Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni 17-23, 2025

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan labarain wasanni a faɗin duniya daga ranar Asabar 17 zuwa 23 ga watan Mayun 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Tarihin da Modric ya kafa a Real Madrid

    Kyaftin ɗin Real Madrid Luka Modric zai bar ƙungiyar bayan Gasar Cin Kofin Duniya ta Ƙungiya da za a buga ta kakar bana.

    Ɗanwasan ɗa Croatia mai shekara mai shekara 39 zai buga wasansa na ƙarshe a matsayin ɗanwasan ƙungiyar a wasansu da Real Sociedad a ranar Asabar a wasan ƙungiyar na ƙarshe na La liga ta bana.

    "Lokaci ya yi. Lokacin da ban so ya zo ba, amma haka lamarin yake a rayuwa saboda komai yana da farko yana ƙarshe," in ji Modric a shafinsa na Instagram.

    "Na je Real Madrid a shekarar 2012 ne domin wakiltar ƙungiya mafi girma a duniya da kuma burin lashe kofuna. Buga wa Real Madrid ya canja min rayuwa a matsayin ɗanƙwallo da ma rayuwata baki ɗaya. Ina farin ciki da alfaharin kasancewa cikin ƴanwasan da suka rubuta tarihi a ƙungiyar nan."

    Modric zai bar ƙungiyar ce a matsayin wanda ya fi taka wasa, inda ya buga wasa 590, ya zura ƙwallo 43, sannan ya taimaka aka zura 95.

    "Modric zai kasance a cikin zukatan ƴan Madrid bar abada," in ji shugaban ƙungiyar, Florentino Perez a sanarwar da ya fitar.

    Modric ya jagoranci Madrid lashe kofuna biyu a matsayin kyaftin, inda yanzu ya lashe kofuna 28, wanda ya sa ya haura Nacho a matsayin ɗanwasan ƙungiyar da ya fi lashe kofuna.

    Ya lashe zakarun turai shida, kofin duniya na ƙungiyoyi shida da gasar european super cup biyar da La liga huɗu da Copa del Rey biyu da Spanish super cup biyar a shekara 13 da ya yi a ƙungiyar.

    Shi ne ɗanwasa mafi tsufa da ya buga wa Madrid wasa a La liga, kuma mafi tsufa da zura ƙwallo, inda ya zura ƙwallo a wasansu da Valencia a shekara 39 da kwana 116, inda ya haura Ferenc Puskas.

  2. Ƙungiyoyin Ingila da suka fi lashe kofin Turai

    Tottenham ta zama ta huɗu a cikin jerin ƙungiyoyin Ingila da suka lashe kofuna a gasar ƙungiyoyin nahiyar Turai.

    Yanzu Spurs na da kofuna huɗu da suka ci daga nahiyar Turai.

    Sun fara cin kofi a gasar Turai ne da kofin 'Winners Cup' a 1963, wanda yanzu aka daina buga shi.

    Daga nan sai suka ci kofin Uefa Cup, wato Europa a yanzu, sau uku.

    Sai dai suna da sauran aiki a gaba kafin su kamo Liverpool, wadda ita ce ta ɗaya da kofuna 13.

    Liverpool ta fara lashe kofin Turai ne a 1973 inda ta fara da Uefa Cup, sai kuma na baya-bayan nan da ta lashe shi ne kofin zakarun Turai na Champions League a shekara ta 2019, lokacin da ta yi nasara kan Tottenham a wasan ƙarshe.

    Ga jerin ƙungiyoyin Ingila da kofunan Turai da suka lashe:

    • Liverpool - 13
    • Chelsea - 8
    • Manchester United - 6
    • Tottenham Hotspur - 4
    • Nottingham Forest, Manchester City - 3
    • Arsenal, Aston Villa, West Ham - 2
    • Newcastle United, Ipswich Town, Everton - 1

    Ba a haɗa da kofin 'Fairs Cup', da 'Inter-Cities Fairs Cup' da kuma 'Intertoto Cup' ba.

  3. Tawagar Tottenham ta koma gida bayan lashe gasar Europa

  4. Barcelona na sha'awar Rashford da Diaz - Deco

    Daraktan wasanni na Barcelona Deco ya ce kulob ɗin na son ɗan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford da kuma Luis Diaz na Liverpool.

    Rahotanni daga ƙasar Sifaniya a wannan makon sun danganta Diaz ɗan ƙasar Colombia da komawa ƙungiyar ta Catalania, yayin da Rashford ya kusa komawa ƙungiyar ta La Liga a watan Janairu kafin ya koma Aston Villa a matsayin aro.

    Duk da cewa babu alamun Liverpool za ta saurari tayi kan Diaz, wanda ya rage shekaru biyu a kwantiraginsa, Rashford zai iya barin Man U idan aka miƙa tayin da ya kai fam miliyan 40 a kansa.

    Barcelona ta ƙulla yarjejeniyar tsawaita kwantiragin kocinta Hansi Flick bayan nasarar lashe gasar La Liga a makon da ya gabata.

    Deco ya ce abin da ƙungiyar ta sa gaba kafin neman siyan sabon ɗan wasan gefe shi ne tswaita kwantiragin ƴan wasan da ta ke da su ƙasa, irin su Lamine Yamal da Pedri da kuma Gavi.

  5. Na fi ƙarfin buga minti 20 na ƙarshen wasa - Garnacho

    Ɗan wasan gefe na Manchester United Alejandro Garnacho ya sanya alamar tambaya kan makomarsa a ƙungiyar inda ya nuna rashin amincewa da matakin da Ruben Amorim ya yanke na ajiye shi a banci a wasan ƙarshe na gasar Europa league.

    Garnacho, mai shekaru 20, ya kasance a benci ne sakamakon fara wasan da aka yi da Mason Mount kuma ya maye gurbin ɗan wasan tsakiya na Ingila ne da saura minti 19 a tashi.

    Ɗan wasan na Argentina, wanda aka alaƙanta shi da komawa Chelsea ko Napoli a watan Janairu, ya soki matakin da Amorim ya ɗauka na ba shi taƙaitaccen lokaci a wasan ƙarshen.

    "Har zuwa wasan ƙarshen na buga kowane zagaye, kuma na taimaka wa ƙungiyar, kuma a yau sai in buga minti 20? abin ya ɗaure mun kai," in ji Garnacho.

    Ba Garnacho ne kaɗai ɗan wasan United da ya sanya alamar tambaya kan makomarsa ba, inda shi ma kyaftin Bruno Fernandes ya nuna cewa zai iya barin Old Trafford idan kulob ɗin ya zaɓi ya sallame shi.

    Ana dai alaƙanta ɗan wasan mai shekaru 30 da komawa ƙungiyar Al-Hilal ta ƙasar Saudiyya.

  6. Barcelona ta tsawaita yarjejeniyar Flick zuwa 2027

    Barcelona ta tsawaita ƙwantiragin Hansi Flick zuwa karshen kakar 2027.

    Ƙungiyar ta yi haka ne, domin sakawa kociyan, sakamakon lashe kofin Sifaniya uku da ya yi a kakarsa ta farko a ƙungiyar.

    Kociyan, wanda ya saka hannu a bara kan yarjejeniyar kaka biyu a Barcelona, na fatan dawo da martabarsa, sakamakon da Bayern Munich ta kore shi a Satumbar 2023.

    Barcelona ta koma kan ganiya tun bayan da ta ɗauki Flick kan fara kakar nan, wanda ya lashe kofi uku ciki har da na La Liga na 28 jimilla, kuma saura wasa biyu a kare kakar a lokacin.

    Haka kuma a kakar nan Barcelona ta lashe Spanish Super Cup da Copa del Rey, kuma Real Madrid ya ci a dukkan kofunan.

    Barcelona ta doke Real Madrid a dukkan wasa huɗun da suka fuskanci juna a bana da cin ƙwallaye 16.

    Flick ya ci wasa 43 daga 54 da ya ja ragama, shi ne kociyan da ya taka rawar gani a kakarsa ta farko tun bayan Luis Enrique a tarihi.

    Haka kuma kociyan ya kai Barcelona zagayen daf da karshe a Champions League, inda Inter Milan ta fitar da su da cin ƙwallo 7-6 gida da waje.

  7. Endrick ba zai buga wa Real Madrid Club World Cup ba, Real Madrid

    Ɗan ƙwallon Real Madrid, Endrick ya ji rauni a wasan da suka doke Sevilla 2-0 a La Liga, kamar yadda ƙungiyar ta sanar ranar Laraba.

    Real Madrid ba ta fayyace ranar da zai warke ya koma taka leda ba, sai dai wasu rahotanni daga Sifaniya na cewar matashin zai yi jinyar wata biyu, kenan ba zai yi gasar Club World Cup ba.

    Real ɗin ta ce Endrick ba zai buga wa Brazil wasan neman shiga gasar kofin duniya da Ecuador da kuma Paraguay ba.

    Endrick ya shiga jerin masu jinya a Real Madrid da ya haɗa da Vinicius Junior da Lucas Vazquez da Dani Carvajal da Eder Militao da Eduardo Camavinga da Antonio Rudiger da Ferland Mendy da kuma David Alaba.

    Real za ta buga wasan karshe a La Liga ranar Asabar da Real Sociedad a Santiago Bernabeu daga nan ta fuskanci Al-Hilal a Club World Cup da za a fara cikin watan Yuni a Amurka.

  8. Birnin Landan zai karɓi bakuncin Laver Cup a 2026., Ƙwallon tennis

    Ana buga Laver Cup duk kaka uku tsakanin tawagar nahiyar Turai da ta sauran duniya, wadda aka sa mata sunan tsohon ɗan wasan Australia, Rod Laver.

    An buga gasar a 2022 lokacin da Roger Federer ya yi ritaya, inda Rafael Nadal da Novak Djokovic da Andy Murray suka buga wasan a London O2 Arena.

    Za a fafata a gasar 2026 tsakanin ranar 25-27 ga watan Satumba.

  9. Djokovic ya ɗauki Vemic a matakin kociyansa, Ƙwallon tennis

    Novak Djokovic ya naɗa tsohon abokinsa, wanda suka yi ƙwallon tennis ta ƴan wasa bibiyu, Dusan Vemic a matakin sabon kociyansa.

    Ɗan kasar Serbia, wanda ya raba gari da Andy Murry na fatan taka rawar gani a gasar ƙwallon tennis ta Geneva Open da kuma French Open.

  10. Wannan ce kakar da na fi samun nasara - Casemiro

    Ɗan wasan Manchester United, Casemiro ya ce wannan ce kakar da ya fi samun nasara a tarihinsa na taka leda a duniya.

    Casemiro ya lashe kofi 18, daga ciki har da Champions League biyar a kaka tara a Real Madrid.

    Sai dai mai shekara 33 ya ɗauki FA Cup da League Cup, tun bayan da ya koma United kan £70m a 2022.

    United tana mataki na 16 a kasan teburin Premier League, kuma saura wasa ɗaya a kammala kakar nan, yana kuma sa ran zai lashe Europa League ranar Laraba a karawa da Tottenham a birnin Bilbao a Sifaniya.

    Duk da United ba ta taka rawar gani a Premier League ba a kakar nan, Casemiro ya ce yana alhari da kansa, yadda ya sa ƙwazon da ya koma buga wa United wasanni.

    Ɗan wasan Brazil, ya koma zaman benci sakamakon kuskuren da ya yi karkashin Erik ten Hag da ta kai an ci United ƙwallo biyu a wasan da Liverpool ta ci 3-0 a cikin Satumba.

    Bayan da Ruben Amorim ya karɓi aikin horar da United a cikin watan Nuwamba ya ajiye Casemira a benci a wasa tara daga 13 da ya ja ragama.

  11. An tuhumi West Ham da Nottingham Forest da halin rashin ɗaya, Premier League

    An tuhumi West Ham da Nottingham Forest da kasa tsawatarwa ƴan wasansu, bayan hatsaniyar da ta ɓarke a tsakaninsu a Premier League ranar Lahadi.

    An yi taho mu gama tsakanin mai tsaron baya, Murillo da Edson Alvarez a cikin karin lokaci a daf da tashi daga wasan da Forest ta yi nasara da cin 2-1 a Landan stadiya.

    Hakan ya sa aka yi ture-ture tsakanin ƴan wasan Forest Murillo da Felipe Morata da na West Ham, Alvarez da kuma Carlos Soler, waɗan da aka bai wa dukkaninsu katin gargaɗi.

    An bai wa ƙungiyoyin nan da ranar Juma'a, domin su kare kansu, kafin hukumar ƙwallon kafa ta Ingila ta yanke hukunci.

  12. Ba za a bai wa Ingila da Scotland da Wales da Ireland ta Arewa tikitin Euro 2028 kai tsaye ba, Euro 2028

    Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa ta sanar cewar ba za ta bai wa Ingila da Scotland da Wales da Ireland ta Arewa tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai, wato Euro 2028 kai tsaye ba.

    Uefa ta sanar bayan tashi daga babban taro da manyan jami'anta suka gudanar a birnin Bilbao ranar Laraba cewar, kasashen za su shiga cikin wasannin neman gurbin shiga gasar.

    Za a samar da rukuni 12 ɗauke da kasa huɗu ko biyar, domin fayyace 24 da za su kece raini a Euro 2028.

    Kenan za a ɗauki duk wadda ta yi ta ɗaya a kowanne rukuni, sannan za a zaɓo waɗan da suka yi na biyu a rukuni da maki mai yawa.

    Za kuma a tanadi gurbi biyu ga kasar da za ta ɗauki nauyin gasar, waɗan da suka kasa kai bante a wasannin cikin rukuni.

  13. Watakila Del Piero zai horar da Juventus nan gaba, Juventus

    Magoya bayan Juventus sai murna suke bayan da suka ji tsohon ɗan wasa, Alessandro Del Piero ya sanar da cewar ya mallaki lasisin horar da tamaula daga hukumar ƙwallon kafar Turai.

    Del Piero, wanda ya yi kaka 19 a Juventus da lashe kofin Serie A shida da Champions League, ya kammala karatun koyon horar da tamaula a Coverciano a birnin Florence.

    Mai shekara 50, ya yi ritaya da buga wa Juventus tamaula a 2012.

    Lokacin da Del Piero ya bar Juventus, ƙungiyar ta yi niyyar rataye riga mai lamba 10, sai dai ɗan wasan bai amince da hakan ba, wanda ya ce zai so matasa su yi mafarkin saka riga.

    Rabon da Juventus ta lashe Serie A tun bayan da ta ɗauki na tara a jere a 2020, wadda a bana ta kori Thiago Motta ta maye gurbinsa da Igor Tudor.

  14. Everton za ta zaƙulo waɗan da suka ci zarafin matar Calvert-Lewin, Everton

    Everton ta sanar cewar tana aiki tare da ƴansandan Merseyside da jami'an Premier League, domin zaƙulo, waɗan da suka ci zarafin matar Dominic Calvert-Lewin a kafar sada zumunta.

    Matar Calvert-Lewin da ake kira Sandra ta ya bi mijinta, wanda yake na uku a jerin waɗan da ke kan gaba a cin ƙwallaye a Everton, wanda ya ci ƙwallo 30, kenan yana biye da Duncan Ferguson da Romelu Lukaku.

    Daga baya ta saka saƙonnin da aka rubuta mata na cin zarafin a kafar sada zumunta, sakamakon don ta yabi ƙwazon mijinta.

    Ɗan wasan na jinya tun bayan raunin da ya ji a watan Janairu, kuma ƙwallo uku kacal ya ci a kakar nan.

  15. Timber da Saliba ba za su buga wa Arsenal wasan karshe ba a Premier, Arsenal

    Ƴan wasan Arsenal, Jurrien Timber da kuma William Saliba ba za su buga wasan karshe a Premier League ba a Southampton.

    Tuni an yi wa Timber tiyata, shi kuwa Saliba ya ji rauni ne a wasan Premier da Arsenal ta ci Newcasle United 1-0 ranar Lahadi a karawar mako na 37.

    Arsenal za ta kare a mataki na biyu a teburin Premier da zarar ta doke Southampton ranar Lahadi a St Mary.

    Idan kuma ta kasa cin Southampton, lalle kuwa Manchester City za ta ɗare mataki na biyu da zarar ta yi nasara a kan Fulham.

    Liverpool ce ta lashe kofin Premier na bana na 20 jimilla, tuni kuma Arsenal ta samu gurbin shiga Champions League na baɗi.

  16. Za a sabunta filin wasan da ake buga US Open, Ƙwallon tennis

    Hukumar kwallon tennis ta Amurka ta sanar cewar ta tanadi miliyan 800, domin inganta filin da ake buga gasar US Open.

    Wurin da zai ci kudi a aikin har da filin Arthur AsheR da katafaran wajen atisaye da za a gina dauke da na'urorin zamani na gani na fada da za a sa masa sunan Billie Jean King, zakakuren tsohon ɗan wasan kwallon tennis.

    Za a kammala gyare-gyaren a 2027, inda za a gudanar da aikin kashi uku, domin kada ya shafi gasar tennis da za yi a bana.

  17. Watakila Gerrard ya sake karɓar aikin kociyan Rangers, Rangers

    Wata jita jita da take ta karakaina na cewa watakila Steven Gerrard ya sake karɓar aikin horar da Rangers daga kakar da za a fara ta baɗi.

    Kenan tsohon ɗan wasan Liverpool yana sawun gaba daga cikin wanda zai maye gurbin Philippe Clement, sakamakon da wanda ke aikin rikon ƙwarya, Barry Ferguson ya yi murabus ranar Lahadi.

    Gerrard ya bar Glasgow cikin watan Nuwambar 2021 zuwa Aston Villa mai buga Premier League, bayan kaka uku a Rangers.

    Kofi ɗaya ya ci a ƙungiyar, kuma ba a doke Rangers ba a lik a lokacin da hana Celtic lashe babban kofin kasar karo na 10 a jere.

    Wasu da ake alakantawa da aikin horar da Rangers har da mataimakin kociyan Real Madrid, Davide Ancelotti da kuma Rusell Martin tsohon mai tsaron bayan ƙungiyar.

  18. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikin ƴan wasa, Daga jaridu

    Bayer Leverkusen ta yi wa ɗan wasan tsakiya na Jamus Florian Wirtz, 22, darajar fam miliyan 126, daidai lokacin da ƙungiyoyin Bayern Munich da Liverpool ke zawarcinsa bayan janyewar da Manchester City ta yi daga son ɗaukar dan wasan. (The Times - subscription required)

    An gano Manchester United,da Barcelona da ƙungiyoyin Pro League na Saudiyya na bibiyar lamarin Martinez. (The Sun)

    Aston Villa na son golan Ireland mai taka leda a Liverpool, Caoimhin Kelleher, 26, da ɗan wasan Argentina, Emiliano Martinez, 32, za su bar Villa a karshen kakar nan. (The Sun)

  19. Raducanu na yin abin kirki a Strasbourg Open, Ƙwallon tennis

    Emma Raducanu ta ci gaba da yin abin kirki a wasan kan tabo ta kuma doke Daria Kasatkina a zagayen farko a Intnational Sitrasbourg

    Yar Burtaniya, wadda ta kai kwata fainal a Italian Open a bana ta yi nasarar cin 6-1 6-3.

    Raducanu na fatan yin abin kiki a shirin da take na taka rawar gani a French Open da za a fara daga 25 ga watan nan na Mayu.