Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna Electric da ke da alhakin samar da lantarki ga jihohin Kaduna da Kebbi da Sokoto da Zamfara ya ce an gaza cimma matsaya tsakanin shugabanninsa da kungiyar ma'aikatan kamfanin duk da sanya bakin gwamnati da masu ruwa da tsaki.
Babban Jami'in sadarwar kamfanin, Abdulazeez Abdullahi a cikin wata sanarwar da ya fitar, ya ce duk da ƙoƙarin samun matsaya tsakaninsu, ma'aikatan sun ƙi amincewa su maido da wutar lantarki bayan katse ta tun ranar Litinin 3 ga watan Fabrairu.
Ya ce an gudanar da taruka tare da hukumomin tsaro da Gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagoranci gwamnan jihar Uba Sani wanda mataimakiyarsa Hadiza Balarabe ta wakilta, inda ta bayyana yadda rashin wutar ke shafar fannin lafiya da kasuwanci ta kuma buƙace su da su mayar da wutar a lokaci ba tare da ɓata lokaci ba a lokacin tattaunawar.
A cewar sanarwar, an kuma yi zaman shiga tsakanin tare da babban lauyan Najeriya Sani Katu da kuma kwamishinan shari'ah na jihar Kaduna Sule Shuaibu SAN, sai dai haƙar ta gaza cimma ruwa sakamakon sabbin buƙatu da ƙungiyar ma'aikatan ta gabatar.
Abdulazeez ya kuma ce: ''Wannan mataki da suka ɗauka ya saɓa wa tabbacin da suka bai wa gwamnatin jihar Kaduna tun da farko na cewa za su mayar da wutar lantarkin a yayin da ake cigaba da tattaunawa.''
A farkon makon nan ne dai Kamfanin rarraba wutar lantarkin na Kaduna Electric ya ce ya sallami ma'aikata fiye da ɗari huɗu, wanda hakan ya kai ga shiga yajin aikin ma'aikatan tare da jefa alummomin jihohi huɗu cikin duhu.
Lamarin ya jefa al'umma cikin ƙunci da haifar da asara ga masu sana'o'i.