Me ya sa wasu ke zuwa bahaya nan take bayan cin abinci?
Asalin hoton, Getty Images
Matsuwar jin bahaya mintoci kaɗan bayan kammala cin abinci, matsala ce da mutane da dama ke fuskanta a kowace rana.
Wannan ya aza ayar tambaya cewa ko abincin da muka ci ya narke yadda ya kamata?
A cewar ƙwararru kan lafiya, dalili guda ka wanna matsala shi ne cin abinci kaɗan ko kuma yawan abinci a wurin aiki da kuma cin abin da ka fi so lokaci da kake hutu.
Amma tambayar ita ce, shin babu matsala ne idan aka je bahaya da zarar an kammala cin abinci, ko kuma alamce ta ciwo? Ko matsala ce yin bahaya da yawa a rana?
A wannan labari, za ku samu amsoshin waɗannan tambayoyi tare da taimakon ƙwararrun lafiya da kuma bincike.
Majalisar Ƙoli ta Shari'ar Musulunci ta nuna takaici kan sauyi a dokar haraji
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Ƙoli ta Shari'ar Musulunci a Najeriya ta ce ta yi takaici dangane da zargin da ake ta yaɗawa cewa akwai banbanci tsakanin dokar haraji da ake son aiwatarwa a watan Janairun 2026 da wadda ƴan majalisar ƙasar suka amince.
A wata sanarwa da ta fitar, majalisar ta ce idan dai har hakan ya tabbata to babu abin da zai haifar illa janyo yanke ƙauna da raini daga al'ummar ƙasa.
Majalisar ta ƙara da cewa dalilin da ya sa al'amarin ya ba ta takaici shi ne sakamakon irin gudunmowar da ta bayar ga kundin na dokar harajin ƙasa.
Daga ƙarshe majalisar ta nemi ɓangarorin biyu na zartarwa da majalisar dokoki da su yi bincike domin gano yadda aka yi aka samu sauye-sauyen.
Yadda ƴanbindiga suka tafi da mai ciki ta haihu a hanya a Zamfara
Asalin hoton, Getty Images
Al'ummar garin Nahuce da ke jihar Zamfara na cikin alhini bayan wasu gungun ƴan bindiga sun sace mata sama da 20 da ƙananan yara da suke goyo da kuma wasu maza huɗu.
Wani abu da ya fi tayar wa al'ummar hankali shi ne yadda ɗaya daga cikin matan da aka sace ta haihu a hanyar tafiya da su daji, amma duk da haka maimakon ɓarayin su bari ta koma, ai suka tafi da ita.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tafka muhawara kan samun sauƙin matsalolin tsaro musamman a arewacin Najeriya, inda wasu ke ganin an samu sauƙi, wasu kuma suke ganin har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cikin jihohin da suke daɗe suna fama da matsalar garkuwa da mutane da fashin daji da kashe-kashe, lamarin da ya yi ajalin mutane da dama.
Sai dai hukumomi a ƙasar suna bayyana cewa an fara samun sauƙi, inda suke bayyana irin nasarorin da suka samu wajen yaƙi da rashin tsaro a arewaci da ma ƙasar baki ɗaya.
Na koma APC ne domin na nuna godiya ga Tinubu - Fubara
Asalin hoton, Fubara/Facebook
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya ce ya yanke shawarar sauya sheƙa daga PDP zuwa APC ne domin ya nuna godiyarsa ga shugaba Tinubu.
Fubara ya yi furucin ne a ranar Alhamis a hedikwatar APC da ke jAbuja, inda ya bayyana cewa ba siyasa ce ta saka shi sauya sheƙar ba zuwa APC illa dai kawai ya nuna godiyarsa ga shugaban.Tinubu dangane da rawar da ya taka a rikicin da ya turnuƙe jihar Rivers da yadda ya magance shi kai tsaye.
"Shigata jam'iyyar APC na da alaƙa da nuna godiya ga Tinubu da kuma haɗa hannu da gwamnonin jam'iyyar domin ciyar da Najeriya gaba. Ba shawara ce mai sauƙi ba. Amma kuma an aiwatar," in ji Fubara.
Kotu ta hana a yi belin Abubakar Malami
Asalin hoton, Malami/Facebook
Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi watsi da buƙatar neman beli da tsohon ministan Shari'ar Najeriya, Abubakar Malami ya yi domin sakin sa daga hannun hukumar EFCC.
Mai Shari'a Babangida Hassan ya ce bai zai iya amince wa da buƙatar belin ba saboda doka ta bai wa hukumar EFCC ta tsare tsohon ministan shari'ar domin ci gaba da bincike.
Tun dai ranar 8 ga watan Disamba Abubakar Malami ke tsare a wurin hukumar ta EFCC.
A ranar Laraba ne Malami ya kwarmata cewa jami'an hukumar sun kai samame ofishinsa da gidajensa da ke Abuja da Kebbi.
EFCC na riƙe da malami ne kan tuhumar laifuka guda uku waɗanda tsohon ministan ya musanta.
Amfani da muƙami ba bisa ƙa'ida.
Safarar haramtattun kuɗade.
Laifuka masu alaƙa da kadarorin tsohon shugaban ƙasa, Sani Abacha da aka karɓo daga ƙasashen waje da suka kai dala miliyan 346.
Fiye da mutum 1000 ne suka mutu a hare-haren RSF cikin kwana uku - MDD
Asalin hoton, Getty Images
Malalisar Dinkin Duniya ta ce fararen hula sama da 1000 ne aka kashe a cikin kwana uku na hare-haren dakarun RSF a watan Afrilu a sansanin yan gudun hijira na Zamzam da ke arewacin Darfur.
Babban jami'in hukumar kare hakkin dan'adam ta MDD, Volker Turk ya ce kisan fararen hular da gangan na iya zama laifukan yaƙi kuma dole a hukunta waɗanda ke aikata kisan.
MDD ta buƙaci gudanar da bincike kan yiyuwar aikata laifukan yaƙi.
Ana dai zargin dakarun RSF da kisan fararen hula a hare-haren da suke kai wa a yankin Darfur - wanda yanzu yake karkashin ikonsu.
China ta buƙaci Amurka ta daina bai wa Taiwan makamai
Asalin hoton, Getty Images
China ta buƙaci Amurka ta daina bai wa Taiwan makamai tare da mutunta tsarinta na dunƙulalliyar kasa daya.
Wannan na zuwa bayan Amurka ta amince da sayar wa Taiwan da makamai na dala biliyan 11.
Makaman sun ƙunshi makaman roka da jiragen yaƙi marar matuka da kuma makamai masu linzami.
China ta ce za ta ɗauki matakan da suka dace na kare iyakokinta.
Wannan ne karo na biyu da Amurka ta sayar wa da Taiwan da makamai tun hawan Donald Trump shugaban Amurka karo na biyu.
Har yanzu ba mu tabbatar da janyewar M23 daga Uvira ba - DR Congo
Asalin hoton, Getty Images
Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo ta ce har yanzu ba ta tabbatar da rahotannin da ke cewa dakarun M23 da ke samun goyon baya Rwanda ba na janyewa daga Uvira da ke gabashin kasar.
M23 ta ce ta fara janye mayaƙanta a ranar Laraba, kuma za ta kammala a yau Alhamis.
Amma mai magana da yawun gwamnatin Congo ya shaida wa BBC cewa suna ɗari-ɗari da iƙirarin yana mai cewa dakarun gwamnati ba su kai ga shiga Uvira ba wanda dakarun M23 suka ƙwace a makon da ya gabata.
Ya kuma yi gargaɗin cewa za a iya barin wasu mayaƙa su baɗda kamanni su saje da fararen hula.
Gwamnatin Congo ta yi kiran janyewar ɗaukacin dakarun na M23 a yankin da suka mamaye.
Tarayyar Turai na muhawara kan miƙa kuɗaɗen Rasha ga Ukraine
Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin Tarayyar Turai na tattaunawa a Brussels inda suke muhawra kan batun amfani da kuɗin Rasha da suka ƙwace domin ba Ukraine a matsayin rance.
Ƙasar Belgium inda galibi kuɗaɗen Rasha suka fi yawa na fuskantar matsin lamba ta jingine adawa da take yi da buƙatar.
Belgium na nuna fargaba ne kan martanin da zai biyo baya.
Shugabar hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta ce suna da manufa guda a wannan taro kuma ita ce zaman lafiya ga Ukraine, saboda Ukraine na buƙatar samun tallafi na shekara biyu.
Tuni babban bankin Rasha ya shigar da ƙara a Moscow domin ƙalubalantar bankin Belgium, tare da barazanar maka wasu bankunan kotu.
Amma Faransa da Portugal ne ke jagorantar da'awar miƙa kuɗaɗen na Rasha ga Ukraine
Taron na zuwa a yayin da Rasha ke ci gaba da kai hare-hare, yayin da kuma Amurka ke matsin lamba ga amincewa da yarjejeniyar da ta tsara ta kawo ƙarshen yaƙin na kusan shekara hudu.
An dakatar da babbar jam’iyyar adawa a Guinea kafin zaɓen shugaban ƙasar
Asalin hoton, Getty Images
An dakatar da babbar jam’iyyar adawa a Guinea ‘yan kwanaki ƙalilan gabanin zaben shugaban ƙasa da aka shirya gudanarwa a ranar 28 ga Disamba.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da aka hana fitattun ‘yan adawa tsayawa takara, lamarin da mutane da dama ke kallon sa a matsayin wani babban amfani ga shugaban ƙasar mai ci, Mamady Doumbouya, wanda ya karɓi mulki a shekarar 2021 da alkawarin mayar da ƙasar ga mulkin farar hula.
Jam’iyyar UFDG, wadda tsohon firaminista Cellou Dalein Diallo ke jagoranta kuma yake neman mafaka ta sake fuskantar dakatarwa bayan wadda aka yi a watan Oktoba da ta shafi wasu jam’iyyun siyasa.
An hana Diallo tsayawa takara ne bisa sabon kundin tsarin mulki da aka amince da shi a watan Satumba, wanda ya tanadi cewa duk mai neman kujerar shugaban ƙasa dole ne babban mazauninsa ya kasance a cikin ƙasar.
Hukumomin Guinea sun ce an dakatar da jam’iyyar ne sakamakon rashin cika sabbin tanade-tanaden doka gaba ɗaya.
Habasha da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar samar da makamashin nukiliya
Asalin hoton, Getty Images
Habasha ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da Rasha domin haɓɓaka samar da makamashin nukiliya kamar yadda gidan labarai ta gwamnatin ƙasar ENA tya ruwaito.
Wannan na zuwa ne bayan wata yarjejeniyar farko da aka cimma a watan Satumba tsakanin firaministan Habasha, Abiy Ahmed, da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin wacce ta gabatar da shirin aiwatar da gina tashar makamashin nukiliya a Habasha
Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Habasha, Sandokan Debebe, da daraktan janar na ayyukan makamashin nukiliya na Rasha, Andrey Rozhdestvin ne suka sanya hannu kan wannan yarjejeniyar a Moscow,
“Habasha da Rasha sun ɗauki mataki mai muhimmanci wajen gina tashar makamashin nukiliya ta farko a Habasha bayan sanya hannu kan Yarjejeniyar rashin bayyana abun ta aka tattauna a Moscow,” in ji ENA.
“Wannan yarjejeniyar wani ɓangare ne na tsarin hadin gwiwar ƙasa da ƙasa da nufin bunƙasa ci gaban makamashin nukiliya a Habasha, wanda ke nuna babban ci gaba na dogon lokaci a tsarin bunƙasa makamashi da masana’antu a kasar.”
Ƴanbindiga sun kashe mutum 12 a Plateau
Asalin hoton, Getty Images
Aƙalla mutum 12 ne suka rasa rayukansu yayin da aka sace wasu uku bayan ‘yan bindiga sun kai hari a wani wurin haƙar ma’adanai a Jihar Plateau da ke tsakiyar Najeriya.
Harin ya faru ne da daddare a garin Atoso da ke gundumar Fan ta ƙaramar hukumar Barkin Ladi a lokacin da mutanen ke haƙar ma’adanai bisa ƙa'ida.
Shugaban al’ummar, Solomon Daylop, ya shaida wa BBC cewa waɗanda suka kai harin sun isa wurin ne dayawansu inda suka fara harbi, lamarin da ya jawo firgici da mutuwar mutane da dama.
Ya ce tuni aka kai waɗanda suka jikkata asibiti, yayin da mazauna ke cikin baƙin ciki suna kuma shirin yadda za a kuɓuatar da waɗanda aka sace.
Hukumar ‘yan sanda ta jihar Plateau ba ta yi wani bayani ba tukuna kan lamarin.
Wannan sabon tashin hankali ya ƙara haifar da fargaba a yankin, inda aka sha fama da hare-hare masu alaƙa da harkokin haƙar ma’adanai da rikice-rikice na dogon lokaci tsakanin manoma da makiyaya.
Jihar Plateau ta kasance cibiyar rikici a ‘yan shekarun nan saboda saɓani kan fili da albarkatu da kuma ƙabilanci.
Ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun fi mayar da hankali kan wuraren haƙar ma’adanai don samun kuɗi da iko.
A watan Satumba, ma’aikatan ma’adanai huɗu sun mutu a garin Dura sakamakon ruftawar wani wuri haƙar ma’adanai, abin da ke nuna hatsarin wannan aiki da kuma rashin tsaro a yankin.
Gwamnati ta haramta fitar da itace zuwa ƙasashen waje
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta haramta fitar da itace da kayayyakin da suka shafi itace zuwa ƙasashen waje a faɗin ƙasar baki ɗaya, tare da soke dukkan lasisi da izini da aka bayar a baya kan irin wannan kasuwanci.
Sanarwar ta fito ne a ranar Laraba daga bakin ministan muhalli, Balarabe Lawal, yayin taron malalisar ƙasa kan kare muhalli karo na 18 da aka gudanar a Jihar Katsina.
Balarabe Lawal ya ce wannan umarni na cikin wata sabuwar dokar zartarwa ta shugaban ƙasa wadda aka ɗauka domin dakile sare itatuwa ba bisa ƙa’ida ba da kuma lalacewar gandun daji a sassan ƙasar.
Ministan ya jaddada cewa gandun dajin Najeriya na da matuƙar muhimmanci wajen ɗorewar muhalli, domin suna samar da iska da ruwa masu tsafta da tallafa wa hanyoyin samun abin rayuw da, kare nau’o’in halittu, da rage illar sauyin yanayi.
Ya kuma yi gargaɗi cewa ci gaba da fitar da itace zuwa ƙasashen waje na barazana ga waɗannan fa’idodi da kuma lafiyar muhalli a nan gaba.
Dokar wadda aka fitar ta dogara ne da sashe na 17(2) da 20 na ƙundin tsarin mulki na 1999 (da aka yi wa gyara), waɗanda ke bai wa gwamnati ikon kare muhalli da gandun daji da namun daji, tare da hana cin gajiyar albarkatun ƙasa don amfanin ƙashin kai.
Hare-haren jirage marasa matuƙa sun katse wutar lantarki a manyan biranen Sudan
Asalin hoton, Getty Images
An samu katsewar wutar lantarki a manyan biranen Sudan, Khartoum da Port Sudan, bayan hare-haren jiragen yaƙi marasa matuki sun lalata wani muhimmin tashar wuta.
Shaidu sun ce sun ga wuta da hayaki mai yawa ya turniƙe tashar wutar lantarki da ke Atbara, a jihar Nile ta Gabas, yankin da ke karkashin ikon sojojin gwamnatin ƙasar.
Rahotanni sun bayyana cewa hare-haren sun lalata na’urorin canza wuta a tashar wutar Al-Muqrin, wacce ke da matuƙar muhimmanci a tsarin rarraba lantarki na ƙasar.
Wani jami’i ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Faransa cewa mutum biyu sun mutu yayin da suke ƙoƙarin kashe gobarar da ta tashi bayan harin farko.
Sauran mutane kuma sun jikkata lokacin da aka kai hari na biyu kan cibiyar.
Tashar Al-Muqrin na karɓar wuta daga mafi girman tashar samar da lantarki ta ruwa a Sudan, kafin a rarraba ta zuwa sauran sassan ƙasar.
Saboda haka, lalacewar da aka samu ta haifar da katsewar wuta da ya shafi yankuna da dama, ciki har da manyan birane.
Ana dai zargin dakarun RSF da kai hare-haren a yankunan tare da kai farmaki kan muhimman kayayyakin more rayuwar jama’a.
Rikicin Sudan da ya shafe kusan shekaru uku yanzu, ya kashe dubban mutane tare da tilasta wa sama da mutum miliyan goma sha biyu barin muhallansu.
ADC ta buƙaci a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji
Asalin hoton, ADC/X
Jam’iyyar haɗakar ƴan adawa ta ADC ta nuna damuwa kan abin da ta kira gazawa iri-iri da ’yan Najeriya ke fuskanta a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ta buƙaci a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji nan take.
Jam’iyyar ta ce aiwatar da sabuwar dokar haraji zai ƙara tsananta matsin rayuwa ne kawai ga talakawa ba.
A cikin wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar, ta jaddada buƙatar tattaunawa a faɗin ƙasa da ƙungiyoyin ƙwadago da na fararen hula da ƙanana da matsakaitan ’yan kasuwa da ƙwararru, da kuma gwamnatocin jihohi.
Jam’iyyar ta ce "Dole ne a saurari ra’ayoyin waɗannan ɓangarori kafin ɗaukar duk wani mataki kan aiwatar da sabuwar dokar harajin."
"Jam’iyyar ta kuma buƙaci bayyanannun matakan kariya da za a ɗaure kai tsaye ga duk wani sabuwar dokar haraji, domin kare talakawa daga ƙarin nauyin rayuwa." in ji sanarwar.
ADC ta ce "Duk wani sauyi a tsarin haraji ya kamata ya rage wahala ne ba ƙara jefa jama’a cikin talauci ba."
Haka kuma, ADC ta buƙaci gwamnati ta mayar da hankali kan harajin kayan alatu da ribar da ta wuce kima da kamfanonin da ke da rinjaye, da yaƙi da cin hanci da rashawa maimakon ɗora haraji kan talakawan da ke fama da tsadar rayuwa.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa dole ne a samar da ƙaƙƙarfan kariyar doka domin kare haƙƙin masu biyan haraji.
Ta kuma yi gargaɗin cewa idan aka tilasta aiwatar da wannan sabuwar dokar harajin ba tare da dakatarwa da tattaunawa ba, gwamnati ce za ta ɗauki alhakin duk wani abu da ya biyu baya na zamantakewa da tattalin arziki.
Amurka na neman mayar da ƙasata ƙarƙashin mulkin mallaka- Shugaban Venezuela
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro, ya zargi Amurka da kokarin mayar da ƙasarsa wani yanki da ke karkashin mulkin mallaka.
Shugaban ya ce Venezuela ba zata zama karkashin mulkin mallakar wani ko wata ba har abada.
Cikin wani jawabi da ya gabatar na nuna turjiya, ya ce duk wani yunkuri na hamɓarar da gwamnatinsa ba zai yi tasiri ba.
Kalaman nasa na zuwa ne kwana guda bayan shugaba Trump ya sanar da dakatarwa da kuma sanya takunkumi a kan wasu tankokin dakon mai, yana mai cewa yanzu Venezuela na kewaye da sojojin Amurka.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta buƙaci ɓangarorin biyu da su daina rura wutar rikicin, sannan kuma shugabar Mexico, Claudia Sheinbaum, ta yi kira da a zauna a tattauna domin kare zubda jini
Tawagar Najeriya ta gana da shugaban Burkina Faso
Asalin hoton, Alkasim Abdulkadir /X
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya aike da wata tawaga mai ƙarfi zuwa Burkina Faso domin tattauna batun matuƙan jirgin saman sojojin Najeriya da ake riƙe da su a ƙasar, sakamakon saukar gaggawa da jirginsu ya yi a ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ta gana da Shugaban Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, a Ouagadougou.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin watsa labarai na minitsan Alkasim Abdulkadir ya fitar a shafin sada zumunta ta X.
A yayin ganawar, Ambasada Tuggar ya miƙa saƙon gaisuwa da goyon baya daga Shugaba Tinubu ga Shugaba Traoré, tare da jaddada muhimmancin kyakkyawar alaƙa da makwabtaka tsakanin ƙasashen biyu.
Shugaban Burkina Faso ne ya tarbi tawagar tare da nuna godiya ga saƙon alheri daga Shugaban Najeriya.
Ɓangarorin biyu sun cimma matsaya cikin fahimta kan batun jami’an sojojin saman Najeriya da aka riƙe, inda aka amince da warware lamarin ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.
Asalin hoton, Alkasim Abdulkadir /X
Tawagar ta kuma kai ziyara wajen ganin halin da jami’an ke ciki, inda aka tabbatar da cewa suna cikin ƙoshin lafiya da ƙwarin gwiwa.
Tattaunawar ta kuma taɓo batutuwan ƙarfafa alaƙar siyasa da tsaro da tattalin arziƙi, tare da jaddada buƙatar haɗin gwiwa wajen tinkarar matsalolin tsaro da ke addabar yankin Sahel da Yammacin Afirka baki ɗaya.
A nasa ɓangaren, Ambasada Tuggar ya sake jaddada ƙudurin Najeriya na kyakkyawar makwabtaka da ci gaba da hulɗa da Burkina Faso, yana mai cewa ƙasar na goyon bayan duk wani yunƙuri da zai tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki a yanki
Me ya kai Abubakar Malami komar EFCC?
Asalin hoton, Malami/EFCC/BBC COLLAGE
A ranar Laraba ne tsohon ministan shari'ar Najeriya a zamani marigayi Muhammadu Buhari, Abubakar Malami ya ɓara cewa jami'an hukuma da ke yaƙi da masu yi wa ƙasa zagon ƙasa, EFCC sun kai wani samame ofishinsa da gidajensa a Abuja da Kebbi.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mohammed Bello ya fitar, Malami ya ce samamen na EFCC sun faru ne jim kaɗan bayan da ofishin nasa ya saki wata sanarwa da ke magana kan sashe na 9 na rahoton Ayo Salami da ake zargin ya samu shugaban hukumar EFCC na yanzu da laifi.
Sanarwar ta kuma ce jami'an hukumar ta EFCC sun yi abin da suka yi ne ba tare da sanar da Malami ba sannan sun kasance suna ta faman neman takardu da suke tsammanin na da alaƙa da rahotan na Ayo Salami.
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya na labaran kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a cikin Najeriya da sauran sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.