Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/11/25

Wannan shafi ne da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/11/25

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi da Aisha Aliyu Jaafar da Abdullahi Bello Diginza

  1. Gwamnatin Najeriya ta rufe kwalejojin tarayya saboda matsalar tsaro

    Gwamnatin Najeriya ta sanar da umarnin rufe makarantunta na sakandare na kwalejojin tarayya da ake kira da Unity Colleges.

    A wata sanarwa da ma'aikatar ilimi ta fitar a ranar Juma'a wadda daraktan makarantun sakandare, Binta Abdulqadir ta sanya wa hannu a madadin ministan ilimi Tunji Alausa, gwamnatin ƙasar ta sanar a rufe kwalejojin guda 47 a faɗin Najeriya.

    Sanarwar ta ce ma'aikatar ta ɗauki wannan matakin ne "saboda barazanar tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar, da kuma yunƙurin daƙile aukuwa wata matsala," kamar yadda sanarwar ta nuna.

    Sanarwar ta kuma umarci shugabannin makarantun su tabbatar an aiwatar da umarnin.

  2. Ya kamata a ayyana dokar ta ɓaci kan matsalar tsaro a Najeriya - Atiku

    Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya Atiku Abubakar ya ce har yanzu lokaci bai ƙure ba na ayyana dokar ta ɓaci kan matsalolin tsaro da suka dabaibaye ƙasar.

    Atiku ya bayyana haka ne a martanin da ya yi kan harin da aka kai a wata makarantar kiristoci a jihar Neja, inda aka yi garkuwa da wasu ɗalibai.

    A rubutun da ya yi a kafofin sadarwa, Atiku ya ce, "wannan abin takaici ne. Mutane nawa za a ƙara rasawa kafin a ɗauki matakin mai ƙarfi da ya dace? ina ganin har yanzu lokaci bai ƙure ba kan ayyana dokar ta ɓaci kan matsalar tsaro domin magance matsalar."

  3. Muna tsaka mai wuya kan yarjejeniyar tsagaita wuta - Zelensky

    Shugaban Ukraine Zelensky ya ce ƙasarsa na fuskantar ƙalubale mafi girma a tarihinta, inda ya ce suna da zaɓi biyu masu girma ne a gabansu.

    Ya ce yanzu suna cikin ƙalubalen ko dai su rasa ƙawarsu wato Amurka ko kuma su rasa mutuncinsu.

    Sai dai a wani jawabi da ya yi ga ƴan ƙasar, ya ce shi dai ba zai yi watsi da buƙatu da muradun ƴanƙasarsa ba, inda ya ce duk da cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wutar, zai fifita buƙatun ƴan ƙasarsa sama da komai.

    Rahotanni na cewa daga cikin abubuwan da ke cikin daftarin yarjejeniyar akwai dakatar da yunƙurin Ukraine na shiga Nato, da kuma amincewar Ukraine na rasa wasu yankunanta da Rasha ta ƙwace.

    Gwamnatin Amurka ta yi barazanar janyewa da taimaka wa Ukraine idan har shugabanta bai amince da daftarin ba.

  4. Ribadu ya gana da sakataren yaƙi na Amurka

    Sakataren yaƙin Amurka Pete Hegseth ya sanar da cewa ya samu ganawa da mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu.

    Hegseth ya ce sun gana da Ribadu ne a game da batun zargin yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya, inda ya ce za u ci gaba da tattaunawa domin kawo ƙarshen matsalar.

    Ya ce a ƙarƙashin mulkin Shugaban Amurka Donald Trump, sashen yaƙi na Amurka za ta yi aiki da Najeriya domin kawo ƙarshen kisan gilla da ya ce mayaƙa masu iƙirarin jihadi suke yi wa kiristoci.

  5. Ba a sace ɗalibai a Nasarawa ba - Ƴansanda

    Rundunar ƴansandan jihar Nasarawa ta ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa cewa an sace wasu ɗalibai biyu a makarantar St. Peter’s Academy da ke yankin Rukubi na jihar.

    A wata sanarwa da kakakin rundunar ya fitar a ranar Juma'a, kakakin rundunar Ramhan Nansel wanda ya yi magana a madadin kwamishinan ƴansandan jihar Shetima Mohammed, ya ce labarin ƙanzon kurege na.

    Sanarwar ta ce duk labaran da ake yaɗawa cewa mahara sun kutsa makarantar da ke ƙaramar hukumar Doma, "shaci-faɗi ne kawai aka ƙirƙira."

    "Abin da ya faru shi ne wasu ɗaliban makarantar ne suka hango mafarauta suna wucewa ɗauke da bindigar farauta, sai suka ji tsoro suka saboda suna tunanin ƴanbindiga ne sai suka tsere," in ji shi kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

  6. Shugaban Nijar ya yi rangadin mako biyu a sassan ƙasar

    Shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya koma Yamai bayan kwashe sama da makonni 2 yana rangadi a lunguna da sakunan ƙasar inda ya gana da al’umma tare da sauraron bukatu da matsalolinsu.

    Yayin ziyarar shugaba Tchiani ya gana da wakilan al'umma na bangarori daban-daban tare da gudanar da taruka na musaman kan al'ammuran tsaron da kasar ke fuskanta.

    Sai dai masana lamuran mulki irinsu Alhaji Doudou Rahama na ganin bayan wannan rangadi abunda ya rage shine shugaban ya zauna yayi nazarin bukatun al'umma kasar domin nema masu mafita.

    Ya ce wajibi ne ya cika alkawuran da ya ɗauka gwargadon iyawarsa, musamman fannin tattalin arziki da ke cikin mawyuacin hali.

    Masanin ya kuma ce ƙoƙarin da shugaban ya yi na cika alƙawuran zai tabbatarwa ƴan ƙasar zai iya kai su tudun mun tsira.

    Al'umma da dama ne dai suka rinka fitowa kwansu da ƙwarƙwatarsu, domin gana wa da shugaban a yayin ziyarar shugaban.

  7. An kai hare-hare 49 kan makarantun arewa maso yammacin Najeriya a shekaru 8- Save the children

    Ƙungiyar agaji ta Save the Children ta yi Allah wadai da sace ɗalibai mata 23 da wasu ƴanbindiga suka yi a wata makarantar kwana da ke garin Maga a jihar Kebbi, inda ta yi kiran ɗaukar matakan da suka dace wajen kuɓutar da su da tsare makarantun ƙasar.

    A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, kamar yadda jarida Punch ta ruwaito, ta bayyana harin a matsayin mai muni da ke ƙara nuna yadda matsalar tsaro ke taɓarɓarewa a arewacin Najeriya, inda hari kan makarantu ke kawo tsaiko ga karatun yara.

    ''Dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya kan ƴancin yara da dokar kare ƴancin yara ta Najeriya sun bayyana ilimi a matsayin haƙƙi ne da ya wajaba ba alfarma ba. Dukkanmu na da alhakin tabbatar da wannan,'' a cewar sanarwar.

    Ƙungiyar save the children ɗin ta buƙaci gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Kebbi su yi gaggawar tabbatar da sakin yaran da kuma hukunta masu laifin.

    A cikin wani rahoton ta, ƙungiyar ta ce tsakanin watan Fabrairun 2014 da Disanbar 2022, aƙalla hare-hare 70 aka kai makarantu a faɗin ƙasar, inda 49 daga cikinsu a arewa maso yamma ne.

    ''Waɗannan hare-hare sun kai ga sace ɗaliban 1,683, da kashe ɗalibai 184, da kuma lalata gine-gine 25,'' a cewar rahoton.

  8. Matawalle ya isa Birnin Kebbi bisa umurnin Tinubu

    Ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Mohammed Bello Matawalle ya isa tashar jirgin sama ta Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, domin taimaka wa da sa ido kan yunƙurin ceton ɗaliban da aka sace a jihar ta Kebbi.

    A ranar alhamis ne Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya umarce shi ya koma jihar - da ke arewa maso yammacin Najeriya - har sai an dawo da ɗaliban gida.

    A farkon wannan mako ne wasu ƴanbindiga riƙe da muggan makamai suka shiga makarantar Sakandiren ƴanmata da ke garin Maga a yankin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar tare da sace ɗalibai 25.

  9. NDLEA ta kama mutum fiye da ɗari biyu da ake zargi da ta'ammuli da ƙwayoyi a Kano

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya a jihar Kano ta ce ta kama aƙalla mutum ɗari biyu da talatin da ake zargi da laifukan da ke da alaƙa da ƙwayoyi, tare da ƙwace muggan ƙwayoyi masu tarin yawa.

    Shugaban hukumar a Kano, Abubakar Ahmed ne ya sanar da ci gaban a yayin wata ganawa da yayi da ƴan jarida a jihar.

    Ya ce hukumar ta sami wannan nasarar ce a yaƙin da take yi da ta'ammuli da ƙwayoyi a wani zazzafar aikin kame da ta yi na kwanaki 30 a faɗin jihar ta Kano.

    Ya ce sun gudanar da aikin kamen ne tare da haɗin gwiwar ƴan sandan ƙasar, da hukumar tsaro ta civil defence, da hukumar kula da shige da fice, da jami'an tsaron farin kaya (DSS) ƙarƙashin wata rundunar haɗin gwiwa ta dawo da zaman lafiya da gyara halayyar matasa.

    A cewar sa, sun shafe tsawon wata guda suna kai samame a sannanun matattarar masu ta'ammuli da miyagun ƙwayoyi da ke Kofar Ruwa da Tashar Rami da Rijiyar Lemo da Kurna da Zage da Dorayi Karshen Waya da Dawanau da Filin Idi da Rimi Market da Zango da Kano Line da Kofar Mata da wasu wuraren.

    Shugaban hukumar ya kuma ce tuni kamen da suka yi ya kawo sauƙin aikata wasu laifuka kamar ƙwacen waya da dabanci da wasu laifukan.

  10. Za mu ceto ɗaliban da aka sace cikin ƙoshin lafiya - ƴan sandan Neja

    Rundunar ƴansandan jihar Neja ta ce tuni ta aika jami'ai yankin da aka sace wasu ɗalibai da ba a san adadin su ba har yanzu domin kuɓutar da su.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP W. A Abiodun ya fitar, ya ce an aika jami'an tsaro da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami'an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru.

    Sanarwar ta ambato kwamishinan ƴansandan jihar, CP Adamu Abdullahi Elleman na jaddada ƙudirin rundunar na kuɓutar da ɗaliban ba tare da ji musu ciwo ba.

    Kwamishinan ƴansandan ya kuma yi kira ga al'umma su kwantar da hankali tare da bai wa jami'an tsaro haɗin kai a ƙoƙarin da suke yi na kuɓutar da ɗaliban.

    Ya kuma ce daga bisani za a ɗauki mataki kan hukumomin makarantar saboda ci gaba da karatu bayan umurnin kulle makarantu a yankin saboda barazanar tsaro.

  11. Ƙungiyar agaji ta Red cross za ta rage kasafin kudinta saboda raguwar samun tallafi

    Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce za ta zaftare kasafin kuɗin ta na shekara mai zuwa da kusan kashi ɗaya cikin biyar, sanadiyyar raguwar kuɗaden da take samu na tallafi.

    Za kuma ta sallami mutum kusan dubu 3, wato kashi 15 cikin 100 na ma'aikatanta da ke faɗin duniya.

    Wata sanarwa da shugabar Red Cross Mirjana Spoljaric ta fitar, ta ce halin da ake ciki a yanzu ne ke tilasta wa ƙungiyar ɗaukar matakai masu tsauri domin ta ci gaba da muhimman ayyukan jinƙai.

    Kasafin kuɗi na fannin ayyukan agaji a faɗin duniya na fuskantar koma baya a yayin da masu tallafawa ke mayar da hankulansu ga fannin tsaro.

  12. Mutum saba'in sun mutu a Gaza tun bayan tsagaita wuta - UNICEF

    Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar ɗinkin duniya ya ce aƙalla yara saba'in ne aka kashe a Gaza tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila ta soma aiki.

    Wani mai magana da yawun asusun, Ricardo Pires, ya ce aƙalla yara biyu ake kashewa duk rana, kuma zuwa yanzu gommai sun jikkata.

    Sojojin Isra'ila sun janye daga gabashin Gaza zuwa inda suke a yanzu.

    Sai dai sun ƙaddamar da hare hare kan abin da suka bayyana a matsayin ƴan Hamas da ke buɗe musu wuta.

  13. Ƴanbindiga sun nemi fiye da naira biliyan uku don sakin masu ibadar da suka sace a Kwara

    Rahotanni sun bayyana cewa ƴanbindigar da suka sace masu ibada a wani coci a jihar Kwara sun soma neman kuɗin fansa.

    Ƴanbindigar na neman a biya su dala dubu sittin da tara, kwatankwacin naira miliyan 100 kan kowane mutum.

    A ranar Talata ne ƴan bindiga suka kai hari kan wani coci da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar, inda suka kashe mutum biyu tare da sace mutane talatin da takwas.

    Sace masu ibadar ya zo ne kwana guda bayan da wasu ƴanbindigar suka sace wasu ɗalibai mata fiye da ashirin a jihar Kebbi.

    A daren jiya Alhamis kuma wasu ƴanbindigar suka yi awon gaba da wasu gwamman ɗalibai da malamai a wata makarantar coci da ke garin Papiri a yankin ƙaramar hukumar Agwara.

    Waɗannan hare hare dai na sake bayyana yadda matsalar tsaro ke addabar ƙasar, musamman ma arewaci.

  14. 'A kan babura maharan Neja suka je makarantar'

    Bayanai daga jihar Neja na cewa maharan da suka sace ɗaliban makarantar St. Mary a kan babura suka je.

    Sarkin Papiri, inda lamari ya faru ya shaida wa BBC cewa maharan sun je garin ne a kan babura inda suka karkasu.

    ''Wasu sun tsaya a bakin kasuwa, wasu kuma suka isa makarantar, inda suka harbe maigadin makarantar, wanda yanzu haka ke kwance a asibiti'',in ji shi.

    Ya ce kawo yanzu ba a san adadin ɗaliban da aka sace be.

    ''Har yanzu ba a gama tantance adadin ɗaliban da aka sace ba, sai zuwa an jima ne in an kammala za a fitar da sunayen ɗaliban'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

    Ya ƙara da cewa al'ummar garin na cikin tashin hankali da ɗimauta, tun bayan aukuwar harin.

  15. Ukraine ta ce Rasha ba ta ƙwace garin Kupiansk ba

    Rundunar sojin Ukraine ta musanta iƙirarin Rasha na ƙwace garin Kupiansk da ke gabashin ƙasar bayan mummunar gwabzawar da aka yi.

    Garin wanda ke a yankin Kharkiv, na da matuƙar muhimmanci saboda akwai layin dogon da ake amfanin da shi wajen gudanar da wasu muhimman ayyuka a kasar.

    Shugaban rundunar sojin ya ce dakarunsu sun ɗauki matakai na tarwatsa duk wasu masu shirin yi wa garin zagon kasa.

    A jiya Alhamis, shugaban rundunar sojin Rasha ya shaida wa shugaba Putin cewa sun kwace ikon Kupiansk.

    A ɓangare guda kuma jami'an Ukraine sun ce an kashe mutane biyar sannan wasu uku sun samu rauni a yayin wasu hare hare da Rasha ta kai a birnin Zaporizhzhia da ke kudu maso gabashin ƙasar.

  16. Gwamnatin Neja ta ɗora alhakin sace ɗalibai kan makarantar

    Gwamnatin jihar Neja da ɗora wa makarantar St Mary alhakin sace ɗaliban makarantar da ƴan bindiga suka yi a tsakar daren jiya Alhamis.

    Cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta ce rashin bin shawarar da ta bayar ne ya haifar da matsalar.

    'Dama tuni mun samu bayanan sirri game da barazanar tsaro a yankin - da ke yankin arewacin jihar, lamarin da ya sa muka ɗauki matakin rufe duka makarantun kwanan da ke yankin tare da dakatar da ayyukan gine-gine''. in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa amma abin kaico sai hukumomin makarantar St. Mary suka yi gaban kansu suka sake buɗe makarantar ba tare da sanar da gwamnati ko neman sahalewa ba, inda suka jefa rayukan ɗalibai da malaman makarantar cikin hatsari.

    Gwamnatin ta ce tuni ta ƙaddamar da bincike da ƙoƙarin kuɓutar da ɗaliban tare da maido da su cikin kwanciyar hankali.

    ''Gwamnatin jihar Neja na tuntuɓar jami'an tsaro kan matakan da ake ɗauka na kuɓutar da ɗaliban'', in ji Sanarwar.

    Harin na zuwa ne kwana biyar da sace ɗaliban makarantar sakandiren ƴanmata da ke garin Maga a jihar Kebbi tare da sace ɗalibai fiye da 20.

  17. Za mu goyi bayan shirin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Ukraine - Tarayyar Turai

    Babbar jami'ar harkokin wajen ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce tarayyar za ta goyi bayan duk wani shiri da zai kawo zaman lafiya mai ɗorewa a Ukraine, bayan shugaba Zelensky ya ce ya ƙarbi wani daftarin yarjejeniyar zaman lafiya daga Amurka.

    Kaja Kallas ta nanata cewa wajibi ne a sanya Kyiv da ƙawayenta na Turai a duk wata tattaunawa da za a yi.

    Zuwa yanzu ba a san mai daftarin ya kunsa ba, amma rahotannin kafafen yaɗa labarai na cewa an yi shi ne kan buƙatun Moscow.

    Buƙatun sun haɗa da Ukarine ta haƙura da ƙarin yankunan ta, ta kuma rage yawa sojojin ta, buƙatun da Kyiv ta yi watsi da su.

  18. Wace rawa Matawalle zai taka a yunƙurin ceto ɗaliban Kebbi?

    Tun bayan umarnin da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bai wa ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Mohammed Bello Matawalle na komawa jihar Kebbi domin taimaka wa yunƙurin ceton ɗaliban da ka sace, ƴan ƙasar ke ta magana kan irin da rawar da zai taka.

    A ranar alhamis ne Shugaba Tinubu ya umarci Bello Matawalle ya koma jihar - da ke arewa maso yammacin Najeriya - domin sanya idanu kan ƙoƙarin da gwamnatin ƙasar ke yi na ceto ɗaliban.

    Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a ranar Alhamis ta ce ministan zai isa jihar Kebbi a yau Juma'a b isa umarnin shugaban ƙasa.

    Tun farko shugaba Tinubu ya aika mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima zuwa jihar domin jajanta wa iyayen ɗaliban tare da ganawa da al'umar yankin da kuma bayyana musu irin matakan da gwamnati ke ɗauka ]wajen kuɓutar da ɗaliban.

    Karanta cikakken labarin a nan:

  19. Girgizar ƙasa ta kashe mutum 3 a Bangladesh

    Aƙalla mutum uku sun mutu a Bangladesh sakamakon wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki biyar da ɗingo biyar da aka samu a tsakiyar ƙasar da safiyar yau juma'ah.

    Wurin da iftila'in ya auku na da nisa kilomita 30 ne daga babban birnin ƙasar Dhaka.

    An ji girgiza a faɗin birnin da wasu jihohin gabashin indiya da ke da iyaka da Bangaladesh ɗin.

  20. Sabbin hare haren Rasha sun yi ajalin mutum biyar a gabashin Ukraine

    Jami'an Ukraine sun ce mutane biyar sun rasa ransu sannan kuma wasu uku sun samu rauni a yayin hare haren da Rasha ta kai birnin Zaporizhzhia da ke kudu maso Gabahsin kasar.

    Shugaban yankin Ivan Fedorov, ya ce harin ya shafi gidaje da wani shago da kuma kasuwa.

    Daga nan ya gargadi Rasha akan amfani da bama baman da aka jefa daga cikin jirgi a birnin.

    Wasu hotunan wajen sun nuna yadda jami'an agajin gaggawa ke ta kai koma wajen ganin sun kashe wutar da ta tashi a wani rukunin gida bayan bam din ya fada kansa.