Rufewa
Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Mu zama lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke wakana a Najeriya da sassan duniya a ranar 27/12/2025.
Ahmad Tijjani Bawage
Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Mu zama lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Sojoji a Chadi sun yi Alla-wadai da harin jirgi mara matuki da dakarun RSF na Sudan suka kai wani gari da ke kan iyaka ranar Juma'a, wanda suka ce ya hallaka sojojin ƙasar biyu.
Shugaban sojojin ƙasar ya bayyana cewa harin da aka kai garin Al-Tina ya saɓa da dokokin ƙasa da ƙasa.
RSF dai sun shafe tsawon lokaci suna yaƙi mai tsanani da sojojin Sudan tun watan Afrilun, 2023.
Dakarun na RSF sun sanar da ƙwace wasu yankuna biyu da ke kusa da iyaka da Sudan, kusa da wurin da aka kai hari ranar Juma'a a Chadi.
Wani jami'in soji na ƙasar ta Chadi ya ce wannan ne hari na farko da RSF ta kai Chadi tun fara yaƙin Sudan.
Zuwa watan Mayu, Malisar Ɗinkin Duniya ta ce zuwa watan Mayu, sama da ƴan gudun hijirar Sudan miliyan ɗaya ne ke zaune a ƙasar Chadi.

Asalin hoton, Corbis/Getty Images
Shekara goma bayan da Jules Vernes ya wallafa shahararren littafinsa na 'A faɗin Duniya cikin kwana 80', wani matafiyi ɗan Ingila ya fita domin shi ma ya zagaya.
Sai dai, ba kamar tauraron da ke cikin littafin Vernes ba wanda ya yi tafiya da jirgin ƙasa, Thomas Stevens ya yanke shawarar zagaya duniya a kan keke.
Ya fara tafiyarsa ne a 1884 kuma ya shafe sama da shekara biyu. Bayan komawarsa gida, ya rubuta wani littafi mai suna 'Zagaya Faɗin Duniya da a kan Keke'.
Latsa nan don sanin abubuwan da Steven ya gani a hanyarsa....

Asalin hoton, Dikko Umaru Radda/Facebook
Gwamnan jihar Katsina kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa maso yamma, Malam Dikko Radda, ya nuna kaɗuwa da kuma takaici kan rasuwar masu ibada bakwai a wani harin ƙunar baƙin wake a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
An kai harin ne kan masallaci ranar Laraba lokacin da mutane ke tsaka da sallah.
Gwamna Radda ya kwatanta lamarin da cewa "rashin imani ne kuma abin Alla-wadai. An kai wa mutanen da ba su ji ba ba su gani yayin da suke sallah."
Wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar ranar Asabar, gwamnan ya ce lamarin ya jefa iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma al'ummomi cikin jimami.
Ya bayyana cewa masallatai da coci-coci da dukkan wuraren ibada wurare ne da ya kamata a kare saboda su ne wuraren zaman lafiya da kuma bauta.
Gwamnan ya ƙara da cewa duk wani tashin hankali irin wannan yana da ciwo kuma ba za a lamunta ba, inda ya ce lamarin ya sake nuna buƙatar haɗin-kai wajen yaƙi da ta'addanci a dukkan ɓangarori.
Ya yi kira ga ga jami'an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da kuma daƙile kai hare-hare irin wannan.
Daga karshe Radda ya miƙa ta'azziya ga gwamna Babagana Umara Zulum, al'ummar jihar Borno da kuma iyalan waɗanda suka rasu da waɗanda suka jikkata da kuma addu'ar Allah ya gafarta musu.

Asalin hoton, Reuters
Jami'ai a Ukraine sun ce hare-haren jirgi mara matuki da kuma makaman linzami da Rasha ta kai birninkyiv, sun yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum ɗaya da kuma jikkata gommai.
Dubun-dubatar mazauna birnin sun fuskanci ɗaukewar lantarki. JIragen yaƙin Poland mai makwabtaka sun yi ta shawagi a kan iyaka a matsayin martani ga hare-haren Rasha.
Shugaba Zelensky ya ce harin ya nuna cewa Moscow ba ta son a kawo karshen yaƙin.
Harin na zuwa ne kwana guda kafin ganawar mista Zelensky da shugaba Trump a Florida domin tattauna sabon yarjejeniyar tsagaita wuta da ake son cimmawa.
A wata tattaunawa da jaridar Politico, mista Trump ya ce tattaunawar za ta iya zama mai ma'ana amma Zelensky ba zai samu komai ba har sai Trump ɗin ya amince da abin da aka tattauna.

Asalin hoton, Nigerian Army/X
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar III ya yaba wa sojojin Najeriya bisa jajircewarsu wajen kare rayuka da kuma dukiyoyin ƴan Najeriya.
Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin hafsan sojojin ƙasa, Laftanar-Janar Waidi Shaibu a fadarsa da ke Sokoto ranar Juma'a, 26 ga Disamban, 2025.
Yayin ziyarar, Janar Shaibu ya ƙara tabbatar da zimmar sojojin ƙasar wajen ƙarfafa aiki da al'umma da kuma haɗin-kai da sarakuna don ganin an samar da zaman lafiya da tsaro.
Sultan Abubakar ya yi addu'ar Allah ya ci gaba da bai wa sojojin nasara a dukkan ayyukansu na kare ƴan ƙasa.

Asalin hoton, Nigerian Army/X

Hukumomi a Ghana sun ce sun kama sama da mutum 100 waɗanda ake zargi da aikata zamba ta intanet a safiyar yau Asabar, a wani samame da aka kai yankunan Tabora da Lashibi, da ke Accra.
An kai samamen da nufin kama ƙungiyoyin da ke aikata zambar intanet da sauransu, inda lamarin ya kai ga kama mutum 141, yawanci ƴan Nijeriya.
An kuma kama wani mutum ɗan asalin Ghana wanda ake zargi da bai wa mutanen da aka kama wurin zama.
Hukumomin ƙasar ta Ghana sun ce sun ƙwato kwamfutoci 38 da wayoyin salula 150 waɗanda ake amfani da su wajen aikatar zambar ta intanet.
A wani sako da ya wallafa a shafin X, ministan sadarwa, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma fasaha na ƙasar, Sam George, ya ce ana zargin mutanen da aikata laifukan zamba daban-daban.
"Muna ci gaba da binciken wayoyin da muka ƙwace, kuma duk wanda aka samu da laifi za a hukunta shi bisa tsarin dokokin Ghana," in ji Sam.
Samamen ya biyo ne bayan kama wasu mutum 48 ranar Laraba, abin da ke ƙara nuna zimmar da ƙasar ke yi wajen daƙile ayyukan masu zambar intanet.
Wani rahoto kan laifukan zamba na 2025 da hukumar ƴansandan ƙasa da ƙasa na Interpol suka fitar, ya nuna cewa ayyukan masu zambar na ƙara girma a nahiyar Afirka.
A baya-bayan nan ma, Ghana ta watsar da wasu gungun masu zamba da suka damfari mutum sama da 200 kuɗi da ya kai dala biliyan 400,000 - kuma suna aiki ne tsakanin Ghana da Nijeriya.

Somaliya ta mayar da martani a fusace bayan da Isra'ila ta zama ƙasa ta farko a duniya da ta amince da Somaliland a hukumance a matsayin ƙasa ƴantacciya.
Firaiminista Hamza Abdi Barre, ya ce Somalia ta yi watsi da abin da ya ce hari da gangan da Isra'ila ta kai a kan yancin ƙasarsu.
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce gwamnatinsa ta amince za ta faɗaɗa danganta da haɗin kai da Somaliland ɗin a ɓangaren noma da lafiya da kuma fasaha.
Tuni dai shugaban Somaliland Abdirahman Mohammed Abdullahi, ya yaba da wannan ci gaba inda ya bayyana shi a matsayin tarihin da ƙasarsa ba za ta taɓa mantawa da shi ba.
Ƙungiyar tarayyar Afirka dai ta yi watsi da duk wani yunkuri na amincewa da yankin Somaliland ɗin a matsayin kasa mai 'yanci inda shugaban ƙungiyar ya yi gargaɗin cewa irin wanann mataki da Isra'ilan ta ɗauka zai iya kawo illa ga zaman lafiyar nahiyar.

Asalin hoton, Bola Tinubu/Facebook
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa sabbin hanyoyi da ake ɗauka don magance matsalar tsaron ƙasar, za su samar da nasara nan ba da jimawa ba.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin karɓar bakuncin Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), karkashin jagorancin shugabanta Archbishop Daniel Okoh, a gidansa da ke Legas ranar Juma'a, kamar yadda sanarwar da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai Bayo Oyanuga ya fitar ta bayyana.
Tinubu ya bayyana cewa a shirye gwamnatinsa take wajen kirkiro da ƴansandan jihohi domin inganta tsarin tsaron ƙasar.
Ya yi kira ga CAN da ta yi aiki da gwamnatinsa domin cimma manufofin da ƙasar ke son cimmawa, inda ya ce wasu matakai da gwamnatinsa ta ɗauka na buƙatar lokaci kafin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Asalin hoton, Bayo Onanuga
"Ƙasa na buƙatar zaman lafiya, duk da cewa wuraren da muke mulka na da faɗi. Babban kalubale ne, amma za mu yi nasara. Mun riƙe addini. Muna addu'o'i. Muna buƙatar haɗin-kai a wajenku.
"Ƴansandan al'umma da kuma na jihohi zai samu da zarar majalisar tarayya ta kammala yin duba a kan batun.
"Jiragen kai hare-hare guda huɗu da muke son saya daga Amurka za su ɗauki lokaci kafin su iso. Mun tinkari Turkiyyya ma domin neman taimako," in ji Tinubu.
Shugaban Najeriyar ya ce tsaiko da ake samu na shafar yadda al'umma ke kallon ƙoƙarin gwamnatinsa wajen shawo kan matsalolin tsaro.
Ya ce gwamnati na aiki tukuru don ganin ta mayar da zaman lafiya a ƙasar, duk da irin hare-haren sari ka-noke da ƴanbindiga da kuma ƴan ta da ƙayar-baya ke yi.

Asalin hoton, Reuters
Thailand da Cambodia sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta domin kawo karshen faɗan da ake yi a kan iyaka wanda ya sake ɓarkewa makonni uku da suka gabata.
Yarjejeniyar wadda ministocin tsaron ƙasashen biyu suka sanyawa hannu za ta fara aiki ne nan ta ke.
A karkashin yarjejeniyar, dukkan ɓangarorin biyu sun amince da ƙara tura sojoji iyakokinsu amma ba za a kai wa juna hari ba.
Sannan fararen hular da ke zaune a yankunan iyakar za su koma gidajensu.
Haka kuma za a mayar da sojojin Cambodia 18 ƙasarsu idan yarjejeniyar ta kai sa'oi 72 da fara aiki.
An dai kashe mutane da dama sannan wasu kusan miliyan guda sun bar muhallansu a rikicin baya bayan-nan.

Asalin hoton, Dare Akogun
Jami'an sashen tattara bayanan sirri na rundunar ƴansandan Najeriya, ta ce ta kama wasu riƙakkun ƴan bindiga biyu waɗanda ake zargi da kai munanan hare-hare a jihohin Katsina, Zamfara, Neja da kuma Kwara.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin ya fitar ranar Juma'a, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan wani samame da suka kai jihar Kwara.
A cewar sanarwar, an ga ɗaya daga cikin ƴan bindigar mai suna Abubakar Usman wanda aka fi sani da Siddi, yana wasa da maƙudan kuɗaɗe da kuma riƙe da makamai a wani bidiyo. Ɗayan kuma an bayyana sunansa da Shehu Muhammadu wanda aka sani da Gide.
Kakakin ƴansandan ya ce jami'an sun ƙwato sabon babur guda ɗaya ƙirar Honda Ace 125 jar kala wanda aka kiyasta kudinsa ya kai naira miliyan 1,850,000, bindigar AK-47 da tarin harsasai da kuma zunzurutun kuɗi da ya kai naira 500,000.
"Bincike da muka fara gudanarwa ya nuna cewa waɗanda ake zargin mambobin wata gawurtacciyar ƙungiyar ƴanbindiga ce da ta ƙware wajen garkuwa da mutane a faɗin jihohin Zamfara da Katsina da Neja da kuma Kwara,"in ji sanarwar.
"Sun kuma kasance waɗanda ke samar da makamai da harsasai ga ɓata-gari.
"Dukkan waɗanda ake zargin na ci gaba da bayar da haɗin-kai ga bincike don ganin an kai ga kama sauran mambobi da suke aikata ta'asar tare.
Mai magana da yawun ƴansandan ya buƙaci al'umma su riƙa bai wa jami'an tsaro bayanai da suka kamata a kan lokaci domin ganin an kawo karshen ayyukan ƴanbindigar.

Asalin hoton, Usman Binji
Ana ci gaba da tafka muhawara kan hare-haren da gwamnatin Amurka ta sanar da ƙaddamarwa a wasu sassan Najeriya.
A daren Alhamis ne Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa sojojin ƙasarsa sun kai wani harin da ya kira mummuna a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Haka kuma da safiyar Juma'a sai aka samu labarin wani harin a garin Offa da ke ƙaramar hukumar Offa ta jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, inda aka ga kwankon bam.
Latsa nan don karanta cikakken labarin....

Asalin hoton, EPA/Shutterstock
Shugaba Trump ya ce ya yi amanna cewa zai yi ganawa mai ma'ana da shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine, a ganawar da za su yi a gobe Lahadi domin tattaunawa kan kokarin da ake yi wajen kawo karshen yakin da Ukraine ɗin ke yi da Rasha.
Amma a game da fatan da ya ke da shi akan sabon kunshin yarjejeniyar da aka gabatarwa mista Zelensky, Trump ya shaida wa kafar yaɗa labaran Amurka ta the Website Politico, cewa babu abin da zai ce har sai ya ga an amince da ita.
Kazalika ya ce yana fatan tattaunawa da shugaban Rasha Vladimir Putin nan ba da jimawa ba.
Masu bibiyar mu barkan mu da warhaka.
Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a wannan rana ta Asabar.
Ku kasance da mu domin samun labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.
Ahmad Bawage ne zai jagoranci kawo muku labaran!