Tarihin da Modric ya kafa a Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Kyaftin ɗin Real Madrid Luka Modric zai bar ƙungiyar bayan Gasar Cin Kofin Duniya ta Ƙungiya da za a buga ta kakar bana.
Ɗanwasan ɗa Croatia mai shekara mai shekara 39 zai buga wasansa na ƙarshe a matsayin ɗanwasan ƙungiyar a wasansu da Real Sociedad a ranar Asabar a wasan ƙungiyar na ƙarshe na La liga ta bana.
"Lokaci ya yi. Lokacin da ban so ya zo ba, amma haka lamarin yake a rayuwa saboda komai yana da farko yana ƙarshe," in ji Modric a shafinsa na Instagram.
"Na je Real Madrid a shekarar 2012 ne domin wakiltar ƙungiya mafi girma a duniya da kuma burin lashe kofuna. Buga wa Real Madrid ya canja min rayuwa a matsayin ɗanƙwallo da ma rayuwata baki ɗaya. Ina farin ciki da alfaharin kasancewa cikin ƴanwasan da suka rubuta tarihi a ƙungiyar nan."
Modric zai bar ƙungiyar ce a matsayin wanda ya fi taka wasa, inda ya buga wasa 590, ya zura ƙwallo 43, sannan ya taimaka aka zura 95.
"Modric zai kasance a cikin zukatan ƴan Madrid bar abada," in ji shugaban ƙungiyar, Florentino Perez a sanarwar da ya fitar.
Modric ya jagoranci Madrid lashe kofuna biyu a matsayin kyaftin, inda yanzu ya lashe kofuna 28, wanda ya sa ya haura Nacho a matsayin ɗanwasan ƙungiyar da ya fi lashe kofuna.
Ya lashe zakarun turai shida, kofin duniya na ƙungiyoyi shida da gasar european super cup biyar da La liga huɗu da Copa del Rey biyu da Spanish super cup biyar a shekara 13 da ya yi a ƙungiyar.
Shi ne ɗanwasa mafi tsufa da ya buga wa Madrid wasa a La liga, kuma mafi tsufa da zura ƙwallo, inda ya zura ƙwallo a wasansu da Valencia a shekara 39 da kwana 116, inda ya haura Ferenc Puskas.



















