Dole ne Tinubu ya kawo ƙarshen zubar da jini a Zamfara - Amnesty

Asalin hoton, STATE HOUSE
Ƙungiyar kare hakkin bila'adama ta Amnesty International ta ce ya zama "wajibi" shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tabbatar an kawo ƙarshen kashe-kashen mutane da ke faruwa a jihar ta Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Amnesty ta faɗi hakan ne a wani martani da ta mayar bayan kisan da ƴan bindiga suka yi wa mutane aƙalla 38 da suke garkuwa da su kisan gilla a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda da ke jihar ta Zamfara.
Sanarwar da Amnesty ta fitar a shafinta na X, ta ce "babu wani yanki na Zamfara da ke cikin aminci tun daga shekarar 2018.
"A cikin shekara biyu da suka gabata an kashe sama da mutum 273 da yin garkuwa da mutane 467," in ji sanarwar.
"Hukumomin Najeriya na da nauyin da ya rataya a kansu bisa dokokin ƙasa da na duniya, na kare dukkanin al'umma ba tare da nuna bambanci ba," in ji sanarwar.
Zamfara na daga cikin jihohin Najeriya waɗanda suka shafe tsawon shekaru suna fama da matsalar ƴan fashin daji masu kisa da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
A lokuta daban-daban hukumomin Najeriya sun yi iƙirarin kashe manyan jagorori ƴan bindiga da ke jihar, sai dai kashe-kashen na baya-bayan nan na nuna cewa akwai sauran rina a kaba.
A tattaunawarsa da BBC, shugaban ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda, Manniru Haidara Ƙaura ya ce yawancin waɗanda aka kashen matasa ne.
"Bayanin da muka samu shi ne sun yi musu yankan rago ne. Abin da ya faru shi ne ƴanbindigar sun nemi kuɗin fansa kuma aka harhaɗa aka ba su kamar yadda suka nema, inda kuma suka saki mutum 18 da suka haɗa da mata 17 da ƙaramin yaro guda ɗaya, a ranar Asabar,"in ji Haidara.























