Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya aike da wata tawaga mai ƙarfi zuwa Burkina Faso domin tattauna batun matuƙan jirgin saman sojojin Najeriya da ake riƙe da su a ƙasar, sakamakon saukar gaggawa da jirginsu ya yi a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ta gana da Shugaban Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, a Ouagadougou.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin watsa labarai na minitsan Alkasim Abdulkadir ya fitar a shafin sada zumunta ta X.
A yayin ganawar, Ambasada Tuggar ya miƙa saƙon gaisuwa da goyon baya daga Shugaba Tinubu ga Shugaba Traoré, tare da jaddada muhimmancin kyakkyawar alaƙa da makwabtaka tsakanin ƙasashen biyu.
Shugaban Burkina Faso ne ya tarbi tawagar tare da nuna godiya ga saƙon alheri daga Shugaban Najeriya.
Ɓangarorin biyu sun cimma matsaya cikin fahimta kan batun jami’an sojojin saman Najeriya da aka riƙe, inda aka amince da warware lamarin ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.
Tawagar ta kuma kai ziyara wajen ganin halin da jami’an ke ciki, inda aka tabbatar da cewa suna cikin ƙoshin lafiya da ƙwarin gwiwa.
Tattaunawar ta kuma taɓo batutuwan ƙarfafa alaƙar siyasa da tsaro da tattalin arziƙi, tare da jaddada buƙatar haɗin gwiwa wajen tinkarar matsalolin tsaro da ke addabar yankin Sahel da Yammacin Afirka baki ɗaya.
A nasa ɓangaren, Ambasada Tuggar ya sake jaddada ƙudurin Najeriya na kyakkyawar makwabtaka da ci gaba da hulɗa da Burkina Faso, yana mai cewa ƙasar na goyon bayan duk wani yunƙuri da zai tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki a yanki