Neymar zai ci gaba da taka leda a Santos

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku dukkan abubuwan dake wakana a fannin wasanni a faɗin duniya daga Asabar 21 zuwa Juma'a 28 ga watan Yunin 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Abdulrazzaq Kumo

  1. Coleman ya tsawaita zamansa a Everton

    Seamus Coleman

    Asalin hoton, PA Media

    Everton ta sanar cewa kyaftin ɗinta Seamus Coleman ya tsawaita zamansa a ƙungiyar da shekara ɗaya, abin da zai sa ya kai shekara 17 kenan a kulob ɗin.

    Ɗanwasan mai shekara 36 ya buga mata wasa 428 a duka gasanni, kuma wasa 369 da ya buga a gasar Premier League shi ne mafi yawa a tariihin Everton.

    "Ina ƙaunar Everton, saboda haka ci gaba da taka mata leda na da muhimmanci sosai a wajena da iyalina," in ji ɗan ƙasar Ireland ɗin mai kare baya.

    "Kamar kowane magoyin bayanmu, na rayu cikin lokaci mafi rashin kyawu a 'yan shekarun nan kuma na yi bakin ƙoƙarina wajen ganin na taiamaka mun fita daga halin da ƙungiyar ta shiga."

  2. Jadawalin zagayen 'yan 16 na Club World Cup

    Club World Cup

    Asalin hoton, EPA

    Daga yau Juma'a ne ake kammala wasannin cikin rukuni na gasar kofin duniya ta Club World Cup, inda tuni aka samu tawagogi 16 da za su tsallaka zagaye na biyu.

    A gobe Asabar ne kuma za a fara buga wasannin zagaye na biyun, inda Banfica za ta kara da Chelsea da wanda Palmeiras za ta buga da Botafogo RJ.

    Ga yadda jadawalin wasannin zai kasance:

    • 28 ga Yuni: Palmeiras v Botafogo
    • 28 ga Yuni: Benfica v Chelsea
    • 29 ga Yuni: PSG v Inter Miami
    • 29 ga Yuni: Flamengo v Bayern Munich
    • 30 ga Yuni: Inter Milan v Fluminense
    • 1 ga Yuli: Manchester City v Al-Hilal
    • 1 ga Yuli: Real Madrid v Juventus
    • 2 ga Yuli: Borussia Dortmund v Monterrey

    Hoton ƙasa yana nuna hanyar da za a bi har zuwa wasan ƙarshe:

    Jadawalin Club World Cup

    Asalin hoton, BBC Sport

    Bayanan hoto, Hoton sama yana nuna hanyar da za a bi har zuwa wasan ƙarshe:
  3. Real Madrid za ta kara da Juventus a Club World Cup

    Real Madrid

    Asalin hoton, EPA

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid za ta fafata da Juventus a zagayen 'yan 16 na gasar kofin duniya ta Club World Cup bayan dukkansu sun yi nasarar tsallakawa.

    Real ta fito ne daga Rukunin H a saman teburin da maki 7 cikin wasa uku, yayin da Juventus ta kammala wasannin Rukunin G a mataki na biyu da maki shida - Manchester City ce ta jagoranci rukunin da maki tara.

    Za su fafata ne ranar Talata a filin wasa na Miami Gardens da ke jihar California ta Amurka da ƙarfe 8:00 na dare agogon Najeriya da Nijar.

    Amma Manchester City ce za ta gwabzawa da Al Ahli da ƙarfe 2:00 na daren ranar.

    Juventus

    Asalin hoton, EPA

  4. Brentford ta naɗa Keith Andrews kocinta

    Keith Andrews

    Asalin hoton, Getty Images

    Brentford ta naɗa Keith Andrews a matsayin sabon kocinta kan yarjejeniyar shekara uku bayan Thomas Frank ya koma Tottenham.

    Andrews mai shekara 44 ya koma Brentford ne tun a farkon kakar bara domin yin aiki tare da Frank a matsayin mai horar da bugun tazara da kwana.

    Ya yi aiki cikin masu horar da Sheffield United, da MK Dons, da kuma tawagar ƙasar Ireland amma wannan ne karon farko da zai zama babban koci.

    Brentford ta duba wasu kociyoyin da dama amma sai ta zaɓi ta bai wa wanda ta sani domin ɗorawa kan aikin da Frank ya faro.

    Ƙungiyar ta ƙare ne a mataki na 10 a teburin gasar Premier League ta 2024-25 da aka kammala.

  5. Real Madrid ta kai zagayen 'yan 16 a gasar Club World Cup

    Real Madrid

    Asalin hoton, EPA

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta kai zagayen gaba a gasar kofin duniya ta Club World Cup bayan doke Salzburg ta ƙasar Jamus 3-0.

    Vinicius Jr ne ya fara ci mata ƙwallo a minti na 40 da fara wasan a wasan da aka buga a birnin Pennsylvenia, kafin Velverde ya jjefa ta biyu minti bakwai bayan haka.

    Saura minti shida a kammala wasan Gonzalo Garcia ya ƙara ta uku, abin da ya bai wa Madrid tashi ba tare da an zira mata ƙwallo ba.

    Real ta kammala wasannin rukunin na H a saman teburi da maki 7 bayan yin canjaras ɗaya da nasara biyu.

    Al Ahli ta Saudiyya ce ta biyu da maki 5, wadda ta bi sawun Real ɗin zuwa zagayen sili ɗaya ƙwala. Sai Salzburg ta uku da maki 4, da kuma Pachuca ta ƙasar Mexico maras maki.

  6. Burnley ta ɗauki Tuanzebe daga Ipswich

    Tuanzebe

    Asalin hoton, Burnley FC

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Burnley ta ɗauki ɗanwasan baya Axel Tuanzebe a kyauta bayan kwantaraginsa ya ƙare a Ipswich Town.

    Tuanzebe ya buga wa Ipswich wasa 45 a duka gasanni, inda ya taimaka musu wajen samun damar komawa gasar Premier League ta Ingila a kakar 2023-24.

    Ɗanwasan mai shekara 27 ya buga wasa 22 a kakar Premier da ta gabata, kuma ya zaɓi ya ci gaba da zama a gasar tare da Burnley wadda ta hauro gasar a kakar bana.

  7. Leicester City ta sallami Van Nistelrooy daga horas da ƴanwasanta

    Van

    Asalin hoton, Getty Images

    A ƙarshe dai ƙungiyar Leicester City ta raba gari da kocinta Ruud van Nistelrooy, kimanin mako shida bayan ƙungiyar ta faɗa rukuni na biyu na gasar Ingila.

    Kocin mai shekara 48 ya jagoranci ƙungiyar a wasa guda 27, inda a ciki aka doke su a 19, ta samu nasara biyar a kakar bara da ya horas da ƴanwasanta.

    Leicester ta yi ban-kwana da premier league ne tun ana sauran wasa biyar a kammala gasar, amma duk da haka ƙungiyar bar tsohon ɗanwasan gaban na Man United ɗin ya kai har ƙarshen kakar.

    Ƙungiyar ta ce ta rabu da Van Nistelrooy ne bayan tattaunawat "fahimtar juna", domin fara shirin fuskantar abin da ke gabansu.

    Sai dai ƙungiyar na fuskantar ƙalubale babba, kasancewar duk da cewa ta faɗa ƙaramar gasar, yanzu haka tana fuskantar ƙalubalen cire maki a kaka mai zuwa bayan hukumar ƙwallon ƙafar Ingila ta zarge ta saɓa dokokinta a kakar bara.

    A sanarwar sallamar kocin, ƙungiyar ta ce tana yi masa fatan alheri, sannan shi ma ya rubuta cewa yana musu fatan alheri.

    Ya ce, "ina godiya ga ƴanwasan Leicester da sauran masu horaswa da ma'aikata da duk wani mai alaƙa da ƙungiyar."

  8. Ronaldo zai ci gaba da taka leda a Al Nassr

    Cristiano Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Ronaldo ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwatiraginsa da shekara biyu a ƙungiyar Al Nassr, kuma hakan na nufin zai ci gaba da zama a ƙungiyar har 2027, lokacin da zai kai shekara 42 a duniya.

    Ɗan wasan mai shekara 40 ya je Al Nassr ne a Disamban 2022 bayan matsalar da ya samu da Manchester United.

    A ƙarshen watan Yunin da muke ciki ne kwantiraginsa na farko zai ƙare a ƙungiyar da ke Saudiyya.

    Bayan sanya hannun ɗan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or har sau biyar ya ce "An buɗe sabon babin buri da sha'awar ci gaba da kafa tarihi tare" a shafinsa na X.

  9. Lewis-skelly ya tsawaita yarjejeniyarsa da Arsenal

    Myles Lewis-Skelly

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Ingila Myles Lewis-Skelly ya ce yana so ya kafa tarihi a Arsenal bayan ya tsawaita zamansa a ƙungiyar - wadda yake gogyon baya tun yana yaro - da shekara biyar.

    "Ina so na ci ko wane kofi a ƙwallon ƙafa, kuma ina son kasancewa mutum mai tarbiyya da son koyon abubuwa." in ji ɗan wasan.

    A kakar wasan da ta gabata ne Arteta ya fara amfani da Lewis-skelly a wasa inda ya buga wasanni 39.

    Kafin ya sa hannu a yarjejeniyar, kwantiraginsa za ta ƙare ne a shekarar 2026.

    A watan Maris Lewis-Skelly ya zama ɗan wasa mafi ƙarancin shekaru da ya ci wa tawagar Ingila ƙwallo a tarihi bayan ya zura ƙwallo a karawar tawagar Ingila da ta Albania.

    Zuwa yanzu ya buga wa Ingila wasa uku.

  10. Inter ta doke Riverplate a wasan da aka kusan yin dambe

    Denzel Dumfries da Marcus Acuna

    Asalin hoton, Getty Images

    Inter Milan ta kai zagayen ƴan 16 a gasar Club World Cup bayan doke River Plate ta Argentina da ta fita daga gasar.

    Francesco Esposito da Alessandro Bastoni ne suka zura ƙwallo yayin da Inter ɗin ta doke Riverplate wadda ta kammala karawar da ƴan wasa 9 bayan samun jan kati biyu.

    Sai dai rikici tsakanin ƴan wasa ne ya fi ɗaukar hankalin mutane bayan da Marcus Acuna ya so ya kai wa Denzel Dumfries hari yayin da yake shirin fita daga filin.

    Lamarin ya yi tsanani har sai da kocin Inter Milan Christian Chivu da wasu ƴan wasa suka hana rikicin kaurewa.

    Magoya bayan River Plate sun riƙa jifan Dumfries da abubuwa a wasan.

  11. Liverpool ta ɗauki Milos Kerkez kan fam miliyan 40

    Milos Kerkez

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool ta tabbatar da sayen ɗan wasan ƙasar Hungary mai shekara 21, Milos Kerkez daga ƙungiyar Bornemouth, bayan ya sa hannu kan yarjejeniyar shekara biyar a Anfield.

    Kerkez ne ɗan wasa na uku da Liverpool ta saya tun da aka buɗe wannan damar ta sayen ƴanwasa, bayan da ta ɗauki Jeremie Frimpong da Florian Wirtz a baya-bayan nan.

    Kerkez ya buga dukkan wasannin Bornemouth a gasar Firimiya a kakar wasa da aka kammala, kuma ya taka rawar gani yayin da ƙungiyar ta tara maki 56 - mafi yawa da ta taɓa samu a tarihinta.

    Sayen Kerkez da Liverpool ta yi ya sa wasu masana ke ganin cewa lokacin Andy Robertson a ƙungiyar ya zo ƙarshe kasancewar wuri ɗaya suke bugawa.

  12. Neymar zai ci gaba da taka leda a Santos

    Neymar

    Asalin hoton, Santos

    Wanda yake kan gaba a yawan ci wa Brazil ƙwallaye a tarihi, Neymar ya sabunta yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Santos, kungiyar da ya fara tamaula tun yana matashi.

    Mai shekara 33 ya sake komawa buga gasar tamaula ta Brazil kan kwantiragin wata shida a Janairu, bayan da Al-Hilla ta soke yarjejeniyar da take tsakaninsu.

    Neymar ya ci ƙwallo 141 ya bayar da 69 aka zura a raga a wasa 243 a Santos har da ukun da ya ci a wasa 14, bayan da ya sake komawa ƙungiyar.

    Tun farko an yi ta alakanta tsohon ɗan wasan Barcelona da Paris St Germain da cewar zai koma Turai da taka leda, sai aka ji ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da buga gasar tamaula ta Brazil da cewar za a iya tsawaita masa ita da zarar ya yi abin kirki.

  13. Wasannin Club World Cup ranar Alhamis

    Club World Cup

    Asalin hoton, Getty Images

    FIFA Club World Cup rukuni na biyar

    • Inter Milan da River Plate a filin wasa na Lumen Field
    • Urawa Red Diamonds da Monterrey a filin wasa na Rose Bowl Pasadena

    FIFA Club World Cup rukuni na bakwai

    • Juventus da Man City a filin wasa na Camping World
    • Wydad Casablanca da Al Ain a filin wasa na Audi Field
  14. Rashford

    Asalin hoton, Getty Images

    Barcelona na tunanin ɗaukar aron ɗan wasan gaban Manchester United ɗan ƙasar Ingila Marcus Rashford mai shekara 27. (Guardian)

    Ɗan wasan Liverpool da Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 25, ya fi bayar da fifiko kan komawa Napoli idan har ya bar Anfield a bazarar nan. ( Football Italia)

    Nottingham Forest ta yi watsi da tayin da Newcastle ta yi mata na kusan fam miliyan 45 kan ɗan wasan Sweden Anthony Elanga, mai shekara 23, wanda ta ƙaƙaba masa farashin Fam miliyan 60. (Sky Sports)

    Chelsea na fatan gaggauta kammala cinikin ɗan wasan gaban Borussia Dortmund ɗan ƙasar Ingila Jamie Gittens, yayin da Bayern Munich ma ke zawarcin ɗan wasan mai shekara 20. (The Athletic)

  15. Arsenal tana son ɗaukar Norgaard madadin Partey

    Norgaard

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal na fatan sayen ɗan ƙwallon Brentford, Christian Norgaard, domin maye gurbin Thomas Partey.

    Wasu majiya na cewar kuɗin da Arsenal za ta ɗauki ɗan wasan tawagar Denmark mai shekara 31, zai kai £10m da karin £5m idan ya taka rawar gani daga karin tsarabe-tsarabe.

    Arsenal ta daɗe tana zawarcin Norgaard, wanda tanzu take fatan zai maye gurbin ɗan kasar Ghana, mai shekara 32, wanda bai amince da ƙunshin yarjejeniyar da Arsenal ta gabatar masa, domin ya ci gaba da taka mata leda.

    Yarjejeniyar Partey za ta cika a mako mai zuwa, idan kuma ba a kai ga cimma kwantiragi ba, zai bar Gunners..

    Norgaard, wanda yake da sauran yarjejeniya da Brentford zuwa 2027 ya koma ƙungiyar a 2019 daga nan ya zama kashin baya a karkashin Thomas Frank, wanda ya koma horar da Tottenham.

  16. Lallana ya yi ritaya daga taka leda

    Adam Lallana

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon ɗan wasan tawagar Ingila, Adam Lallana ya yi ritaya daga taka leda yana da shekara 37 da haihuwa.

    Lallana ya buga wa Ingila wasa 34, ya sake komawa Southampton a kakar da ta wuce, kungiyar da ya fara da yin suna a fannin tamaula.

    Sai dai wasa biyar ya buga a ƙungiyar da ta bar Premier League ta yi kasa zuwa Championship, sai dai ya yi aiki a matakin koci, abin da zai yi kenan domin taimakawa Will Still.

    Lallana ya je Liverpool daga Southampton kan £25m a 2014, wanda ya lashe kofin Premier League da na Champions League a ƙungiyar Anfield.

  17. Ƙudin da Chelsea za ta samu a Club World Cup

    Kamar yadda Fifa ta ce Club World ita ce gasa mai ɗan karen tsoka da ƙungiya za take samun makudan kudade.

    Chelsea ta samu $38m (£28m) kuɗin samun damar shiga gasar.

    Ƙungiyar ta Stamford Bridge kan karɓi $2m da zarar ta ci wasa ɗaya a cikin rukuni, kuma ta doke LAFC da ES Tunis.

    Za kuma ta samu $7.5m a wasan zagaye na biyu da za ta kara da Benfica, jimilla ƙungiyar Stamford Bridge za ta karɓi.$49.5m.

    Chelsea za ta karɓi $13.1m da zarar ta kai kwata fainal da kuma $21m idan ta kai daf da karshe da samun $30m zuwa zagayen karshe. Duk wadda ta lashe kofin za ta samu $40m.

  18. Forest ta ki sallama tayin da Newcastle ta yi wa Elanga, Sky Sports

    Elanga

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamar yadda Sky Sports ta wallafa, ɗan wasan Nottingham Forest, Anthony Elanga ya ki tayin komawa Newcastle da taka leda.

    Cinikin zai kai £45m, amma Forest ta ce Elanga ya kai £60m.

    Elanga ya koma Nottingham Forest daga Manchester United a 2023.

  19. An bai wa Southagte lambar girmamawa ta Sir

    Southgate

    Asalin hoton, Getty Images

    An karrama Gareth Southgate da lambar girmamawa ta Sir a wani kasaitatcen biki da aka a yau Laraba.

    Tsohon kociyan tawagar Ingila ya kai kasar wasan karshe biyu a jere a Euro 2020 a Ingila da kuma 2024 a Jamus da zuwa daf da karshe a gasar kofin duniya a Rasha a 2018.

    Yariman Wales ne ya karrama Sir Southagate a katafaren bikin da aka yi a Windsor Castle.

    Ya zama na hudu mai horar da tamaula dan Ingila da aka karrama da lambar girmamawar bayan Sir Walter Winterbottom da Sir Alf Ramsey da Sir Bobby Robson.

    Thomas Tucel ne ya maye gurbin Sir Southagate, wanda zai kai Ingila gasar kofin duniya a badi a Amurka da Canada da Mexico – lokacin zai cika shekara 60 rabon da Ingila ta lashe wani babban kofi a fannin tamaula a duniya.

  20. Pogba zai saka hannu kan kwantiragi a Monaco

    Pogba

    Asalin hoton, Getty Images

    Paul Pogba na daf da komawa Monaco a cikin makon nan, yana fatan zai ci gaba da taka leda bayan dakatar da shi da aka yi kan zargin shan abubuwan kara kuzarin wasa.

    Wasu rahotannin na cewar an kusan cimma yarjejeniya, ana sa ran Pogba zai je Faransa daga gidansa na Amurka domin sa hannu kan kunshin yarjejeniya.