Mene ne ƙarfin sojin Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan ɗaukin gaggawa da sojojin saman Najeriya suka kai ƙasar Benin inda suka taimaka wajen daƙile yunƙurin juyin mulki da sojoji suka so yi, ƴan Najeriya da ma Afirka sanin irin karfin da Najeriya ke da shi idan aka kwatantan da sauran ƙasashen Sahel.
Baya ga tura jiragen yaƙi, majalisar dokokin Najeriya ta kuma amince da buƙatar Bola Tinubu na aikewa da rundunar soji zuwa Benin ɗin domin wanzar da zaman lafiya.
Ana cikin haka ne kuma sai hukumomin Burkina Faso suka riƙe wani jirgin sojin Najeriya ƙirar C-130 tare da mutane 11 da yake dauke da su.
Ƙungiyar ƙasashen Sahel, wadda ta ƙunshi Jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso sun zargi jirgin na Najeriya da keta hurumi ta hanyar tsallake iyaka ba bisa ƙa'ida ba.
Najeriya a nata ɓangaren ta ce jirgin yana kan hanyarsa ce ta zuwa ƙasar Portugal, inda ya samu tangardar na'ura, lamarin da ya tursasa masa yin saukar gaggawa a ƙasar ta Burkina Faso, kuma hukumomin sun ce an yi komai ne "a kan tsari."




















