Nan muka kawo karshen shirin
Da fatan za ku tara a wani shirin na sharhi da bayanai kai tsaye a gasar cin kofin Afirka.
Sunana Mohammed Abdu nake ce muku asuba ta gari.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku bayanai kan wasan Najeriya da Tunisia a gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025 da ake yi a Moroko.
Mohammed Abdu
Da fatan za ku tara a wani shirin na sharhi da bayanai kai tsaye a gasar cin kofin Afirka.
Sunana Mohammed Abdu nake ce muku asuba ta gari.
Kyaftin ɗin Tunisiya ka bugowa ƙwallo ya sa kai amma ta yi faɗi - har yanzu Tunisiya sai kai matsi take gidan Najeriya.
Yanzu dai Super Eagles ta koma tare gida, domin ta tsira da wannan makin ukun da yake da mahimmaci a wajenta.
Lokaci ya cika na minti 90 an kuma yi karin minti bakwai daga nan a tashi wasan.
Ko Najeriya za ta kai zagaye na biyu kai tsaye da maki shida ko raaaba maki za ta yi da Tunisia? Sai a cikin karin lokacin nan za a tantance.
Mai tsaron bayan Tunisia, Abdi shi ne ya taɓe ya buga ƙwallon ta kuma faɗa ragar Najeriya, wanda ya buga ƙwallon da karfi don kada a samu matsala.
Ana zargin Osayi-Samuel ya taɓa ƙwallo da hannu, an kammala duba VAR an kuma bai wa Tunisiya bugun fenariti.
Moses Simon ya maye gurbin Frank Onyeka
Sannan kuma Chidera Ejuke ya cnaji Akor Adams.
Ɗan wasan Tunisiya, Ismaël Gharbi ya maye gurbin Elias Achouri.
Montassar Talbi na Tunisiya ne ya sa kai ta faɗa raga daga bugun da Hannibal Mejbri ya yi masa.
Ƙwallo aka bai wa Osimhen ya shiga da ita da'irar Tunisia daga nan ya bai wa Lookman shi kuma sai da ya tsaya ya kaɗa kafa daga baya ya buga da kafar hagu sai ta bugi jikin mai tsaron gida ta faɗa raga.
Tunisia ta saka Sebastian Tounekti ya maye gurbin Mohamed Ben Romdhane saboda raunin da ya ji.
An bai wa ɗan wasan tawagar Najeriya, Semi Ajayi katin gargadi, sakamakon ketar da ya yi wa Hannibal Mejbri, kuma ta yi muni kam
Kwana ce aka kwaso ta hannun Ademola Lookman ta wuce kowa ta je wajen ƙyaftin Wilfred Ndidi ya yi tsalle ya sa kai ta kuma faɗa raga.
Osimhen ya saka fuskar kariya ta roba da aka koma zagaye na biyu, bayan sun sha ruwa sun huta.