa ran zamanantar da ɓangaren sufufi ta hanyar komawa amfani da motoci masu amfani da gas da lantarki da sauransu.

    Gwamna ya yaba wa jagororin kamfanin bisa zaɓar jihar Katsina, inda ya yaba musu, sannan ya yi alƙawarin ba su dukkan gudunmuwar da suke buƙata domin samun nasara, kamar yadda sakataren watsa labaran jihar, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar.

    Gwamnan ya ce wannan dama ce ga jihar domin inganta tattalin arzikinta na cikinta, sannan ta samar da ayyukan yi ga ɗimbin matasanta, sannan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta samar da sababbin motocin safa, waɗanda a cikinsu akwai masu amfani da lantarki, sannan ya ce jami'an gwamnati sun kusa komawa amfani da irin motocin.

    Ya ƙara da cewa shirye-shiryen kamfanin na Safe Space Energy sun yi daidai da tsare-tsaren gwamnatinsa, inda ya ce kamfanin zai taimaka masa wajen samun nasara.

    A nasa jawabin, mai ba gwamnan shawara kan tattalin arziki, Khalil Nura Khalil ya ce babu tattalin arzikin da zai inganta ya yi armashi ba tare da isasshen makamashi ba.

    Shugaban kamfanin Safe Space Energy, Nazir Abdulahi Alhassa ya ce sun zaɓi Katsina ne saboda tarihinta na tarbar baƙi da kuma sauƙin kasuwancinta, sannan ya ce za su buɗe tashar gas ta CNG da tashar cajin motoci masu amfani da lantarki da tashar sauya KENE Naped zuwa mai amfani da gas maimakon fetur.

  9. Rasuwar Sheikh Ɗahiru Bauchi rashi ne ga Musulmi - Atiku

    Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana rasuwar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi a matsayin rashi babba ga al'ummar Musulmi na Najeriya da ma Afirka baki ɗaya.

    A wata sanarwa da Atiku ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya bayyana marigayin da babban malami wanda ya koyar da addini da tarbiya.

    "Sheikh malami ne wanda rasuwarsa ta haskaka al'umma, sannan ya sadaukar da rayuwarsa ne wajen tabbatar da haɗin kai da son juna, kuma ya bar baya mai kyau. Najeriya ta yi rashin uba sannan Afirka ta yi rashin babban malami," in ji jigon na jam'iyyar ADC.

    Atiku ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga iyalai da ɗalibai da mabiya ɗarikar Tijjaniya a faɗin duniya, "waɗanda koyarsa ya taɓa wa rayuwa. Allah Ya sa ya huta, ya yafe masa kura-kuransa, ya karɓa masa ayyukansa na alheri, sannan ya saka shi a Aljanna maɗaukakiya."

  10. Rasuwar Sheikh Ɗahiru Bauchi ta bar giɓi babba - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, lamarin da ya ce ya kaɗu matuƙa da ya samu labarin.

    Tinubu ya ce jagoran na ɗarikar Tijjaniya mutum ne mai daraja da ƙima, sannan ya bayyana shi a matsayin madubi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa.

    Shugaban ya ce rasuwar shehin malamin rashi ne ga ƙasar baki ɗaya, ba ga iyalansa da ɗalibansa ko mabiyansa kaɗai ba, inda ya ƙara da cewa har yanzu yana tuna irin ƙarfafa gwiwar da marigayin ya ba shi a lokacin da ake shirin zaɓen 2023.

    "Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba ne kuma murya babba da ke amo sosai," in ji shi shugaban, sannan ya bayyana shi da hadimin Qur'ani kuma malamin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyar da zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa za ta ba babban giɓi a Najeriya," in ji shugaban.

    Tinubu ya yi ta'aziya ga mabiya shehin a faɗin Najeriya da ma ƙasashen waje, sannan ya yi kira gare su da su yi koyi da halayensa na gari.

  11. Ƴansanda na neman masu ƙunshin harsasai da ya faɗo daga wata mota a titin Zaria

    Rundunar ƴansanda jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta ƙaddamar da farautar waɗanda ake zargi da mallakar wani ƙunshin harsasai 210 da ya faɗo daga wata mota da ke tafiya a kan titin Zaria zuwa Funtua a ranar Talata.

    A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga ƙunshin abu a kan titi da harsasai a tarwatse, inda mutanen da ke kusa da wurin suka tattara su wuri ɗaya tare da sanar da jami'an tsaron da ke yankin Samaru.

    Kakakin rundunar ta Kaduna, Mansur Hassan, ya ce ana kan neman mutanen da ake zargi, kuma suna hasashen mutanen sun jefar da ƙunshin harsasan ne saboda fargabar jam'ian da ke kan titin sakamakon rundunar ta tsaurara tsaro a hanyar.

    Ya kuma ce zuwa yanzu ba su gano motar ba saboda bayanai ba su isa wurinsu ba a kan lokaci.

  12. Najeriya ta yi Allah-wadai da juyin mulkin Guinea-Bissau

    Gwamnatin Najeriya ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da aka yi a Guinea-Bissau, inda ta buƙaci a dawo da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar.

    A cikin wata sanarwa da ma'aikatar kula da harkokin ƙasashen waje na ƙasar ta fitar a yau alhamis, Najeriya ta ce ta damu matuƙa game da lamarin, inda ta bayyana ƙwace mulkin a matsayin 'abin takaici'

    ''Juyin mulkin na bayyana karya dokokin ECOWAS na mulkin dimokuraɗiyya da gwamnati mai adalci, waɗanda suka haramta hawa mulki ta hanyar da ba na tsarin mulki ba.'' inji sanarwar.

    Ma'aikatar harkokin wajen ta kuma ce Najeriya na tare da ƴan ƙasar Guinea Bissau, kuma ta na kiran dawo wa mulkin dimokradiyyar, da dawo da dukkanin waɗanda ake riƙe da su.

  13. An rantsar da shugaban riƙo a Guinea Bissau

    Sojojin da suka ƙwace mulki a Guinea-Bissau sun rantsar da wani Janar a matsayin sabon shugaban riƙo na tsawon shekara ɗaya.

    Janar Horta N’Tam ya sha rantsuwa ne yau alhamis a hedikwatar sojojin da ke babban birnin ƙasar Bissau.

    Hakan na zuwa ne bayan da suka hamɓarar da shugaban ƙasar Umaro Sissoco Embalo a jiya Laraba.

    Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka ECOWAS ta yi Allawadai da ƙwace mulkin da aka yi, inda ta yi kiran a gaggauta sakin hamɓararren shugaban ƙasar.

  14. Karantarwar Shiekh Dahiru Bauchi ta taɓa rayukan miliyoyin mutane - Gwamnonin Arewa

    Gwamnonin arewacin Najeriya sun nuna alhinin su bisa rasuwar jagoran ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya Shiekh Dahiru Usman Bauchi wanda ya rasu a yau alhamis.

    Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ta gwamnonin jihohin arewa, ya bayyana Shehin a matsayin malamin da rayuwarsa da koyarwarsa suka taɓa rayukan miliyoyin mutane a tsawon shekaru.

    A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin jihar Gombe Uba Misili ya fitar, Gwamnan ya ce Sheikh Dahiru Bauchi ya sadaukar da rayuwarsa ta tsawon shekara 100 wajen yaɗa ilimin addinin musulunci, inda ya taimaka wajen koyar da karatun al Qurani da Hadisi da fiqihu da sauran karatuka.

    Shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriyar ya kuma ce malamin ya taka muhimiyyar rawa wajen samar da zaman lafiya,da juriya, da haɗin kai da kuma tarbiyya a tsawon rayuwarsa.

    Ya kuma miƙa ta'aziyyar ɗaukacin gwamnonin arewacin Najeriya ga iyalan marigayin, da mabiya ɗariƙar Tijjaniyyah, da ma alummar musulmi kan gagarumin rashin da aka yi.

  15. Ramaphosa ya soki Trump kan ƙin gayyatar ƙasarsa taron G20 na 2026

    Shugaban Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa ya soki kalaman Trump na cewa ba zai gayyace shi taron ƙasashe 20 masu ƙarfin tattalin arziƙi na G20 na shekara mai zuwa a Florida.

    Ramaphosa ya ce abin takaici ne yadda Trump ke ci gaba da ɗaukar matakai bisa labaran da ba na gaskiya ba ko kuma aka yi musu kwaskwarima.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba zai gayyaci Afirka ta kudu taron na baɗi ba, kuma ya nanata sukar da yake yi wa Afirka ta kudun kan zargin cewa an aikata kisan kiyashi a Afirka ta Kudu a kan tsirarun fararen fata.

    Amurka ta ƙauracewa taron na G20 na bana a Johannesburg, inda shugabanni suka amince da matakan da aka ayyana na magance matsalar dumamar yanayi da sauran matsaloli na duniya, duk da ƙin yardar Amurka.

  16. Masu sa ido kan zaɓen Guinea Bissau sun yi Allah-wadai da juyin mulkin sojoji a ƙasar

    Shugabannin tawagar masu sa ido kan zaɓen Guinea Bissau na ƙungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS, sun bayyana '' matuƙar damuwa game da sanarwar da sojoji suka yi na yin juyin mulki a ƙasar."

    A wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, shugabannin sun ce gabanin sanarwar, ƙasar na cikin shirin sauraron sakamakon zaɓen da aka yi, wanda suka bayyana a matsayin wanda ya gudana lami lafiya.

    ''Abin takaici ne yadda aka samu wannan sanarwar jim kaɗan bayan tawagar mu ta kammala ganawa da manyan ƴan takarar zaɓen shugaban ƙasar waɗanda suka tabbatar mana da cewa za su amince da zaɓin alumma,'' in ji su.

    Sun kuma yi Allawadai da kama manyan jami'an gwamnatin ƙasar, ciki har da hukumomin zaɓe, inda suka buƙaci a gaggauta sakin su.

    A gefe guda kuma, sakataren Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres wanda ke bibiyar lamarin, ya buƙaci waɗanda ke da hannu a lamarin '' su yi haƙuri su kuma girmama doka ''

  17. Gwamnan Bauchi ya miƙa ta'aziyyar rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi

    Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya bayyana marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin mutumin da ya damu da harkokin addinin musulunci, mai son zaman lafiya, da samar da fahimta da juriya tsakanin musulmai da mabiya sauran addinai.

    A wani saƙon ta'aziyya mai ɗauke da sa hannun mai bai wa gwamnan shawara kan yaɗa labarai, Muktar Gidado, gwamnan ya bayyana matuƙar baƙin ciki da alhinin rashin sannanen malamin addinin musuluncin.

    Ya kuma ce ''Malamin babban abin kwatance ne a fannin koyar da addini, mutum ne me tsantsar imani, da basira da tawali'u. Sheikh Dahiru Bauchi ya sadaukar da rayuwarsa wajen ɗabbaƙa addinin musulunci, da koyar da alQur'ani da kuma gina alumma''.

    Gwamnan Bauchin ya ce jihar za ta ci gaba da martaba tarihin jagoran ɗarikar Tijjaniyyan ta hanyar yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da wanzuwar irin koyarwar sa da abin da ya yi imani da shi.

  18. Hamas ta nemi Isra'ila ta bari mayaƙanta da ke maƙale a Kudancin Gaza su wuce lafiya

    Hamas ta buƙaci masu shiga tsakani su matsawa Isra'ila lamba kan ta bari gomman mayaƙan ta da ke maƙale a hanyar ƙarƙashin ƙasa a Kudancin Gaza su fito su wuce lafiya, inda ta ce hakan na da tasiri kan makomar yarjejeniyar da aka yi.

    A cikin wata sanarwa, ƙungiyar ta ce ta gabatar da wasu ''shawarwari da hanyoyi'' na shawo kan lamarin, sai dai ta zargi Isra'ila da ƙin amincewa.

    Kafafen yaɗa labaran Isra'ila sun ce Isra'ila ta ce ba za ta kashe mayaƙan ba muddin suka miƙa wuya.

    Sojojin Isra'ila sun ce a baya bayan nan sun kashe gomman mayaƙan Hamas tare da tsare wasu da ke fitowa daga ƙarƙashin ƙasar.

  19. Tinubu ya tura wa majalisar dattawa sunayen jakadu 3

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar dattawan ƙasar sunayen mutum uku domin tantancewa da amincewa a matsayin jakadu.

    Tinubu ya aike da sunayen Ayodele Oke da Kanal Lateef Are mai ritaya da kuma Amin Dalhatu domin amincewa su zama jakadun ƙasashen Amurka da Birtaniya da kuma Faransa.

    Shugaban majalisar Dattawan ƙasar Godswill Akpabio, wanda ya karanto sunayen a zaman majalisa na jiya Laraba, ya umurci kwamitin kula da harkokin waje na majalisar ya tantance sunayen ya kuma kawo rahotonshi cikin mako ɗaya.

    A ƴan kwanankin baya bayan nan, an yi ta kira ga shugaban Najeriyar ya naɗa jakadun ƙasar, bayan shafe kusan shekaru biyu ƙasar ba ta da jakadu.

    Masana sun sha tsokaci kan yadda rashin jakadun ke mayar da ƙasar baya ta fuskar hulɗarta da ƙasashen waje, da kuma yadda hakan ke shafar ƴan ƙasar da ke zaune a ƙasashen waje.

    Gwamnatin a baya dai ta danganta lamarin da rashin isassun kuɗi.

  20. Gobarar Hong Kong ta hallaka mutum 55

    A Hong Kong, ma'aikatan kashe gobara na can suna ta faman aiki a wajen da wata babbar gobara ta tashi a tsakanin benaye masu tsawon gaske tun a jiya Laraba, inda wutar ta hallaka mutum 55.

    An kwantar da gommai a asibiti, da kuma wasu kusan 300 da ba a san inda suke ba.

    Yansanda sun kama mutum uku na wani kamfanin gine-gine bisa zargin kisan jama'a ba da niyya ba, saboda wasu abubuwa masu saurin kamawa da wuta da suka bari a inda suke aiki.