A nan na kawo karshen sai mun kara haduwa a wani shirin
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skipper Tudun Wada nake ce muku asuba ta gari.
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan wasan Najeriya da Mozambique karawar zagaye na biyu gasar kofin nahiyar Afirka 2025/26 da ake yi a Moroko.
Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skipper Tudun Wada nake ce muku asuba ta gari.

Asalin hoton, BBC Sport

Asalin hoton, BBC Sport
Super Eagles za ta buga kwata fainal da duk wadda ta yi nasara tsakanin Aljeriya ko Jamhuriyar Congo ranar Asabar.
Super Eagles ta ci wasa na huɗu a jere a Masar ta kai ƙwata fainal
Daf ake a tashi daga karawar Najeriya na shirin kai wa zagayen ƴan takwas ita kuwa Mozambique na shirin komawa gida.
Najeriya na daf da kai wa zagayen kwata fainal a Afcon a Morocco.
Super Eagles ta yi canji biyu, inda Paul Onuachu da kuma Samuel Chukwueze suka canji Akor Adams da Ademola Lookman.
Onuachu ne ya fara cin ƙwallon da Najeriya ta ci Uganda 3-1 a cikin rukuni.

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Mozambique, Chiquinho Conde, shi ne ɗan wasan tsakiya mai shekaru 20 a cikin tawagar farko ta Mozambique a AFCON 1980, sannan ya taka rawa yayin da suka samu makin farko a 1996, har ya zama kaptin a gasar 1998.
Yanzu Conde, wanda kuma ya jagoranci kasar zuwa kunnen doki a wasa da Masar da Ghana a gasar 2023, ya rubuta tarihi cin wasan farko a Afcon bayan doke Gabon 3-2 a matakin rukuni a wannan gasar.
Kawo yanzu Super Eagles ta ci ƙwallo 12 a gasar da ake yi a Morocco.
Koda yake an zura mata huɗu a lokacin wasannin cikin rukuni.

Asalin hoton, Getty Images
Super Eagles ta zama ta farko da ta ci ƙwallo huɗu a bana a Morocco kuma ba tare da an zura mata ko ɗaya ba.
Moses Simon ya miƙa kwallo zuwa ga Ademola Lookman a bakin da'irar Mozambique, wanda ya kai kwallon ga Akor Adams a gefen dama.
Dan wasan da aka bai wa kwallon ya buga da ƙarfi mta kuma faɗa raga.

Asalin hoton, Getty Images
Wanda ya ci ƙwallo biyu, Victor Osimhen ya fita daga filin an maye gurbinsa da Moses Simon.
Daga gani an samu rashin jituwa tsakanin Osimhen da Lookman, watakila shi ya sa Eric Chelle ya cire shi domin kada faɗan ya faɗaɗa.

Asalin hoton, Getty Images
Haka kawai ɗan wasan Mozambique, Faizal Bangal ya ja rigar ɗan ƙwallon Najeriya, Calvin Bassey.
Mozambique ta yi canji na uku ta maye gurbin Witi da matashi mai shekara 21 Chamito.
Abun tausayi ga Ernan. Mai tsaron ragar Mozambique ya sha ci uku, yanzu ya sake faɗuwa karo na biyu domin a duba shi.
A wannan karon, alamar rauni a gwiwar hagu ne, amma ya ɗaga tsaye ya koma ya ci gaba da wasan.
Bright Osayi-Samuel na Birmingham City ya buga ƙwallo wacce ta kusa shiga raga daga bugun da ya samu daga Ademola Lookman.
Daga nan Mozambique suka kai hari mai ƙyau, inda Witi ya yi yunƙurin buga kwallo amma an ƴan wasan Najeriya sun yi masa yawa.

Asalin hoton, Reuters
Ademola Lookman ya ya bajintar jan kwallo zuwa ragar Mozambique daga nan Victor Osimhen ya samu ya kuma buga ta faɗa rana na biyu da ya ci a bana kuma na uku a Morocco.