Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/12/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/12/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Fararen hula na shan baƙar wahala a birnin El Fashe na Sudan - MDD

    Suda

    Asalin hoton, Mohamed Zakaria/BBC

    MDD ta ce ta ganewa idonta yadda farar hula ke tagayyare cikin bakar yunwa da tashin hankali a ziyarar farko da ta kai birnin El Fasher na Sudan tun bayan karbe ikon shi daga hannun 'yan tawayen RSF a watan Oktoba.

    Wakiliyar BBC ta ce a ranar Juma'a ne karamar tawagar hukumar jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta kai ziyarar El Fasher, ta farko cikin kusan shekara 2, tun bayan kawanyar da 'yan tawayen RSF suka yi wa birnin.

    Daraktar tsare-tsare na ayyukan jin kai na Majalisar Denise Brown, ta bayyana abin da suka gani da ainahin inda aka aikata mugun laifi, kuma kwararru kan kare hakkin dan adam za su gudanar da binke kan hakan, ya yin da ofishinta zai maida hankali kan kai agaji.

  2. Ƴan kasuwa sun yi zanga-zangar karyewar darajar kuɗin Iran

    Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    An shiga kwana na biyu da ƴan kasuwa da masu tsaron shaguna suka fito tituna domin yin zanga-zanga a birnin Tehran, inda suke zanga-zanga kan yadda darajar kuɗin ƙasar ke durƙushewa.

    Hotuna da bidiyon da ke wadari a shafukan sada zumunta, sun nuna ƴan kasuwar sun yi dirshan a yankin kasuwancin Iran suna rera waƙoƙin ƙin jinin gwamnatin shugaba Mas'oud Pezeshkian.

    Hukumomi sun yi kakkausan gargadi kan zanga-zangar, da sauya gwamnan babban bankin ƙasar amma duk da haka ƴan ƙasar sun yi biris.

    Darajar Riyal ɗin ƙasar Iran ta faɗi da kusan kashi 50 cikin 100 cikin shekara guda, lamarin da ake dangantawa da matsin lamba da takunkuman ƙasashen yamma.

  3. Ina fata za a yi gaggawar cimma matsaya kan yaƙin Gaza - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Donald Trump na Amurka sun gana da Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu a Maralago da ke birnin Florida, inda suka tattauna kan batun Gaza da wasu batutuwa.

    Wannan ne karo na 6 da suke haduwa tun bayan dawowar Mr Trump fadar White House a farkon shekarar nan.

    Wakiliyar BBC ta ce Amurka ta zamo babbar mai tallafawa Isra'ila tun bayan barkewar yakin Gaza shekaru 2 da suka gabata.

    Sai dai haduwarsu ta yau gwaji ne kan alakar da ke tsakaninsu musamman da ake tunkarar babban zabe a Isra'ila a watan gobe.

    Da yake jawabi ga 'yan jarida a lokacin isowar Netanyahu, Trump ya ce yana fatan za a gaggauta cimma matsaya kan kashi na biyu na yarjejeniyar kawo karshen yakin Gaza.

  4. Wane ne Anthony Joshua, ɗan damben duniya da ya yi hatsari a Najeriya?

    Joshua

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da cewa fitaccen ɗan damben nan na Birtaniya, wanda asalinsa ɗan Najeriya ne, Anthony Joshua ya yi hatsarin mota inda mutum 2 suka mutu.

    Mr Joshua ya tsallake rijiya da baya da ƙananan raunuka, a hatsarin da ya faru a kan babban titin Legas zuwa Ibadan a kudu maso yammacin Najeriya, sannan tuni aka fara gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin motar.

    Hotunan da aka yaɗa a intanet sun nuna Joshua mai shekara 36 cikin motar da ta yi raga-raga, kafin daga bisani a fito da shi.

  5. Tinubu ya jajanta wa Anthony Joshua bisa hatsarin mota a Najeriya

    Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike da saƙonsa na jaje ga fitaccen ɗan damben duniya Anthony Joshua, wanda ha yi hatsari a Najeriya, inda mutum biyu abokan rakiyarsa suka mutu.

    A wata sanarwa da Tinubu ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya bayyana alhininsa kan lamarin, sannan ya masa fatan samun sauƙi cikin gaggawa.

    "Ina aika wa da saƙon jajena ga waɗanda hatsarin ya rutsa da su a babban titin Legas zuwa Ibadan, inda mutum biyu suka mutu, sannan wasu suka jikkata."

    Shugaban ya ce wannan iftila'i ne babba da zai ɗaga hankalin mutane, sannan ya bayyana jigon tafiyar, Anothony Joshua a matsayin ɗan wasan da ake alfahara da shi.

    "A matsayinka na ɗanwasa, ka daɗe kana nuna juriya da jajircewa da kuma matuƙar ƙaunar wannan ƙasar. Waɗannan abubuwan ne suka sa ka zama abin alfahari kuma abin koyi a ƙasar. A irin wannan lokaci, dole mu ƙarfafa maka gwiwa a matsayin ƴanuwanka."

  6. Yadda ƙungiyar Lakurawa da Trump ya kai wa hari suka ɗaɗe suna firgita ƴan ƙauyukan Najeriya

    Tangaza

    Asalin hoton, Gift Ufuoma/BBC

    Tun kafin hare-haren Amurka, ƙauyukan da ke jihohin arewa maso yamma sun daɗe a cikin zullumi saboda barazanar hare-haren ƴan bindiga.

    Mayaƙan waɗanda suke amfani da muggan makamai, suke yawan amfani da kayan sojoji sun daɗe a garin Tangaza, wani ƙauye jihar Sokoto da ke da iyaka da jihar Neja na tsawon lokaci, wato Lakurawa.

    Mazauna garin Tangaza, waɗanda yawanci musulmi ne sun ce suna zargin yawancin ƴan Lakurawa ƴan Jamhuriyar Nijar ne da Mali, kuma yawanci suna tsoronsu.

  7. Mutum 12 sun mutu a CAR bayan sojojin hayan Rasha sun kai hari a wata kasuwa

    Sojojin hayan Rasha daga ƙungiyar Wagner sun kashe aƙalla mutum 12 a ranar 25 ga Disamba a Hadjlitaye, lardin Vakaga da ke arewacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR), bayan sun kai hari a wata kasuwa kamar yadda shafin labarai mai adawa da gwamnati, Corbeau News, ya ruwaito.

    Rahoton ya ce sojojin hayar sun buɗe wuta inda suka kashe mutum takwas, lamarin da ya haifar da martani daga ’yan tawayen ƙungiyar FPRC da ke sayen kayayyaki a kasuwar.

    An ce an yi musayar wuta na tsawon mintuna da dama, inda aka kashe sojojin hayan Rasha biyu da ’yan sa-kai biyu na Boromata da ke taimaka musu.

    Sojojin hayan, waɗanda aka tura CAR tun 2018, ana yawan zarginsu da kisan gilla, azabtarwa, da tsoratar da fararen hula a sassa daban-daban na ƙasar.

  8. Anthony Joshua ya tsallake rijiya da baya a hatsarin mota a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yansanda a Najeriya sun ce fitaccen dan danben nan dan Birtaniya asalin Najeriya Anthony Joshua ya yi hatsarin mota inda mutum 2 suka mutu.

    Joshua ya tsallake rijiya da baya da kananan raunuka, a hatsarin da ya faru a kan babban titin Lagas zuwa Ibadan a kudu maso gabashin Najeriya.

    An fara gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin motar.

    Hotunan da aka yaɗa a intanet sun nuna Joshua mai shekara 36 cikin motar da ta yi raga-raga, kafin daga bisani a fito da shi.

    Ya dai kawo ziyara Najeriya inda ya ke da dangi, bayan doke abokin karawarsa Jake Paul a wasan da suka kara a farkon watan nan. do a headline for this

  9. Amurka ta ba da tabbacin bai wa Ukraine cikakken tsaro na shekaru 15

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ukraine Zelensky ya ce Amurka ta ba da tabbacin bai wa ƙasarsa cikakken tsaro har tsahon shekaru 15 kan duk wata barazana daga Rasha.

    Sai dai ya ce ina ma wa'adin zai wuce wannan shekarun.

    Da ya ke magana bayan ganawa da shugaba Trump a birnin Florida, Mr Zelensky idan babu tabbacin tsaron to ba za a ce yaƙin ya zo karshe ba, saboda a kowanne lokaci barazanar Rasha na iya tasowa.

    Har yanzu akwai batutuwan da ba a ƙarƙare ba, musamman na tilastawa Ukraine sadaukar da wasu yankunan ta ga Rasha.

    Duk da haka dai shugaba Trump ya bai wa Ukraine tabbacin tsaronta da kashi 95.

  10. DSS ta kama waɗanda ake zargi da kisan kai bayan shekara biyu

    ...

    Asalin hoton, DSS

    Jami’an hukumar DSS sun kama mutanen da ake zargi da kashe wata farfesa a fannin ilimin jijiyoyi (Neurology), Ekanem Philip Ephraim, kusan shekaru biyu bayan faruwar kisan kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

    Wata majiyar da ta bayar da sahihan bayanai ne ta tabbatar wa gidan talabijin na Channels ɗin da lamarin a ranar Litinin.

    Majiyar ta ce an kama mutanen biyu ne a wani asibiti a jihar Cross River a ranar 27 ga Disamba, yayin da suke shirin sace wani babban likita.

    Rahoton ya nuna cewa DSS ta shafe lokaci tana bibiyar ƙungiyar masu garkuwa da mutane tun bayan kisan Farfesa Ephraim a watan Yulin 2023.

    A wancan lokaci, wasu ‘yan bindiga da suka yi shigar marasa lafiya ne suka sace farfesar daga asibiti.

    Daga bisani, mutanen da aka kama sun amsa laifin aikata kisan, inda suka ce sun kashe ta ne bayan karɓar kuɗin fansa sau da dama daga iyalanta.

  11. 'Ba lallai mu yi nasara a 2027 idan har ba a magance rikicin jam'iyar PDP ba'

    ...

    Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ya ce jam'iyyar PDP na iya kasa samun nasara a babban zaɓen 2027 idan shugabancinta ya gaza magance rikice-rikicen cikin gida da ke addabarta yana mai gargaɗin cewa hakan na iya kawo cikas ga burin PDP na komawa kan mulki.

    Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata tattaunawa da manema labarai a ofishinsa da ke Port Harcourt, babban birnin Jihar Rivers.

    Ya bukaci shugabancin PDP da su ɗauki matakan gaggawa wajen warware rikicin da ke cikin jam’iyyar kafin a shiga zagayen zaɓe na gaba.

    A cewarsa, shugabancin jam’iyyar ba ya nuna cikakken mayar da hankali, kuma ba ya karɓar shawarwari.

    Ya ce "Idan shugabanni jam'iyyar suka amince da sun yi kuskure tare da tambayar kansu abin da ke haddasa matsalolin da suka fuskanta da kuma yadda za a gyara su, to jam’iyyar za ta iya farfadowa."

    Jam’iyyar PDP dai ta daɗe tana fama da rikice-rikicen cikin gida tun bayan zaɓen 2023, lamarin da ya janyo ficewar wasu mambobinta, ciki har da gwamnoni masu ci, zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

  12. Mutum shida sun mutu a harin ƴanbidiga a Ecuador

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum shida, ciki har da wani yaro ɗan shekara biyu, sun mutu sakamakon wani mummunan hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a birnin Puerto Lopez da ke ƙasar Ecuador.

    Harin ya faru ne a wata kasuwa da ake sayar da kifi da sauran halittun ruwa, inda jama’a ke cunkushe a lokacin.

    Rahotanni sun ce maharan da dama ne, wasu a kan babura wasu kuma a cikin wata mota, suka buɗe wuta kan mutanen da ke kasuwar kafin su tsere daga wurin.

    Lamarin ya haifar da firgici da tashin hankali a yankin, yayin da mutane ke neman mafaka.

    Har yanzu 'yansanda na musamman da aka tura yankin na can suna ta neman 'yan bindigan.

    'Yansandan sun ce, ƙila harin ba zai rasa nasaba da ramuwar gayya ta fadan 'yan daba ba.

    Da wannan, a yanzu jumullar mutum tara kenan suka rasu a makon nan a tashe-tashen hankali a birnin Puerto Lopez.

  13. Tashin farashin kuɗin jirgin sama a Disamba bai da alaƙa da haraji - NCAA

    ...

    Asalin hoton, NCAA/Facebook

    Hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta musanta iƙirarin cewa harajin gwamnati ne ya haddasa tashin farashin tikitin jiragen sama na cikin gida da aka samu a watan Disamba.

    Daraktan hulɗa da jama’a da kare haƙƙin masu amfani na hukumar, Michael Achimugu ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi.

    A cewarsa, ƙaruwar farashin ta samo asali ne daga yanayin kasuwa, inda yawan buƙatar tafiya a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara ke haifar da tashin farashi.

    Ya ce wannan lamari abu ne da ke faruwa a kowace shekara, kuma ba jiragen sama kaɗai ba ne ke fuskantar irin wannan hauhawar farashi a lokacin bukukuwan ƙarshen shekarar.

    Achimugu ya ƙara da cewa ana sa ran farashin zai fara raguwa a watan Janairu, musamman bayan mako na biyu, yayin da buƙatar tafiya ke raguwa.

    “Yanayin kasuwa ne kawai. ‘Yan Najeriya ne ke yi wa junansu. Ba laifin gwamnati ba ne. Farashin jiragen sama a Disamba ba shi da alaƙa da haraji ko kaɗan. Haraji ba su ƙaru a Disamba ba, kuma da alama farashin zai ragu bayan mako na biyu na Janairu,” in ji shi.

  14. Har yanzu ba a kammala cimma yarjejeniyar zaman lafiyar Ukraine da Rasha ba - Trump

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa har yanzu akwai batutuwan da ba a cimma matsaya a kai ba, bayan tattaunawar da ya yi a gidansa na Florida tare da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, kan yarjejeniyar zaman lafiya da za ta kawo ƙarshen yakin Ukraine da Rasha.

    Duk da haka, Trump ya nuna cewa suna kusa da cimma matsayar kawo ƙarshen yakin.

    A yayin da yake magana da 'yan jarida, ya bayyana cewa shugabannin biyu sun tattauna kan yadda za a samar da tsaro, inda suka cimma matsaya kan kusan kashi 95 cikin dari na batutuwan.

    Shugaban Amurka ya kara da cewa abu na gaba da zai faru shi ne tattaunawa da Moscow, inda ake bukatar ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Rasha domin warware sauran matsalolin.

    A lokacin da aka tambaye shi kan wane batu ne yanzu ya kasance karfen-kafa da ba a warware ba, Trump ya bayyana cewa maganar ƙasa ce.

    Ya kara da cewa, Rasha tana son ganin Ukraine ta hakura da wasu yankunan da ta kama, inda a halin yanzu Ukraine na riƙe da kusan kashi 20 cikin 100 na yankunanta.

  15. Muna kira ga gwamnan Kano da ka da ya koma APC - Dungurawa

    ..

    Asalin hoton, Dunguruwa/Facebook

    Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano, Hon. Suleiman Hashim Dungurawa ya ce gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da duk waɗanda za su bi shi zuwa jam'iyyar APC sun yi hakan ne domin raɗin kansu sannan sun yi iya yinsu wajen ganin ba su ɗauki matakin sauya sheƙar ba.

    "Ina so na sanar cewa da jam'iyya ta Kano, da kasa da Jagora na Kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwasiyya da sauran jagorori duk abin da yake faruwa ba da lamuncewarmu ba ne. Hasali ma, duk abin da za mu iya mun yi don su yi hakuri kar su koma APC saboda hakkinmu da ke kansu, da kuma hakkin jama'ar Kano amma abubuwa sun ci tura," in ji Suleiman Hashin.

    Sai dai kuma shugaban jam'iyyar ta NNPP a Kano ya roƙi gwamnan da ya mayar da wuƙarsa kube.

    "A madadinmu gaba ki ɗaya, muna sake rokonsu da su yi wa Allah su yi wa Annabi ka da su bar wannan jam'iyyar kar su bar wannan jam'iyya su koma wadda aka yi hamayya da ita kuma talakawa da sauran masu zabe suka ka da ita."

    Daga ƙarshe Suleman Hashimu ya tabbatar wa da jama'a cewa shi da wasu jiga-jigan ƴan jam'iyyar da ake ta yaɗa jita-jitar cewa su ne suka haɗa gwamna Abba da Kwankwaso ba gaskiya ba ne.

    "Ina son na jawo hankalin masu yadda jita-jita cewa, musamman akwai wasu da suke hada Gwamna da Jagora Sanata Kwankwaso; musamman mataimakin gwamna, da Sanusi Surajo da Hashimu Dungurawa da Sanata Rufai Hanga, ana ganin ana zargin mu saboda ganin kusancinmu da jagora, amma mu ba mu taba hada kowa da jagora ba, amma idan wani yana da shaida sai ya fito da ita, kuma Allah ya ba su hakuri."

  16. Me ya faru Abba zai koma APC ya bar Kwankwaso a NNPP?

    ...

    Asalin hoton, Kano State Government

    Alamu na nuna cewa duk wata jita-jita yanzu ta ƙara dangane da ko gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

    Kusan yanzu batun da ake ta yi ke nan a kafafen watsa labarai na jihar da ma tsakanin ƴan siyasa har ma da ma'aikatan gwamnati.

    Wannan dai na zuwa ne mako biyu bayan da shugaba Tinubu ya yi wa gwamnoni gargaɗi da barazanar cewa idan ba su aiwatar da hukuncin kotun ƙolin ƙasar ba da ta yanke hukuncin jihohi su sakar wa ƙananan hukumomi mara to shi zai fara aike musu da kuɗaɗensu kai tsaye.

    Yaushe Abba zai koma APC?

    Wata majiya ta tabbatar wa BBC cewa ana sa ran gwamnan na Kano, Abba Kabiru Yusuf zai sanar da sauya sheƙar zuwa jam'iyya mai mulki a ranar Laraba lokacin taron majalisar zartarwar jihar.

    Majiyar ta kuma tabbatar wa da BBC cewa kawo yanzu ba kowane ya san inda gwamnan yake ba.

  17. China ta fara wani gagarumin atisayen soji a kusa da Taiwan

    ...

    Asalin hoton, Eastern Theater Command

    China ta ce ta fara wani babban atisayen soji a kusa da tsibirin Taiwan, inda rundunar soji ta ƙasar ta tura dakarunta na sama da na ruwa domin gwajin yadda za su iya ƙulle ko datse hanyar ruwa zuwa tsibirin.

    China na ɗaukar Taiwan a matsayin wani yanki na kasarta, kuma wannan atisayen na soji yana cikin shirin tabbatar da iko da karfi a yankin.

    Gwamnatin Taiwan ta soki wannan matakia matsayin wata takala ga dokokin duniya da tsare-tsaren zaman lafiya na kasa da kasa.

    Taiwan ta ce ta tura dakarun sojinta domin mayar da martani ga atisayen sojin China, tare da ƙarfafa tsaron iyakokinta.

    Wannan dambarwa ta yaƙi ta faro ne bayan da Amurka ta ƙaddamar da sayar da makamai masu ƙarfi ga Taiwan, wanda ƙasar Taiwan ta shaida cewa ba ta taɓa samun irin wannan tallafi daga Amurka ba a baya.

  18. Ƴan majalisa sun buƙaci a jingine sabuwar dokar haraji

    ...

    Asalin hoton, other

    Majalisar wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya ta jingine shirinta na fara aiwatar da sabuwar dokar haraji mai cike da ce-ce-ku-ce da ruɗani, har sai an kammala bincike kan zargin sauya wasu daga cikin dokokin da majalisar ta amince da su.

    Ɓangaren marasa rinjaye a majalisar sun bayyana bukatar dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji domin gudanar da bincike mai inganci, wanda majalisar ta kafa don gano gaskiyar batun.

    Wannan kiran ya biyo bayan zargin cewa an sauya wasu sassa na dokokin haraji bayan da majalisar ta amince da su, wanda hakan ya janyo mummunan ruɗani a tsakanin sassan gwamnati da ƴan Najeriya.

    Zarge-zargen sun samo asali ne daga bambance-bambancen da aka samu tsakanin dokokin da majalisar ta amince da su da kuma waɗanda shugaban ƙasa ya rattaɓa hannu a kai.

    A halin yanzu, ɗaya daga cikin shugabannin majalisar, ya bayyana cewa akwai bukatar a tabbatar da gaskiyar wannan al'amari kafin a ci gaba da aiwatar da dokar.

    Duk da haka, ɓangaren gwamnatin ya nesanta kansa daga zargin, inda ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa sabuwar dokar haraji za ta fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2026, kuma akwai haɗin kai tsakanin gwamnati da majalisar kan wannan lamari.

    Ministan ya kuma ce, idan akwai wata matsala, to daga ɓangaren majalisar ne.

    A yanzu haka, majalisar ta kafa kwamitin bincike domin gano gaskiyar lamarin.

  19. Yadda addinin Musulunci ya shiga Najeriya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Tarihi ya nuna cewa addinin Musulunci ya shiga Najeriya ne ta hanyoyi daban-daban, musamman kasuwanci da masu wa'azi, ba kamar yadda wasu suke tunanin yaƙi ne ya kai addini ƙasar ba.

    Tarihi ya nuna malamai daga arewacin Afirka sun taka rawa wajen isar da addinin zuwa wasu sassan ƙasar tun kafin Daular Usmaniyya, sannan akwai ƙaulin da ke nuna yadda Musulunci ya zo Daular Borno.

    Haka kuma yadda addinin ya yaɗu zuwa ƙasar Hausa da sassanta ma yana da jan hankali, musamman ganin yadda ake alaƙanta al'ummar Hausa da addinin na Musulunci da daɗewa.

    Domin sanin yadda addinin Musulunci ya shiga Najeriya, da yadda ya yaɗu zuwa yankunan ƙasar da rawar da jihadin Ɗanfodio ya taka, mun yi nazari domin rabe aya da tsakuwa ka tarihin.

  20. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barka da safiyar ranar Litinin wanda ake yi wa take da tushen aiki wai ko nasara ma na tsoronki.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu a shafin namu na kai tsaye da muke kawo muku labarai da rahotanni na musamman.

    Za ku kuma iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.