Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/12/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/12/2025.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Me ya sa ake saka jar hula a lokacin bukukuwan Kirsimeti?

    Santa

    Asalin hoton, Getty Images

    A lokutan bukukuwan Kirsimeti da mabiya addinin Kirista ke yi a faɗin duniya, kamar yadda ake ƙawata wurare da bishiyoyi masu lantarki haka ma za ka mutane na saka jar hula mai tulluwa da rastin fari a wuraren liyafa da taruka.

    A wasu wurare kuma kamar manyan shaguna da ma'aikatu za ka ga an kakkafa hular a kusa da bishiyar lantarki ta Kirsimeti.

    Ana dai kiran wannan hula da suna hular Santa.

  2. Mata a Iran na neman a saki wata ƴar fafutuka da aka yanke wa hukuncin kisa

    mata yan Iran

    Ɗaruruwan fitattun mata, ciki har da tsofaffin shugabannin kasa da firai ministoci da waɗanda suka samu kyautar Nobel ta zaman lafiya, sun fitar da takardar koke ga gwamnati ta saki wata mai fafutuka, a yayin da ake fargabar za a iya zartar da hukuncin kisa a kan ta.

    Wasikar ta ce a watan Oktoba aka yankewa Zahra Tabari mai shekara 67 hukuncin kisa, karkashin wani 'zaman kotu na jeka na yi ka da aka yi cikin minti goma'.

    Zuwa yanzu ba a tabbatar da hakan ba a hukumance.

    Sun ce ana zargin Ms Tabari da laifin rike wata takarda da ke kira da karfafawa farar hula gwiwa su nuna turjiya kan matsin da mata ke fuskanta a kasar Iran.

    Ana kuma zargin ta da zama ƴar kungiyar PMOI da gwamnati ta haramta a kasar.

  3. Kwamitin tsaro na MDD zai tattauna kan karuwar tashin hankali tsakanin Amurka da Venezuela

    Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na gab da fara zaman muhawara kan ƙaruwar tashin hankali tsakanin kasashen Amurka da Venezuela.

    Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela ne ya buƙaci muhawarar domin tattauna takalar faɗan da Amurka ke yi wa kasarsa.

    Rasha ta nuna cikakken goyon baya ga Venezuela, tare da nuna matukar damuwa kan matakan da Washington ke dauka da ta ke fakewa da na yaƙi da safarar muggan kwayoyi ne.

    Amurka dai ta sanar da hana tankokin mai na Venzuela wucewa ta tekun ta, da cewa za ta kwace man ta kuma saida shi.

    A nata bangaren Venezuela ta zargi Washington da fashi a tekun kasa da kasa.

  4. Canja dokokin haraji cin amanar ƴan ƙasa ne - Atiku

    ...

    Asalin hoton, TWITTER

    Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP, kuma a jigo a ADC, Atiku Abubakar ya ce canjin da ake zargi an samu a ƙudurin haraji da takardun da aka sanya wa hannu cin amanar ƴan ƙasa ne, sannan karan-tsaye ga kundin tsarin mulkin ƙasa.

    Atiku ya bayyana haka ne a shafukansa na sada zumunta, inda ya ce sauye-sauyen da aka samu sun nuna cewa gwamnatin ta fi mayar da hankali ne kan tatsar ƴan ƙasar sama da taimakonsu.

    Jigon siyasar hamayyar ya yi kira da a dakatar da aiwatar da ƙudurin harajin, wanda ake sa ran farawa a watan Janairun domin gudanar da cikkaken bincike.

    Ya kuma bukaci majalisar dokokin ƙasar ta yi gaggawar gyara sauye sauye da aka yi ba bisa kaida ba, sannan a hukunta masu hannu a yi wa kundin tsarin mulki zagon ƙasa, sannan hukumar EFCC ta gudanar da bincike kan su.

  5. 'Lambar NIN ce za ta zama TIN daga shekarar 2026'

    ...

    Asalin hoton, FIRS/WEBSITE

    Hukumar tattara haraji ta Najeriya (FIRS) ta ce daga watan Janairun 2026, lambar zama ɗan ƙasa (NIN) da hukumar rijistar katin ɗan ƙasa (NIMC) ta bai wa ƴan Najeria zai kasance lambarsu ta biyan haraji wato TIN, kamar yadda gidan talibijin na Channels ya ruwaito.

    Alƙaluman NIMC sun nuna cewa zuwa Octoban 2025, ƴan Najeriya miliyan 123 da dubu ɗari tara ne ke da lambar NIN.

    A cikin wani saƙon wayar da kan alumma kan sabuwar dokar harajin da hukumar tattara harajin ta wallafa a shafinta na X, ta ce lambobin rijista da hukumar yi wa kamfanoni rijista ta bai wa kamfanoni zai zama lambarsu ta biyan haraji a ƙarƙashin sabuwar dokar.

    FIRS ta ce sabon tsarin samar da lambar biyan harajin zai kawo sauƙi wajen tantance mutane da kamfanoni, ya rage matsalar nanata sunaye, ya rufe duk wata kafa da ake amfani da ita wajen kaucewa biyan haraji, da kuma tabbatar da cewa duk wanda ke samun kuɗin da ya kamata ya biya haraji ya biya kasonsa.

    Hukumar ta ce mutanen da ba su da hanyar samun kuɗaɗen shiga kamar ɗalibai ba sa buƙatar lambar biyan harajin.

  6. Magoya bayan tawagar Super Eagles a Morocco

    Nan ba da jimawa ba ne za a soma fafatawa tsakanin tawagar Super Eagles ta Najeriya da tawagar kwallon kafa ta Tanzania a ƙasar Morocco a gasar cin kofin Nahiyar Africa, AFCON.

    Tuni magoya bayan tawagogin suka isa filin wasan da ke birnin Fes.

    Ga yadda wasu daga cikin magoya bayan Super Eagles suka isa filin wasan.

    ...
    ...
    ...
    ...
  7. Tattalin arziƙin Amurka ya ƙaru a rubu'i na uku na 2025

    Tattalin arzikin Amurka ya karu fiye da yadda ake tsammani a rubu'i na uku na wannan shekara.

    Tattalin arzikin ya bunƙasa da kashi huɗu da digo uku, wani adadi da ya fi wanda aka samu a rubu'i na biyu na shekarar.

    Wannan dai shi ne ƙaruwa mafi girma da tattalin arziƙi mafi girma a duniya ya samu cikin shekaru biyu.

    Wani rahoto na gwamnatin Amurka ya ce an samu ci gaban ne sakamakon ƙaruwar kashe kuɗi da masu sayen kaya ke yi da kuma ƙaruwar fitar da kayyayaki daga ƙasar.

    Sai dai duk da haka hauhawar farashin kayayyaki bai ragu ba, inda har yanzu ya ke maki biyu da digo takwas, wanda kuma ya wuce yadda gwamnati ta tsara.

  8. DRC ta koma fitar da ma'adanin Cobalt

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo ta koma fitar da ma'adinin Cobalt da ake amfani da shi wajen hada latironi, bayan dakatar da fitar da shi na watanni 10 da nufin daidaita farashinsa da sauran kasashen duniya.

    Ministan kudin kasar Doudou Fwamba ya ce matakin da aka gabatar ya yi amfani, kuma za a fitar da sabon tsarin yadda fitar da ma'adinin za ta kasance.

    Ya ce farashin cobalt ya karu da kusan kashi 50 cikin 100, inda a baya ake saida tan 1 kan farashin dala dubu 22, yanzu kuma ya kusan dala dubu 50.

    Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo dai na sahun gaba a duniya wajen samar da ma'adinun na Cobalt da ake amfani da shi wajen yin batiran wayar salula da kayan laturoni da mota mai aiki da lantarki.

  9. Ƴan Houthi da gwamnati sun amince su yi musayar fursunoni

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan tawayen Houthi a Yemen da gwamnatin da kasashen waje ke marawa baya sun cimma yarjejeniyar musayar fursunoni 3000 a tsakaninsu.

    Wakilai daga dukkan bangarorin biyu sun tabbatar da cimma matsayar da ke xuwa bayan kusan makonni biyu da tattaunawa tsakaninsu da kasar Oman ta jagoranta.

    Wakilin BBC ya ce idan hakan ta tabba wannan zai zamo musayar fursunoni mafi girma tun bayan barkewar yaki a Yemen sama da shekaru 10 da suka gabata.

    Wani mai shiga tsakani a bangaren Houthi ya ce gwamnati za ta sako mambobinsu 1700, inda su kuma za su yi musayarsu da fursunonin bangaren gwamnati 1200.

    Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Yemen Hans Grundberg, ya ce su na fatan wannan zai bude wata hanya da fursunoni da iyalansu za su masu saukin wahalar da suke ciki.

  10. Sojojin Isra'ila ba za su fice gaba ɗaya daga Gaza ba - Israel Katz

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan tsaron Isra'ila ya ce sojojin Isra'ila ba za su fice baki daya daga zirin Gaza, a wani mataki da ake ganin zai janyo cikas a shirin Amurka na zaman lafiya a yankin.

    A jawabin da ya gabatar ga shugabannin yankunan da Yahudawa 'yan kama wuri zauna, Israel Katz, ya kara da cewa idan lokaci ya yi, za a samar da rundunar sojin Isra'ila maimakon a zaba cikin Falasdinawa da suka rasa muhallansu.

    Wannan na nufin zama daram ga 'yan kama wuri zauna da ke wurin sama da shekaru 20. Firai minista Benyamin Netanyahu ya sha nanata fadada matsugunan yahudawa a zirin Gaza.

  11. Myanmar na tilasta farar hula yin zaɓe - Volker Turk

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce gwamnatin sojin Myanmar na amfani da azabtarwa da barazana ga farar hula da tilasta musu fita kaɗa kuri'a a zaben da ke tafe.

    Volker Turk ya ce sojojin na amfani da matakin kan duk wanda ya nuna ra'ayin da bai zo daidai da muradinsu ba.

    Ya yi gargadin mutane na cikin kalubale da firgici daga kungiyoyin masu dauke da makamai da ke adawa da gwamnatin sojin Myanmar.

    Zaben da za a yi a ranar 28 ga watan nan na Disamba, shi ne na farko a kasar tun bayan hambarar da mulkin shugaba Aung San Suu-kyi da sojojin suka yi a shekarar 2021,

    Sai dai an cire 'yan takarar yawancin jam'iyyun adawa, kuma lamari ne mai matukar wuya a gudanar da zaben a wuraren da 'yn tawaye suke iko da su.

  12. Sabbin bayanai sun nuna Trump ya sha yin tafiye-tafiye a jirgin Epstein

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar shari'ar Amurka ta wallafa karin dubban bayanai masu alaka da mutumin nan da aka samu da laifukan lalata da kananan yara, Jeffrey Epstein.

    Wannan ce wallafa mafi girma tun bayan fara binciken, cikin bayanan akwai sakon Email da wani mai bincike a ma'aikatar shari'a ya aike da ke cewa shugaba Donald Trump ya sha yin tafiye-tafiye a jirgin Epstein fiye da bayanan da aka bada tun da farko.

    Wakilin BBC ya ce sakon Email din an aike shi ne ranar 7 ga watan Junairun shekarar 2020, lokacin da Mr Trump na matsayin shugaban kasa.

    Mataimakin shugaban tawagar masu binciken, ya yi bayanin balaguron da Mr Trump da Epstein da Ghislaine Maxwell su ka yi, da a lokacin da ake kokarin bincike akan ta.

  13. MDD ta ce dubban yan gudun hijira daga Kongo na tserewa zuwa Burundi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar ɗinkin duniya ta ce aƙalla ƴan gudun hijira dubu casa'in ne ke tserewa daga Kudancin Kivu a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo zuwa Burundi saboda ƙaruwar tashin hankali.

    Mutanen da suka rasa matsugunansu na fuskantar mawuyacin hali a sansanin ƴan gudun hijira, kuma ba sa samun isassun abinci da ruwa.

    Kungiyar agaji ta Doctors without Borders ta bayyana damuwarta kan yadda kiwon lafiya ke taɓarɓarewa da kuma matsalar agaji.

    Kungiyar ta ce ta na kula da aƙalla mutum 200 a kullun, tun bayan da ƴan gudun hijirar suka soma isa Burundi makonni biyu da suka gabata.

    Kusan rabin mutanen da suka rasa muhallansu yara ne ƴan kasa da shekara 18, da dama kuma mata ne ciki har da masu juna biyu waɗanda rahotanni ke cewa sun kwashe kwanaki ba su ci abinci ba.

  14. NBA ta nemi a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji

    ..

    Asalin hoton, NBA/WEBSITE

    Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta yi kira da a dakatar da aiwatar da sabuwar dokar haraji da ake shirin fara aiki da ita a ranar 1 ga watan Janairun 2026.

    Wannan dai na zuwa ne bayan zargin cewa an sauya ko kuma yin cushe a dokar da aka fitar saɓanin abin da majalisar ƙasar ta amince da shi.

    Wannan batu ya fara fitowa ne makon da ya gabata bayan wani ɗan majalisar wakilai daga Sokoto, Abdulsamad Dasuki, ya bayyana cewa akwai bambance-bambancen a dokar da ya lura da su.

    A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, NBA ta ce lamarin na tayar da “hankali dangane da sahihanci da gaskiya da amincin tsarin dokokin Najeriya.”

    Ƙungiyar ta nemi a gudanar da cikakken bincike a bayyane domin fayyace yadda aka samu dokokin tare da jaddada cewa dole ne a dakatar da duk wani shiri na aiwatar da dokar har sai an warware batun.

    Shugaban NBA, Afam Osigwe, ya ce "zargin ya sanya ayar tambaya kan tsari da bin doka wajen samar da dokoki."

    Ya kara da cewa "Irin wannan rikici na iya haifar da matsalolin tattalin arziki tare da tayar da hankalin ’yan kasuwa da masu zuba jari da haifar da rashin tabbas ga jama’a da hukumomin da dokar ta shafa.

    A watan Yuni ne Shugaba Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan kudurorin gyaran haraji guda huɗu, inda suka zama doka bayan dogon muhawara.

  15. Ana ƙaddamar da rundunar tsaro da kare unguwanni ta jihar Kano

    ...

    Asalin hoton, Ibrahim Adam (Deemoo)/Facebook

    Yanzu haka gwamnatin jihar Kano na ƙaddamar da rundunar tsaro da kare unguwanni na mutum 2000 a filin wasa na Sani Abacha, a wani mataki da ake sa ran zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da rage laifuka a sassan jihar.

    An kafa rundunar ne domin taimakawa hukumomin tsaro na ƙasa wajen sa ido da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a matakin unguwanni.

    ...

    Asalin hoton, Ibrahim Adam (Deemoo)/Facebook

    Rahotanni sun nuna cewa rundunar za ta ƙunshi matasa da aka horas musamman kan ayyukan tsaro da tattara bayanan sirri da kuma aiki tare da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro.

    Gwamnatin jihar ta ce za a rarraba rundunar a ƙananan hukumomi daban-daban domin tabbatar da tsaro a kasuwanni da makarantun da unguwanni da sauran muhimman wurare.

    Haka kuma, gwamnatin jihar ta jaddada cewa ƙaddamar da rundunar na daga cikin ƙoƙarin da take yi na samar da zaman lafiya mai ɗorewa da kuma bai wa al’umma kwarin gwiwar rayuwa cikin aminci.

    Ta yi kira ga mazauna jihar da su ba da haɗin kai tare da tallafa wa rundunar domin ta samu nasara a aikinta na kare lafiyar jama’a.

    ...

    Asalin hoton, Ibrahim Adam (Deemoo)/Facebook

  16. Muna da ƙwarin gwaiwa Najeriya za ta doke Tanzaniya - magoya bayan Super Eagles

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton domin kallon bidiyon

    Magoya bayan Super Eagles sun bayyana cikakken ƙwarin gwiwa da cewa tawagar Najeriya za ta doke Tanzaniya a wasan da za su fafata a ranar Talata a filin ƙwallo da ke birnin Fez na Morocco.

    Magoya bayan sun ce Super Eagles na da ƙwarewa da jajircewar da za su kai ga samun nasara duk da rashin samun tikitin shiga gasar kofin duniya.

    Da yake magana da BBC, kocin Kano Lions ya ce wasan Najeriya da Tanzaniya wata dama ce ga tawagar ta farfaɗowa tare da dawo da martaba.

    Ya jaddada cewa ƴan wasan Najeriya na da ƙoƙari da hazaka da za su iya ba su nasara a wasan. Ya ƙara da cewa duk da ƙalubalen da suka fuskanta a baya, tawagar na cike da ƙwarin gwiwa da azama.

  17. Man da ake samarwa a kullum ya kai lita miliyan 71.5 - NMDPRA

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, NMDPRA ta bayyana cewa yawan man fetur da ake samarwa a kullum ya ƙaru zuwa lita miliyan 71.5 a watan Nuwamba 2025, daga lita miliyan 46 a kullum da ake samu a watan Oktoba.

    Hukumar ta ce gagarumin ƙarin a watan Nuwamba ya samo asali ne daga shigo da man da Kamfanin NNPCL ya yi, wanda ya samar da kashi 55 cikin 100 na wadataccen man fetur a kasuwannin Najeriya, daga hanyoyin cikin gida da kuma ƙasashen waje.

    Takardar bayanai ta watan Nuwamba 2025 da aka fitar a ranar Litinin ta nuna cewa yawan amfani da man fetur a ƙasar ya ƙaru da kashi 44.5 cikin 100 zuwa lita miliyan 52.1 a kullum a watan Nuwamba, idan aka kwatanta da lita miliyan 28.9 a watan Oktoba, lamarin da ya nuna akwai ƙarin lita miliyan 37.4.

    A cewar rahoton, matatun mai na cikin gida sun samar da lita miliyan 17.1 a kullum a wannan lokaci, yayin da matsakaicin yawan amfani da man fetur a watan ya kai lita miliyan 52.9 a kullum.

    Sai dai NMDPRA ta bayyana cewa ba a samar da mai daga dukkan matatun mai na gwamnati da suka haɗa da na Fatakwal da Warri da Kaduna, domin matatun sun ci gaba da kasancewa a rufe.

  18. Rasha ta ƙara tsananta hare-harenta kan yankin Odesa na Ukraine

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rasha ta ƙara tsananta hare-harenta a yankin Odesa da ke kudancin Ukraine, lamarin da ya haddasa katsewar wutar lantarki a wasu sassa tare da barazana ga muhimman ababen more rayuwa na harkar jiragen ruwa.

    Mataimakin Firaministan Ukraine, Oleksiy Kuleba, ya ce Moscow na kai hare-haren ne “cikin tsari,” yana mai gargaɗin cewa a makon da ya gabata cewa hankalin yaƙin “na iya karkata zuwa Odesa.”

    Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce hare-haren da ake kaiwa akai-akai na nufin toshe damar Ukraine ta amfani da hanyoyin safarar kayayyaki ta teku.

    A farkon watan Disamba, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi barazanar katse wa Ukraine hanyarta ta zuwa teku a matsayin martani ga hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da aka kai wa tankokin man Rasha a Tekun baharul aswad.

    A daren Litinin ne hare-hare suka auku kan kayayyakin tashar jiragen ruwa a Odesa, inda suka lalata wani jirgin farar hula, kamar yadda gwamnan yankin ya bayyana.

  19. Gwamnatin Najeriya ta ayyana masu sace mutane a matsayin ’yan ta’adda

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta ayyana masu garkuwa da mutane da ƙungiyoyi masu ɗaukar makamai da masu tayar da ƙayar baya a matsayin ’yan ta’adda, a wani sabon mataki da nufin ƙara tsaurara yaƙi da sace-sacen mutane da hare-hare da kuma tashin hankali a yankunan karkara.

    Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na ƙarshen shekara da aka gudanar a Abuja, inda ya ce matakin ya kawo ƙarshen ruɗani kan yadda ake kallon irin waɗannan laifuka.

    Ya ce daga yanzu duk wanda ya sace mutane ko kuma ya kai hari kan manoma ko ya tsoratar da al’umma, za a ɗauke shi a matsayin ɗan ta’adda, kuma za a yi mu’amala da shi bisa haka.

    Ministan ya ƙara da cewa "Sabon tsarin zai ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomin tsaro, lamarin da zai ba su damar ɗaukar mataki cikin gaggawa da inganci."

    Domin kare yankunan karkara, ministan ya ce "An tura masu gadin daji da aka horar da su tare da kayan aikin sa ido da saurin ɗaukar mataki, domin katse hanyoyin samar da abinci ga ’yan ta’adda da rushe maboyarsu da kuma ƙarfafa gwiwar manoma da ke fama da rashin tsaro."

  20. Muna tunanin sayar da man da muka ƙwace daga Venezuela - Trump

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce zai iya ajiye ko sayar da man da ke cikin tankokin man da ya ƙwace a wannan watan a gaɓar ruwan Venezuela.

    Kazalika ya ce jami'an tsaron tekun Amurka na ci gaba da kokarin ƙwace wata tankar man.

    Ya shaida wa manema labarai cewa da shugaban Venezuela mai dabara ne da ya sauka daga kan muƙaminsa duk da goyon bayan siyasar da ya ke samu daga China da Rasha.

    Trump na wannan jawabin ne bayan sanar da cewa Amurka za ta kera wani sabon jirgin ruwa na yaƙi da za a kira da sunansa.

    Sabon jirgin ruwan yaƙin zai kasance mafi girma da inganci da kuma sauri kamar yadda shugaba Trump din ya yi alkawari.