Sai da safe
Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Alhamis.
Mu haɗu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbi daga sassan duniya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/12/2025.
Daga Aisha Babangida da Umar Mikail
Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na ranar Alhamis.
Mu haɗu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbi daga sassan duniya.

An amince wa Isra'ila shiga gasar waƙoƙi ta Eurovision ta shekara mai zuwa bayan hukumar da ke shirya gasar ta ki yarda a kaɗa ƙuria kan batun halartar Isra'ilar.
Nan take ƙasashen Sifaniya da Netherlands da Irelandsu sukka sanar da ƙaurace wa gasar, matsayin da tun farko suka yi barazanar ɗauka idan hakan ta faru. Daga baya ƙasar Slovenia ma ta bi sawunsu.
Ƙasashen na nuna rashin jin dadinsu kan abubuwan da sojojin Isra'ila ke yi a Gaza.
Ita kuwa kasar Jamus, wadda ita ce ɗaya daga cikin manyan masu bai wa shirin tallafin kudi, ta yi gargadin za ta janye idan aka cire Isra'ila daga cikin gasar.
Dakarun rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar tarwatsa sansanonin 'yanbindiga tare da kashe da dama daga cikinsu a jihar Taraba da ke tsakiyar ƙasar.
Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Umar Mohammed, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa dakarun aikin Operation Whirl Stroke (OPWS) ne suka kai samamen ranar Talata a yankunan Shiid, Agia, da Tyozua da ke ƙaramar hukumar Takum.
Ya ce sun kai samamen bayan samun bayanan sirri na 'yanbindigar da ke karakaina a yankin.
Ya ƙara da cewa sun yi nasarar kama wani jagoran 'yanfashin mai suna Dahiru Maigari. Sai dai rundunar ba ta faɗi adadin 'yanbindigar da ta kashe ba, ko kuma yanayin da nata dakarun suke ciki bayan fafatawar.

Asalin hoton, Reuters
Shugabannin ƙasashen Rwanda da Dimokradiyyar Congo sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Washington da nufin kawo karshen rikicin da aka kwashe tsawon lokaci ana yi a gabashin Congo.
Shugaban Amurka Donald Trump ne ya karbi bakuncin Felix Tshisekedi na Congo da Paul Kagame na Rwanda, a yunƙurin zaman lafiyar da Amurkar ta shiga tsakani.
Sun sanya hannun ne duk da cewa ana ci gaba da gwabza faɗa tsakanin dakarun gwamnatin Congo da mayaƙan M23 masu goyon bayan Rwanda.
"Wannan rana ce mai muhimmanci ga Afirka da ma duniya baki ɗaya," in ji Trump.
Wakilin BBC ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce fiye da mutum miliyan shida ne aka raba da muhallansu a gabashin Congo.

Asalin hoton, EPA
Wani bincike da ya sanya ido kan ayyukan ma'aikatar tsaron Amurka ya gano cewa akwai yiwuwar Sakataren Tsaron Pete Hegseth ya sanya rayuwar sojojin ƙasar cikin haɗari saboda yadda ya yi amfani da manhajar aika sakonni ta Signal.
Binciken ya yi nazari kan yadda aka sanya wani ɗanjarida cikin zauren tattaunawa na manhajar a yayin da ake muhawara kan batun shirin da Amurka ke yi na kai hari kan Yemen.
Ofishin supeto janar na yansanda sun tabbatar da cewa Mista Hegseth ya aika sakonnin sirri ta manhaja wadda ba ta da cikakken tsaro, wanda hakan ya yi barazanar kawo tarnaƙi kan shirin, da sanya jam'ian sojin cikin haɗari.
Wannan abin kunya ne ga Mista Hegseth wanda ake suka kan mummunan harin da aka kai kan jiragen ruwan da ake zargi na safarar ƙwayoyi ne a yankin Caribbean.

Asalin hoton, Getty Images
Kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, William Troost-Ekong, ya sanar da yin ritaya daga taka wa ƙasar leda.
Ekong mai shekara 32 ya sanar da matin cikin wata sanarwa a shafukansa na sada zumunta kwana ɗaya bayan mai horarwa Eric Chelle ya zaɓe shi cikin tawagar farko ta 'yanwasan da za su wakilci Najeriya a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2025.
"Lokaci ya yi da zan miƙa damar, na miƙa ƙyallen kyaftin ɗin," in ji shi. "A yau, ina sanar da yin ritaya daga taka leda a matakin ƙasa da ƙasa."
Ɗanwasan bayan ya buga wa Super Eagles wasa 83 tare da cin ƙwallo takwas cikin shekara 10. Shi ne ɗanwasa mafi hazaƙa a gasar Afcon ta 2023 da aka yi a Ivory Coast, inda Najeriya ta ƙare a mataki na biyu.
A watan Agustan 2024 ne Ekong ya koma taka wa ƙungiyar Al-Kholood ta Saudiyya leda daga PAOK ta ƙasar Girka.

Asalin hoton, Reuters
Attajiri mafi arziki a nahiyar Afirka Aliko Dangote ya ce yana ganin amfanin kuɗaɗen da ya zuba jari a Najeriya ƙasarsa ta haihuwa.
Dangote na magana ne a yau Alhamis yayin taron zuba jari da gwamnatin jihar Imo ta shirya a jihar, wanda ya samu halartar baƙi daga ciki da wajen Najeriya.
"Akwai tsare-tsare da dama da gwamnati ta fito da su masu kyau. Najeriya kamar katin waya ne, ba za ku gane darajarsa ba sai kun kankare katin. Mu da muka kankare muna ganin amfanin abin," in ji shi.
"Shawarar da nake bai wa masu kuɗinmu ita ce, don Allah ku zuba jari a cikin gida."
A shekarar da ta gabata ne matatar mai da Aliko ya kashe sama da dala biliyan 20 wajen ginawa ta fara aiki a jihar Legas, wadda ke da ƙarfin tace gangan mai 600,000 duk rana.

Asalin hoton, Reuters
Jaridar New York Times ta ce za ta maka ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon a kotu kan buƙatar ta janye dokokin da ta sanya wa ƴanjaridar da ke rahoto game da sojoji.
Takardar ƙarar ta ce dokokin da aka sanya, kamar na buƙatar ƴanjaridan da ke ma'aikatar su sanya hannu kan wata takardar alƙawari, ya saɓa wa dokar da ta bai wa ƴanjarida ƴanci.
Hakan na nufin ƴanjaridan da aka sahale wa ɗaukar rahoto ba za su iya bayar da rahoto ba sai wanda hukumomi suka amince da su.
Sakataren Tsaro Pete Hegseth ne ya sanar da sabbin dokokin, wanda a baya ya sha samun matsala da ƴanjarida.
Jami'an gwamnatin Amurka sun ce sun ɗauki matakin ne domin hana fitar da bayanai masu hatsari.

Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaron ƙasar bayan amincewar majalisar dattawa.
An yi bikin rantsar da tsohon babban hafsan tsaron ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a yau Alhamis, kwana ɗaya bayan 'yanmajalisar dattawan sun shafe kusan awa biyar suna yi masa tambayoyi yayin tantance shi.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya wallafa hoton bikin rantsuwar a shafinsa na dandalin X.

Asalin hoton, X/STATE HOUSE NG
Sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce "sabon ministan zai fara aiki ne nan take, kasancewar Tinubu na son cin gajiyar nasarorin da aka samu a baya-bayan nan domin hanzarta tabbatar da sauye-sauyen da ake buƙata wajen tabbatar da zaman lafiya a fadin ƙasar.

Asalin hoton, X/STATE HOUSE NG
Janar Musa, wanda aka haifa a shekarar 1967 a garin Sokoto, ya fara aikin soja a matsayin ƙaramin laftanar a shekarar 1991, inda ya yi fice a aikinsa.
A shekarar 2023 ne shugaban Najeriya Bola Timunu ya naɗa shi babban hafsan sojin Najeriya, sannan ya yi ritaya a shekarar 2025.

Asalin hoton, X/STATE HOUSE NG
Cikin wadanda suka halarci bikin rantsar da sabon ministan akwai shugaban majalisar dattijan Najeriya Godswill Akpabio, da shugaban masu rinjaye na majalisar Opeyemi Bamidele, da shugaban kwamitin majalisar dattijai kan shari'a da kare hakkin dan'adam Adeniyi Adegbonmire da ministan yaɗa labarai Mohammed Idris, da mai taimaka wa shugaban ƙasa kan tsaro Nuhu Ribadu.
Sai kuma mai ɗakin sabon ministan Lilian Oghogho Musa; da babban hafsan sojin Najeriya Janar Olufemi Oluyede; da shugaban cocin katolika na Sokoto Matthew Hassan Kukah;da wasu da dama.

Asalin hoton, Maxine Collins/BBC
Gidauniyar Gates ta ce ƙarin yara aƙalla dubu ɗari biyu za su iya mutuwa kafin cika shekara biyar a wannan shekarar, adadin da ya zarta na 2024.
Wannan ne hasashe na farko na ƙaruwar mutuwar yara da za a iya kauce mawa a wannan ƙarnin, wanda za a iya samu sakamakon katse tallafin da ƙasashen duniya ke bayarwa.
Tallafin da ake bayarwa a fannin lafiya ya ragu sosai a wannan shekarar, inda rahoton gidauniyar na shekara shekara ya yi gargadin idan hakan ya ci gaba da faruwa, yara miliyan 16 za su iya mutuwa nan da 2045.
Wakilin BBC ya ce rage adadin yaran da ke mutuwa shi ne babban ci gaban da ƙasashen duniya suka samar tun shekarun 1990.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Rasha Vladimir Putin din ya kafe cewa Rasha za ta ƙwace ikon yankin Donbas da ke gabashin Ukraine da ƙarfin tsiya ta hanyar amfani da karfin soji.
Cikin wani jawabi da ya yi da kafafen yada labaran kasar suka ruwaito, ya ce dole ne sojin Ukraine su tattara su bar yankunan da har yanzu ke hannunsu, in ba haka ba za su ƙwace yankin da ƙarfin tsiya.
Wakilin BBC ya ce yankin Donbas na da matuƙar muhimmanci a mamayar da Rasha ke yi a Ukraine, sai dai bayan shekara goma ana faɗa kans, har yanzu aƙalla kashi ashirin na hannun Ukraine.
Mr Putin ya yi jawabin ne kwana guda bayan ganawa da babban wakilin Trump na musamman Steve Witkoff inda suka tattauna kan shirin zaman lafiya da Amurka ke jagoranta.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Shugaba Putin ya isa Indiya domin tattaunawar da ake sa ran za ta mayar da hankali kan kasuwanci da faɗaɗa alaƙar tsaro.
Wannan ziyarar ita ce irinta ta farko da shugaban na Rashan ya kai zuwa birnin Delhi tun bayan yaƙin da ƙasarsa ta ƙaddamar a Ukraine.
Indiya, kamar China ta kasance babbar mai sayen man Rasha, kuma ƙasashen yamma sun sha zargin ta da tallafa wa yaƙin.
Amurka ta sanya haraje haraje kan Indiya na kusa kashi hamsin domin tilasta mata kawo ƙarshen kasuwancinta da Moscow. Moscow na kuma so Indiya ta ci gaba da siyan makamanta.

Asalin hoton, Facebook
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tura ƙarin sunan mutum 4 ɗoriya a kan waɗanda aka fitar a baya zuwa ga majalisar dattawa domin a tantance su a matsayin jakadun ƙasar da za a tura ƙasashen waje.
Mutum huɗu da Tinubu ya tura su ne: Ibok-Ete Ekwe Ibas, tsohon shugaban riƙon-ƙwarya na jihar Rivers da tsohon ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau.
Sauran kuma su ne Sanata Ita Enang da tsohon gwamnan jihar Imo Chioma Ohakim.
Yanzu dai jimilla shugaban ya tura sunan mutum 65 ke nan da yake buƙatar majalisar ta tantance, inda ake sa ran da zarar an tantance su, zai sanar da ƙasashen da za a tura su.

Asalin hoton, @cenbank
Babban Bankin Najeriya (CBN) a jiya ya soke iyaka kan adadin kuɗin da ake iya ajiyewa a banki tare da ƙara kuɗin da ake iya cirewa daga naira 100,00 zuwa naira 500,000 a kowane mako.
Wannan canji ya fito ne a cikin wata sanarwa da bankin ya aika wa dukkan bankuna wacce Dr. Rita Sike, Daraktar Sashen Tsare-Tsaren Kuɗi da Dokoki, ta sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce daga 1 ga watan Janairu, 2026, za a yi amfani da waɗannan sabbin dokokin kuɗi a duk fadin Najeriya.
"An soke iyaka kan addadin kuɗin aka ake iya ajiyewa a banki da kuma kudin da ake biya idan an wuce iyaka. Haka kuma an ƙara kuɗin da ake iya cirewa zuwa naira 500,000 ga mutum ɗaya kuma naira miliyan 5 ga kamfanoni. Idan aka wuce waɗannan iyakokin, za a cire kuɗin tara.
A bangaren injin cire kuɗi kuma, iyakar kuɗin da mutum zai iya cirewa zai kasance N100,000 a rana kuma N850,000 a kowane mako.
A cewar bankin, an yi sauye-sauyen manufofin ne da nufin rage tsadar sarrafa kuɗi da magance matsalolin tsaro da kuma daƙile haɗarin safarar kuɗi ba bisa ka’ida ba da ke da alaƙa da dogaro da mu’amalar kuɗi kai tsaye.

Asalin hoton, @DefenseNigeria
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na haɗin gwiwa da ke aikin wanzar da zaman lafiya sun kai samame kan wani da ake zargin mai sayar da makamai ne a jihar Plateau.
Rundunar ce ta sanar da hakan a shafin sada zumuntarta na X.
Harin ya gudana ne a ranar 3 ga Disamba, 2025, a Gashish, bayan samun sahihan bayanai kan harkokin wanda ake zargi a kauyen Ranbiri, Kafi Abu, ƙaramar hukumar Barkin Ladi na jihar
Ko da yake wanda ake zargin ya tsere kafin isowar sojojin, bincike mai zurfi a wajen da yake zama ya ba da damar gano wasu abubuwa masu muhimmanci.
Sojojin sun samu nasarar ƙwace makamai irin su bindiga ƙirar AK-47da sauransu.
Jami’an rundunar sun ce har yanzu suna kan aiki wajen bin sawun wanda ya tsere don kamo shi.
Rundunar na ci gaba da sanya ido sosai don hana masu aikata laifuka amfani da wannan yankin wajen safarar makamai.

Asalin hoton, Getty Images
Bayan fiye da watanni takwas na ƙoƙarin diflomasiyya da Amurka da Qatar suka yi don kawo ƙarshen rikicin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango (DRC), har yanzu fararen hula na fuskantar munanan cin zarafi daga kungiyar M23 da sojojin Wazalendo, hadakar ƙungiyoyin makamai da sojojin Kwango ke goyon baya.
Amnesty International ta ce sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin shugabannin DRC da Rwanda a Fadar White House yau zai faru ne yayin da tashin hankali ke ci gaba a gabashin Kwango, inda fararen hula ke ci gaba da fama da wahala mai yawa.
Tigere Chagutah, daraktan yankin Gabas da Kudancin Afirka na Amnesty, ya bayyana cewa tattaunawa da yarjejeniyoyi da aka cimma a Washington da Doha ba su yi tasiri a rayuwar fararen hula ba.
Amnesty ta samu rahotanni kan cin zarafin da ‘yan Wazalendo ke yi da kuma kisan fansa da M23 ke yi ga fararen hula da ake zargi da yin aiki tare da Wazalendo.
Dubban mutane ne aka tilasta musu barin gidajensu a watan Oktoba, yayin da wasu fararen hula ke ɓoye a cikin dazuzzuka saboda tsoron hare-haren kungiyoyi masu makamai a sassan lardin Kivu ta Arewa.
Amnesty ta yi kira ga shugabannin duniya, ciki har da na Amurka da Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka, da su mayar da hankali wajen dakatar da cin zarafin bil’adama.

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin Meta ya fara cire yaran Ostiraliya ‘yan ƙasa da shekara 16 daga dandalin Instagram da Facebook da Threads, mako guda kafin fara dokar haramta wa matasa amfani da kafafen sada zumunta.
An fara sanar da ƴan shekaru 13 zuwa 15 cewa za a rufe shafukansu daga 4 ga Disamba.
Ana sa ran wannan mataki zai shafi kusan masu amfani da facebook 150,000 da Instagram 350,000.
Dandalin Threads kuwa ba za a iya amfani da shi kai tsaye ba sai ta dandalin Instagram.
Dokar ta Ostiraliya, wadda ta zama ta farko a duniya, za ta fara aiki daga 10 ga Disamba, inda kamfanoni za su iya fuskantar tarar har A$49.5m idan suka kasa daukar matakan da suka dace don hana ƙasa da shekara 16 amfani da shafukan.
Meta ta bukaci gwamnati ta tilasta wa rumbun manhajoji tabbatar da shekaru kafin sauke wata manhaja tare da samun amincewar iyaye ga ‘yan ƙasa da 16, domin hakan zai kawar da buƙatar tabbatar da shekaru a kowanne manhaja.
Sauran kafafen sada zumunta da wannan dokar ta shafa sun haɗa da YouTube da X da TikTok da Snapchat da Reddit da Kick da Twitch.

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta yi barazanar saka takunkumai da hana bizar shiga ƙasar kan duk wanda ta samu da hannu a zargin yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
Ministan harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya wallafa a shafinsa na dandalin X cewa matakin martani ne ga matsalar yi wa Kiristoci kisan gilla, zargin da bai bayar da wata hujja a kansa ba.
"Amurka na ɗaukar mataki game da tashin hankali da zalincin da ake yi wa Kiristoci a Najeriya da duniya baki ɗaya," a cewarsa.
"Ofishin harkokin waje zai dakatar da bayar da biza ga waɗanda suka tsara da gangan, ko suka bayar da umarni, ko ɗaukar nauyi, ko take haƙƙin 'yancin yin addini. Matakin hana bizar ya shafi Najeriya da sauran gwamnatoci ko mutane da ke zalintar mutane kawai saboda addininsu."
A jiya Laraba ne wani kwamatin Majalisar Wakilan Amurka ya fitar da rahoto kan zargin, inda wasu 'yanmajalisa suka nanata iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci da gangan a Najeriya.

Asalin hoton, Inec nigeria/facebook
Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta ce daga cikin ’yan Najeriya miliyan 9.89 da suka fara yin rijistar katin zaɓe ta intanet, miliyan 2.57 ne kawai suka kammala cikakken rajista.
Daraktar wayar da kan jama’a, Victoria Eta-Messi, ta ce Osun ce ta fi kowa yawan sabbin masu rijista da lamba 200,251, sannan Kano da 151,604, Imo da 144,912 da kuma Sokoto da 141,526.
Jihohin da suka fi ƙaranci masu rijista sun haɗa da Ekiti da Abia da Ondo da Enugu da Ebonyi.
Jami’an INEC da masu sa ido sun ce babban dalilin giɓin shi ne mutane da dama na fara rijista ne amma ba sa samun damar kammala ɗaukar hoto da sauran bayanai.
Jami’in hulda da jama’a na INEC, Wilfred Ifogah, ya ce matsalolin aiki da kuma lokaci ma na hana mutane kammala rajista, sannan wasu da suka fara a ƙasashen waje ba su samu damar kammalawa bayan dawowa Najeriya ba.

Ministan Tsaro mai jiran rantsuwa, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa idan har ya fara aiki a matsayin ministan tsaro, dole ne a daina tattaunawa da kuma biyan kuɗin fansa ga ‘yan bindiga a Najeriya.
Janar Musa ya yi wannan bayani ne jiya yayin tantance shi a gaban Majalisar Dattawa, inda ya ce yaƙi da rashin tsaro ba zai inganta gaba ɗaya ba har sai an samar da cikakkiyar rumbun bayanan ƴan ƙasa tare da danganta su da tsaro da banki da tsarin tantance mutum.
Tantancewar janar Musa ta zo ne a rana ɗaya da Majalisar Wakilai ta nemi a tabbatar da gudanar da shari’o’in ta’addanci a fili domin rage yawaitar laifukan ta’addanci da tashin hankali a ƙasar.
Yayin jawabinsa, Janar Musa ya tsaya tsayin daka cewa gwamnatoci dole su guji duk wani nau’i na tattaunawa da masu aikata ta’addanci, domin hakan na ƙara musu ƙarfi ne kawai.