Afirka ta Kudu ta ayyana matsalar rashin kyawun yanayi a matsayin babban bala'i
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ayyana matsalar rashin kyawun yanayi da ke shafar larduna da dama na ƙsar a matsayin babban bala'i a ƙasa.
Hukumomi a Afirka ta Kudu sun ce an ɗauki matakin bayan mamakon ruwan sama da ambaliya da hadari da walƙiya da iska mai ƙarfi da dusar ƙanƙara da suka lalata gine-gine da muhimman ayyuka a yankuna da dama.
Zuwa yanzu hukumomi ba su yi ƙarin bayani ba kan irin ta;annatin da rashin kyawun yanayin ya haifar.
Elias Sithole, shugaban hukumar yaƙi da bala'oi a Afirka ta Kudu ta ayyana lamarin a matsayin babban bala'i a ƙasar.
Sithole ya yi kira ga gwamnati da ta samar da tallafi ga hukumar don ta samu damar aiwatar da tsare-tsarenta na ganin ta magance matsalolin yanayin.