
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Brazil, Neymar, ya tsawaita kwantiraginsa da Santos har zuwa ƙarshen kakar 2026, yayin da yake ƙoƙarin ganin an gayyace shi gasar cin kofin duniya.
Ɗan wasan mai shekaru 33, wanda ya koma ƙungiyar da ya fara yiwa tamaula tun yana matashi, bai buga wa Brazil wasanni ba, saboda fama da jinya.
Tsohon ɗan wasan Barcelona da Paris St-Germain ya na buga wasanni duk da raunin da yake ɗauke da shi domin taimaka wa Santos wadda ba ta faɗi ba daga babbar gasar Brazil a kakar da ta wuce, inda ya zura ƙwallaye biyar a wasa biyar na ƙarshe.
Daga bisani an yi masa tiyata a gwiwar ƙafarsa ta hagu, don ya samu shiga cikin tsare-tsaren kocin Brazil, Carlo Ancelotti, a wannan bazarar.
Ancelotti ya sanar a watan Oktoba cewa dole ne Neymar — wanda shi ne dan wasan da ya fi kowa zura kwallaye a tarihin Brazil da guda 79 a raga — ya kasance cikin koshin lafiya kuma kan ganiya kafin a sake kiransa.
Neymar ya shafe wata 12 ba tare da buga wasa ba bayan jijiyar gwiwa a watan Oktoban 2023.
An shirya zai koma cikin tawagar kasa a bara bayan wata 17 na rashin buga wasa, amma an tilasta masa janyewa daga tawagar sakamakon raunin da ya ji.
Brazil za ta kara da Scotland da Morocco da Haiti a rukuni na uku a gasar cin kofin duniya, wadda za ta fara wasa a ranar 11 ga watan Yuni a wasanin da za a yi haɗaka a Amurka da Canada da kuma Mexico.


















