Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na yau Juma'a 7 ga watan Fabrairun 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna da Abdullahi Bello Diginza da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Sallama

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin na BBC Hausa, da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan za mu rufe shafin na yau Juma'a 7 ga watan Fabarairun 2025.

    Da fatan za ku sake kasancewa da mu a gobe, Asabar 8 ga watan na Fabarairu, 2025, idan Allah Ya kai mu.

    Kafin sannan za ku iya ci gaba da leƙawa shafukanmu na sada zumunta da muhawara domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo, har ma ku yi muhawara.

    Mu rufe da wannan karin maganar da ke cewa - Mai haƙuri yakan dafa dutse har ya sha romansa

  2. An bai wa ango ɗan talakawa kariyar 'yansanda 150, don kilisa a India

    Mutane kewaye da ango a kan doki

    Asalin hoton, THE HINDU

    Kusan 'yansanda 150 ne suka bayar da kariya ga wani ango ɗan talakawa lokacin da yayi kilisa a bikin aurensa a yammacin India.

    Mukesh Parecha, wanda lauya ne daga garin Gujarat, ya nemi kariyar 'yansanda saboda wata ta'ada da mutanen garin ke nuna wa ƙabilarsa ta Dalit, ta haramta msu hawa doki saboda an ɗauki ƙabilar tasa a wasu sassan India, ƙasƙantattu, talakawa, kuma 'yan bora da su cancanci wasu abubuwa na more rayuwa ba.

    Ana ɗaukar hawan doki a matsayin wani abu na alfarma da sai masu hali ne za su yi - banda baya-a-dangi

    A wasu wuraren ana kai wa matasan Dalit hari saboda sun hau doki, to amma matasa da dama na ci gaba da bijirewa tsohuwar al'adar ta ɗaruruwan shekaru ta nuna wariya da fifiko a India.

    Akwai 'yan wannan ƙabila Dalit da ake ɗauka baya-a-dangi kuma ƙasƙantattu, tare da nuna musu wariya, har miliyan 200 a India.

    Mista Parecha ne na farko da ya yi wannan kilisa ta hawan doki daga wannan gari a ƙauyensa.

    Haka kuma 'yansandan sun sa ɗan ƙaramin jirgin sama maras matuƙi da ke ɗauke da kyamara yana shawagi a lokacin bikin.

  3. Rasha ta ce dakarunta sun kama gari mai matuƙar muhimmanci a Ukraine

    Wata mata na tafiya a garin Toretsk kusa da gidajen da yaƙi ya lalata

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar tsaro ta Rasha ta ce dakarunta sun kama garin Toretsk na gabashin Ukraine wanda kusan an lalata yawancinsa.

    Garin wanda ake haƙar kwal a cikinsa a yankin Donetsk ya kasane wanda hare-haren Rasha suka fi mayar da hankali a kansa tsawon watanni.

    Sai dai ba wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da iƙirarin na Rasha na kama garin.

    Wasu kafofi ciki har da mai nuna bayanai game da yakin na Ukraine sun nuna cewa har yanzu sojojin Ukraine ne ke iko da wasu sassan birnin na Toretsk.

    A irin bayanan da Ukraine ke bayarwa kan yaƙin a baya-bayan nan ta ce ana kai hare-hare a yankin amma kuma ba tare da ta ayyana matsayin garin ba.

    Idan har Rasha ta kama garin na Toretsk hakan zai ba dakarunta damar nausawa arewa masu yammacin Ukraine wajen garin Kostyantynivka mai masana'antu.

  4. Shugabannin duniya na Alla-wadarai da Trump kan kotun duniya

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatocin ƙasashe a faɗin duniya na yin Alla-wadarai da matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauka na sanya wa ma'aikatan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC.

    Wata sanarwa da kusan shugabannin ƙasashe tamanin suka sanya wa hannu ta ce matakin zai ƙara haɗarin aikata manyan laifuka ba tare da hukunci ba.

    Ministar waje ta Jamus Annalena Baerbock, ta ce a sanadin aikin kotun ta duniya - shugaban Rasha Vladimir Putin ba zai iya tafiye-tafiye ba gaba-gaɗi saboda tsoron kada a kama shi a kan laifukan cin zarafin bil'Adama a Ukraine.

    Mista Trump ya soki kotun ta duniya saboda bayar da izinin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu bisa zargin aikata laifukan yaƙi a Gaza.

  5. Mexico ta karɓi baƙin haure kusan 11,000 daga Amurka

    Baƙin haure 'yan Mexico

    Asalin hoton, Reuters

    Shugabar Mexico Claudia Sheinbaum ta ce ƙasarta ta karɓi kusan baƙin haure 11,000 da aka kora daga Amurka, tun bayan da Donald Trump ya hau mulki.

    Ta ce daga cikin baƙin sama da 2,539 ba 'yan Mexico ba ne in ji shugabar, sannan wasu daga cikinsu an kai su Honduras bisa raɗin kansu.

    A farkon makon nan, Ms Sheinbaum ta cimma yarjejeniya da Trump kan ya dakatar da barazanar da ya yi ta ƙara haraji a kan kayan Mexico da ake shigarwa Amurka.

    A nata ɓangaren ta ce za ta saka hakan ta hanyar zuba dubban 'yansanda a iyakar ƙasar da Amurka, wadda ke ɓangaren Arewa don ƙara rage kwararar 'yancirani Amurka.

  6. Hamas ta saki sunayen Isra'ilawa da za ta saki bayan an shiga fargaba

    (Daga hagu zuwa dama): Or Levy, da Ohad Ben Ami da Eli Sharabi

    Asalin hoton, The Hostages and Missing Families Forum

    Hamas ta saki sunayen maza uku 'yan Isra'ila da za ta saki gobe Asabar, daga cikin mutanen da ta yi garkuwa da su.

    Ƙungiyar ta ce tana sa ran Isra'ila ta saki Falasɗinawa 183 fursunoni na musayar da za a yi.

    Wannan shi ne karo na biyar da za a yi musayar fursunonin tun bayan da aka cimma yarjejeniyar dakatar da bɗe wuta mako uku da ya gabata.

    Waɗanda Hamas ɗin za ta saki a wannan karon su ne Or Levy, da Ohad Ben Ami da Eli Sharabi.

    An samu jinkirin sa'o'i da dama kafin Hamas ta saki sunayen waɗanda za ta sakin ta intanet bayan wa'adin fitar da sunayen ya yi kamar yadda yarjejeniya ta tanada.

    Wannan jinkirin ya sa aka fara fargaba cewa ko an samu matsala a shirin.

    Tun da farko kakakin Hamas, Abdul Latif al-Qanou, ya zargi Isra'ila da jinkirin aiwatar da sharaɗin bayar da damar shigar da kayan agaji Gaza, kamar yadda yarjejeniya ta tanada.

  7. Iyayen da ƴaƴansu suka mutu wajen yin bidiyon TikTok sun kai ƙara kotu

    Manhajar TikTok

    Asalin hoton, AFP

    Iyayen matasa huɗu ƴan Birtaniya da suka ce ƴaƴansu sun mutu bayan yin wani bidiyon TikTok sun shigar da manhajar ƙara a wata Kotun Amurka.

    Ƙarar wadda aka shiga a jihar Delaware na zargin shafin sada zumuntar na TikTok da tunzura yara yin bidiyoyi masu hatsari na kwaikwayon wasu domin bunƙasa lokacin da yara ke kwashewa suna amfani da shafin.

    Iyalan na kuma buƙatar damar shiga shafin ƴaƴansu a manhajar domin samun amsoshi kan mutuwar yaran a shekarar 2022.

    Manhajar TikTok ta ce ba ta barin bidiyo da ke nuna ko kuma tallata abubuwa masu hatsari kuma tana sauke kusan duk waɗanda aka wallafa.

  8. Yin sulhu da Amurka ba komai ba ne face ganganci - Ayatollah Khamenei

    Ayatollah Ali Khamenei

    Asalin hoton, AFP

    Jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya yi kira ga gwamnatin ƙasar kada ta ''kuskura'' ta yi tattaunawar sulhu da Amurka, yana mai cewa yin hakan ganganci ne.

    A taron da ya yi da shugabbanin sojin ƙasar, Ayatollah ya ce gwamnatin Trump mai ruguzawa tare da saɓa wa yarjejeniyoyin da aka ƙulla ne.

    Ya yi gargadin cewa magana da gwamnatin irin wannan ba alheri ba ne inda ya ce idan suka yi musu barazana toh za su mayar da martani.

    ''Idan kuma suka ce mana kule, to za mu ce musu cas'', in ji jagoran addinin.

    A farkon makon nan ne shugaba Trump ya nemi a samar da ingantaciyyar yarjejeniyar makamin nukliya da Iran wadda a ƙarƙashinta za a hana ta ƙera makaman nukliya

  9. Wani jirgi ɗauke da mutum 10 ya ɓace a Amurka

    Jirgin sama

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'ai a Amurka sun bazama neman wani ƙaramin jirgi ɗauke da mutum 10 da ya ɓace a jihar Alaska.

    Masu kula da gaɓar teku a yankin Alaska sun ce jirjin samfurin Cessna Caravan ya yi nisan kilomita 19 daga Unalakleet zuwa Nome a lokacin da ' ya ɓace'.

    Cikin wata sanarwa da hukumomin jihar suka fitar, sun ce ma'aikatan ceto na cigaba da ƙoƙarin gano wurin da yake.

    A cewar sashen kula da alumma na Alaska, mutum 10 ne ke cikin jirgin, da suka haɗa da fasinjoji 9 da matuƙin jirgi ɗaya, sai dai har yanzu babu cikakkun bayanai kai mutanen.

    Alaska yanki ne mai cike da tsaunuka da kuma yanayi maras kyau, kuma yankin na samun haɗarin jirgin sama fiye da wasu jihohi a Amurka.

  10. NAFDAC ta buƙaci a riƙa yanke wa masu jabun magunguna hukuncin kisa

    Shugabar hukumar NAFDAC

    Asalin hoton, NAFDAC

    Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC ta nemi hukuncin kisa ga masu haɗawa da shigar da jabun magunguna.

    A cewar shugabar hukumar Mojisola Adeyeye, tsauraran matakai ne kawai za su hana aikata hakan musamman idan lamarin na kai wa ga mutuwar yara.

    ''Wani ya sayi magani naira 13,000 a wani kanti, wani kuma ya sayi irin wannan maganin a wani shagon kan naira 3,000, hakan ya ankarar da mu, kun san mene ne? da muka gwada maganin a ɗakin gwaje-gwajenmu da ke Kaduna, babu wani sinadarin magani mai amfani a cikin shi, a don haka ina son a fara aiwatar da hukuncin kisa,'' in ji ta a wani hira da gidan talibijin na Channels.

    Ko a jiya ma majalisar wakilai ta buƙaci babban mai shari’a na tarayya da ya gabatar da tsauraran takunkumai da suka hada da ɗaurin rai da rai ga masu haɗawa da masu shigo da magungunan jabu cikin ƙasar.

    Bayan muhawara kan ƙudurin wanda ya samu goyon bayan ƴan majalisar, majalisar ta buƙaci babban lauyan gwamnatin tarayya da ya gabatar da gyara ga dokokin da ake da su da nufin zartar da hukunci mai tsauri.

  11. Wani ƙaramin jirgi ya faɗa kan hanyar mota a Brazil

    ...

    Asalin hoton, Michael Krogh

    Wani ƙaramin jirgi ya faɗa kan wata motar safa a birnin São Paulo da ke ƙasar Brazil.

    Rahotannin farko-farko na nuna cewa aƙalla mutane biyu sun mutu.

    Motar ta kama da wuta inda hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniyar birnin.

  12. An gaza cimma matsaya kan yajin aikin ma'aikatan lantarki a Kaduna

    Gwamnan jihar Kaduna

    Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna Electric da ke da alhakin samar da lantarki ga jihohin Kaduna da Kebbi da Sokoto da Zamfara ya ce an gaza cimma matsaya tsakanin shugabanninsa da kungiyar ma'aikatan kamfanin duk da sanya bakin gwamnati da masu ruwa da tsaki.

    Babban Jami'in sadarwar kamfanin, Abdulazeez Abdullahi a cikin wata sanarwar da ya fitar, ya ce duk da ƙoƙarin samun matsaya tsakaninsu, ma'aikatan sun ƙi amincewa su maido da wutar lantarki bayan katse ta tun ranar Litinin 3 ga watan Fabrairu.

    Ya ce an gudanar da taruka tare da hukumomin tsaro da Gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagoranci gwamnan jihar Uba Sani wanda mataimakiyarsa Hadiza Balarabe ta wakilta, inda ta bayyana yadda rashin wutar ke shafar fannin lafiya da kasuwanci ta kuma buƙace su da su mayar da wutar a lokaci ba tare da ɓata lokaci ba a lokacin tattaunawar.

    A cewar sanarwar, an kuma yi zaman shiga tsakanin tare da babban lauyan Najeriya Sani Katu da kuma kwamishinan shari'ah na jihar Kaduna Sule Shuaibu SAN, sai dai haƙar ta gaza cimma ruwa sakamakon sabbin buƙatu da ƙungiyar ma'aikatan ta gabatar.

    Abdulazeez ya kuma ce: ''Wannan mataki da suka ɗauka ya saɓa wa tabbacin da suka bai wa gwamnatin jihar Kaduna tun da farko na cewa za su mayar da wutar lantarkin a yayin da ake cigaba da tattaunawa.''

    A farkon makon nan ne dai Kamfanin rarraba wutar lantarkin na Kaduna Electric ya ce ya sallami ma'aikata fiye da ɗari huɗu, wanda hakan ya kai ga shiga yajin aikin ma'aikatan tare da jefa alummomin jihohi huɗu cikin duhu.

    Lamarin ya jefa al'umma cikin ƙunci da haifar da asara ga masu sana'o'i.

  13. An ci tarar wani mutum sama da naira 300,000 saboda saka waya a sifika

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani mutum - da aka ci tararsa euro 200, wato sama da naira 300,000 saboda saka waya a sifika lokacin da yake waya a wata tashar jirgin ƙasa da ke Faransa - ya ƙalubanaci tarar.

    Mutumin mai suna David, ya shaida wa kafar talibijin ta Faransa mai suna BFM cewa yana waya ne da ƴar'uwarsa a tashar Nantes ranar Lahadi a lokacin da wani jami'i daga kamfanin jirgin ƙasan, SNCF, ya tunkaro shi.

    David ya ce jam'in ya ce za a ci tarar sa euro 150 idan bai kashe sifikar ba - tarar da yayi iƙirarin daga bisani an ƙara ta zuwa euro 200 saboda bai biya kuɗin nan take ba.

    Tuni dai ya ɗauko lauya domin ƙalubalantar tarar.

    Kamfanin SNCF ya tabbatar da cewa jami'in tsaronsu ne ya ci tarar David a wani wuri da babu hayaniya.

  14. Ƴanbindiga sun kashe mutum guda tare da sace kuɗaɗe a wani hari a Kebbi

    mahara

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi da ga jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutum guda tare da raunata wasu bayan da wasu ƴanbindiga suka kai hari garin Gulma da ke yankin aramar hukumar Argungu a jihar.

    Shugaban ƙaramar hukumar Hon Aliyu Sani Gulma, ya shaida wa BBC cewa maharan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe takwas na maraicen ranar Alhamis ɗaue da muggan makamai.

    ''Ƴanbindigar sun shiga garin ne a kan babura bakwai ɗauke da goyon bibbiyu, ciki har da mata biyu, ɗauke da muggan makamai, inda suka je wani babban kantin sayar da kayyaki na Alh Fatawu a garin, suka kuma buƙaci a ba su kuɗaɗe''.

    Shugaban ƙaramar hukumar ya ce mata biyu daga cikin ƴanbindigar sun tsaya a ƙofar kantin, riƙe da bindigogi, yayin da sauran mazan suka shiga cikin domin ƙwato kuɗaɗe.

    ''Sun faɗa masu kantin cewa kuɗin Saifa suke ce ba naira ba, sa dai kuma a kantin babu saifar sosai, lamarin da ya sa suka riƙa bugun masu kula da kantin, inda daga baya suka kwashe duka kuɗaɗen da ke cikin kantin suka yi awon gaba da su'', a cewar shuagaban ƙaramar hukumar.

    Ya ce maharan sun kuma kashe mutum guda a cikin al'ummar gari tare da raunata wasu a dama a lokacin da suka shiga garin.

  15. An gano gawarwakin ƴan cirani fiye da 30 a Libya

    ƴan cirani a tekun kusa da Libya

    Asalin hoton, AFP

    An gano gawar aƙalla ƴan cirani 29 a wurare daban-daban a ƙasar Libya.

    Hukumomi sun ce 19 daga cikinsu, an gano su ne a wani katon kabari a wata gona da ke yammacin garin Jikharra, sun kuma ce mutuwarsu na da alaƙa da masu safarar mutane.

    A wani yankin na daban kuma ƙungiyar agaji ta Red Crescent a Libyar ta gano gawarwakin ƴan cirani 10, bayan kwale-kwalen da suke ciki ya nutse a kusa da birnin Zawiya da ke kusa Tripoli, babban birnin ƙasar.

    Dubban ƴan cirani ne ke mutuwa duk shekara a ƙoƙarin amfani da Libya a matsayin hanyar tsallaka tekun Bahar rum domin tsallakawa ƙasashen Turai.

  16. Majalisar Dattawan Najeriya za ta binciki zarge-zargen Tchiani kan Najeriya

    Godswin Akpabio

    Asalin hoton, Njerian Senate/X

    Majalisar dattawan Najeriya ta ba da umurnin binciken zarge zargen da shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya yi na cewa gwamnatin Najeriya na haɗa kai da Faransa wajen kawo cikas ga tsaron ƙasarsa.

    Umurnin na zuwa ne bayan wani ƙuduri da shugaban kwamitin tsaro na majaliar, Sanata Shehu Buba ya gabatar, inda ya jaddada cewa babban abin damuwa shi ne yadda Tchiani ya zargi mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da tsohon shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasa, Ahmed Rufai, da hannu dumu-dumu wajen yi wa ƙasarsa bita-da-ƙulli.

    Cikin zarge-zagen nasa, Tchiani ya ce gwamnatin Najeriya na taimaka wa ƙungiyar ƴan ta'adda ta Lakurawa da ke arewa maso yammacin ƙasar, wajen kafa sansanoni a Sokoto da Zamfara da kuma Kebbi, sannan suna amfani da wasu sansanonin sojoji a Najeriya domin kai hari kan bututun man Nijar da kuma kawo barazanar tsaro a ƙasarsa.

    A martaninsa a zaman majalisar, mataimakin shugaban majalisar, sanata Barau Jibrin wanda ya jagoranci zaman ya amince da matsayar da ta buƙaci kwamiti kan tsaron ƙasar da kwaminitin harkokin ƙasashen waje su gudanar da bincike su kuma gabatar da rahoton nan da makonni huɗu.

  17. Netanyahu ya gode wa Trump kan sanya wa kotun ICC takunkumi

    Firaministan Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gode wa Donald Trump kan matakin da ya auka na sanya wa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC takunkumi.

    Mista Netanyahu ya ce dokar shugaban ƙasar da Trump ya sanya wa hannu za ta kare ƙasashensu daga abin da ya kira kotu mai ƙin jinin Amurka da ƙin jinin yahudawa.

    Mista Trump ya kalubalanci Kotun ICC kan sammacin da ta bayar na kama Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa, Yoav Gallant.

    Kotun ta yi zargin cewa su biyun sun aikata laifukan yaƙi da kuma laifukan cin zarafin ɗan'adam a Gaza.

    Ƙungiyoyin fararen hula a Gabas ta Tsakiya sun yi ƙorafin cewa ƙoƙarin Amurka na hana ayyukan ICC zai raunana oarin tabbatar da adalci a duniya

  18. 'Sai ka shekara 15 kafin zama ɗan Birtaniya, ko da ka shiga bisa ƙa'ida' - Kemi Badenoch

    Ms Kemi Badenoch

    Jam'iyyar Conservative mai hamayya a Birtaniya ta ce ba za ta bar ƴancirani da suka shigar ƙasar da bizar aiki su samu takardun zama a Birtaniya na dindindin ba, har sai sun shekara 15.

    Wannan shi ne babbar manufa ta farko da shugabar jam'iyyar, Kemi Badenoch ta bayyana tun bayan da ta samu matsayin.

    Ms Kemi Badenoch ta kuma ce jam'iyyar tasu za ta tsawaita lokacin da ƴancirani za su ɗauka ƙasar kafin su nemi takardun izinin zama 'yan ƙasa a Birtaniya daga shekara biyar zuwa 10.

    A yanzu dai mutum zai iya neman izinin zama ɗan Birtaniya, wata 12 bayan ƙasar ta ba su takardar zama ƙasar ta ILR.

    To sai dai Ms Badenoch ta ce a ƙarƙashin shirin da jam'iyyarta ke da shi, ba za a bai wa ƴanciranin masu laifi izinin zama a ƙasar ba.

    Shugabar jam'iyyar ta ce mutumin da ya cancanci samun izinin zama dan Birtaniya, ''shi ne mutumin da ya nuna sha'awar inganta Birtaniya''.

  19. Sojojin Kenya 100 sun isa Haiti domin yaƙi da ƴandaba

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Sama da sojojin Kenya 100 ne suka isa ƙasar Haiti, domin karfafa jami'an tsaron Haiti da kuma aikin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, a yaƙin da suke yi da gungun ƴandaba da suka addabi ƙasar.

    Sai dai ana nuna damuwa kan yadda har yanzu dakarun suka gaza tabbatar da doka a babban birnin ƙasar, Porto Prince.

    An yi ta raɗe-raɗin ayyukan dakarun sun zo ƙarshe, amma kwamandan rundunar, Godfrey Otunge ya ce lamarin ba haka yake ba.

    Ya ce lokacin da yake magana da jakadun yana yi ne domin kawar da shakkun da ake yi na aikinsu, ya kuma shaida cewa ƙawancen na nan daram.

  20. MDD za ta yi zaman gaggawa kan yaƙin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo

    MDD

    Asalin hoton, reut

    A yau ne ake sa ran kwamitin kare haƙƙin dan adam na MDD zai yi zaman gaggawa kan yaƙin da ya rincabe a jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.

    Ƴan tawayen M23 da Rwanda ke mara wa baya dai sun karɓe iko da birnin GOMA.

    MDD ta yi ƙiyasin cewa sama da farar hula 2,900 ne aka kashe, yayin da rahotanni ke cewa faɗa na kara yaɗuwa zuwa wasu sassan ƙasar, sannan take hakkin ɗan'adam na ƙara munana.

    Jakadan Congo a Geneva ya ce gwamnatin ƙasar na buƙatar MDD ta gudanar da cikakken bincike kan hakan.

    Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun yi amannar cewa ƴan tawayen M23 da sojojin Rwanda da na Congo duk sun aikata munanan laifuka.

    Sai dai har yanzu Rwanda ba ta bayyana a hukumance cewa dakarunta na a cikin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congon ba.