Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 5 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

  • Kwankwasiyya ta musanta fitar da Kwankwaso waje don neman lafiya
  • Latsa nan domin shiga zaurenmu na Whattsapp
  • Nnamdi Kanu ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin ɗaurin rai-da-rai da aka yanke masa
  • An kashe ƴan Road Safety fiye da 100 a shekarar 2025 - Shugaban FRSC
  • An ceto mutane 166 da aka sace a Kajuru
  • Jami'an LASTMA sun ƙwace motoci 27 a Legas
  • Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta sake tura tawagar sa ido zuwa Tigray bayan ɓarkewar rikici
  • Musulmai 75 aka kashe a harin Kwara - AbdulRazaq
  • MDD ta yi gargaɗin barazanar nukiliya yayin da yarjejeniyar Amurka da Rasha ke ƙarewa
  • Tinubu ya tura bataliyar soji jihar Kwara

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Ahmad Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Najeriya za ta ƙarfafa dangantaka da Falasɗinu

    Najeriya da Falasɗinawa

    Asalin hoton, Ministry of Foreign Affairs

    Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya ce Najeriya za ta ƙarfafa hulɗar dangantaka da Falasɗinawa da kuma kyautata ayyukan jin-ƙai a Gaza.

    Tuggar ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin jakadan Falasɗinawa a Najeriya, Muhannad Halmouri a Abuja, babban birnin Najeriya.

    Jakadan na Falasɗinawa ya nuna jin daɗinsa kan daɗaɗɗiyar goyon baya da Najeriya ke bai wa Falasɗinu da kuma ganin ta samu cin gashin kai.

    Halmouri ya bayyana irin yanayin jin-ƙai da Gaza ke fama da shi, ciki har da matsalolin tsaro da ake fuskanta da kuma taƙaita shigar da agaji yankin.

    Jakadan Falasɗinawan ya ce gwamnatin Falasɗinawa na cike da farin ciki kan tattaunawar da aka yi a Najeriya don ganin dangantakar ɓangarorin ta ɗore.

    Tuggar ya tabbatar da cewa Najeriya za ta yi abin da ya kamata wajen ganin an shawo matsalolin da Falasɗinawan ke fuskanta ta hanyar tattunawar diflomasiyya.

    Najeriya dai ta daɗe tana nuna goyon baya ga Falasɗinawa a rikicinsu da Isra'ila, inda a watan Nuwambar 2024, shugaba Tinubu ya yi kira ga shugabannin duniya da su taimaka wajen kawo karshen farmakin soji da Isra'ila ke yi a Gaza da kuma ƙara nanata goyon baya na samar da mafita ta ƙasashe biyu.

  3. Ƴanbindiga sun hallaka mutum biyar a harin kwanton ɓauna a Zamfara

    Ƴanbindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu ƴanbindiga sun hallaka mutum biyar tare da yin garkuwa da wasu da dama bayan harin da ƙwantan ɓauna da suka kai wata kasuwa a jihar Zamfara.

    Mazauna yankin na komawa gida daga kasuwar Maga a karamar hukumar Bukkuyyum da yammacin ranar Laraba lokacin da aka kai musu harin.

    Lamarin ya saka fargaba a zuƙatan al'ummomi da ke kusa.

    "Aƙalla mutum biyar aka tabbatar da mutuwarsu, sannan ba a ga wasu da dama ba zuwa yanzu. Ana ci gaba da aikin ceto, sai dai fargaba na ƙara yaɗuwa a tsakanin al'ummomi," kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana.

    Mazauna yankin dai na buƙatar gwamnati ta kai musu ɗaukin gaggawa domin nemo waɗanda suka ɓata da kuma dakatar da hare-haren da ake kai musu.

    Harin na zuwa ne kwana guda bayan artabu tsakanin sojoji da ƙungiyoyin ƴanbindiga ya janyo mutuwar dakaru da ƴan ta'adda da dama a karamar hukumar Maru na jihar ta Zamfara.

  4. Kwankwasiyya ta musanta fitar da Kwankwaso waje don neman lafiya

    Sanata Kwankwaso

    Asalin hoton, Saifullahi Hassan/FB

    Ƙungiyar siyasa ta Kwankwasiyya ta musanta rahotanni da ke iƙirarin cewa an fita da jagoran jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso waje don neman lafiya.

    Mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiyya a Najeriya, Captain Mansur Kurugu, ya shaida wa BBC cewa Kwankwaso ya tafi ƙasar waje ne don wata buƙatarsa.

    "Abin da zai ƙara tabbatar da haka shi ne ranar Laraba kafin balaguronsa ya shiga jihar Kano kuma ya gana da mutane daban-daban. A safiyar yau Alhamis kuma dubban mutane daga karamar hukumar Dawakin Kudu sun kawo masa ziyara aka tattauna sannan ya zarce zuwa kasuwar Singer don jajantawa ƴan kasuwar da suka rasa duƙiyoyi," in ji Mansur.

    Ya ce mutumin da ba shi da lafiya ba zai yi irin waɗannan al'amura ba, inda ya ce waɗanda ba su ji daɗin tarbar da aka yi masa ba a Singer su suka kirkiro da labarin.

    "Babu wata magana ta rashin lafiya ko wata damuwa. Kawai masu jin tsoro ne ke son kawo labarin don disashe irin karɓuwar da Kwankwaso yake ƙara samu," in ji shi.

    Ya ce jagoran Kwankwasiyyar zai koma Najeriya nan ba da daɗewa ba idan ya kammala abin da ya je yi a ƙasar waje.

    Balaguron da Sanata Kwankwaso ya yi zuwa waje dai ta karaɗe shafukan sada zumunta inda ake ta yaɗa cewa ya fita ne don neman lafiya.

  5. 'Fari na ƙara yaɗuwa a yankin Darfur na Sudan'

    Farmine

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata ƙungiyar sa ido da ke samun goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa fari na ƙara yaɗuwa a yankin Darfur na Sudan, kusa da iyaƙa da Chadi.

    Ƙungiyar ta ce rashin abinci mai gina jiki ya kai maƙura a yankunan Um Baru da Kernoi, inda ta ce lamarin ya shafi jarirai da ƙananan yara.

    Yankunan sun fuskanci ƙwararowar mutane da dama waɗanda ke tserewa daga birnin El-Fasher, tun bayan da birnin ya faɗa hannun dakarun RSF a shekarar da ta gabata.

    Ƙungiyar ta IPC ta yi kiran cewa a ɗauki mataki nan take domin dakatar da faɗa a yaƙin basasar ƙasar, da buɗe hanya ga fararen hula su fice da kuma samar da agaji.

  6. An kama ƴan Najeriya 109 kan zargin safarar ƙwayoyi a Indiya

    India

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴansanda a jihar Maharashtra na Indiya sun ce sun tsare wasu ƴan Najeriya 109, waɗanda suka kama kan laifin zama ba bisa ka'ida ba a ƙasar, inda suka ce sun ƙwace hodar iblis mai nauyin kilogram biyu a wajen miutanen.

    Hukumomin ƙasar sun ce babu wanda yake da cikakkun takardun zama cikin mutanen, waɗanda ke zaune a birnin Nalasopara da ke gabashin ƙasar.

    An kai samame yankin ne da misalin karfe 6 na safe, a cewar mataimakiyar kwamishinan ƴansandan yankin Poornima Chowgule-Shringi.

    "A lokacin samamen ne muka samu damar ƙwace hodar iblis mai nauyin giram 2 daga hannun wani mutum," in ji ta.

    An sha samun hannun ƴan ƙasashen waje daga Najeriya, Uganda da kuma Ghana waɗanda ke rayuwa a Nalasopara da Achole da kuma Tulinj a batun safarar miyagun ƙwayoyi, in ji jami'ar ƴansandan.

  7. Iran ta ƙwace jiragen ruwa biyu ɗauke da ɗanyen mai

    Jirgin ruwa

    Asalin hoton, Reuters

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce dakarun juyin juya-hali sun ƙwace jiragen ruwa biyu ɗauke da ɗanyen mai tare da ma'aikatansu a yankin Gulf.

    Kamfanin dillancin labarai na Tasnim (wanda ke kusa da dakarun) ya ce jiragen ruwan na ɗauke da litocin fetur sama da miliyan ɗaya, wanda Tehran ta yi zargin cewa safarar shi a aka yi.

    An kama jiragen ne bayan wani samame da aka gudanar.

    Ba a dai san tutocin ƙasashen da ke jikin jiragen ba da kuma inda ma'aikatan suka fito, sai dai an damka su hannun hukumomin shari'ar Iran.

    An ƙwace jiragen ne kusa da tsibirin Farsi na Iran, wanda yake kusa da Saudiyya.

    Ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar tsakanin Iran da Amurka, sai dai ƙasashen biyu na sa ran tattaunawa a ranar Juma'a.

  8. Gwamnonin arewa sun yi Alla-wadai da kashe-kashen Katsina, Kwara da Benue

    Gwamnonin arewa

    Asalin hoton, Gombe State Government

    Ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ta yi Alla-wadai da kashe-kashen mutane a jihohin Katsina, Kwara da kuma Benue, inda suka kwatanta hakan a matsayin rashin imani kuma cin mutunci ga ƙasa.

    Alla-wadai ɗin na zuwa ne bayan munanan hare-hare da aka kai karamar hukumar Kaiama na jihar Kwara, inda waɗanda ake kyautata zaton ƴanbindiga suka kutsa jihar ranar Talata tare da kashe sama da mutum 100, da harin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina wanda ya hallaka aƙalla mutum 20, sai kuma wani hari na daban a karamar hukumar Kwande na jihar Benue da ya janyo mutuwar mutane da dama.

    Cikin wata sanarwa, shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya nuna kaɗuwarsa kan rayukan da aka rasa, inda ya miƙa ta'aziyya a madadin sauraran gwamnonin zuwa ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa da kuma al'ummar jihohin uku.

    "Wannan ɗayen aiki abin Alla-wadai ne kuma abu ne da ba za mu lamunta ba.

    "Cigaba da far wa mutane, ciki har da mata da yara da kuma tsofaffi yana ƙara nuna rashin imani na waɗannan mahara da kuma buƙatar ɗaukar mataki mai tsauri a kansu," in ji Inuwa Yahaya.

    Ya yaba wa gwamnonin jihohin bisa jajircewarsu wajen ganin an daƙile barazanar tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya.

    Gwamnan na Gombe ya shawarci jami'an tsaro da su ci gaba da hoɓɓasa da tattara bayanan sirri wajen ganin an bi sawun ƴanbindigar da nufin kama su.

    Ƙungiyar gwamnonin arewar ta yi addu'ar Allah ya gafartawa waɗanda suka mutu da kuma addu'ar samun lafiya ga mutanen da suka jikkata a hare-haren.

  9. An yanke wa mutumin da ya yi yunƙurin kashe Donald Trump ɗaurin rai-da-rai

    Ryan Routh

    Asalin hoton, Getty Images

    An yanke wa mutumin da ya yi yunƙurin hallaka Donald Trump, mai suna Ryan Routh hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

    An samu Routh mai shekara 59 da laifin koƙarin kashe Trump a filin wasan golf da ke jihar Florida a watan Satumbar 2024, lokacin da yake ɗan taƙarar shugaban ƙasa.

    Wani jami'in sirri na Amurka ne ya hango kan bindigar mutumin cikin wani daji, inda bai yi wata-wata ba ya yi harbi zuwa wajen.

    Lamarin ya saka Routh tserewa daga wajen, sai dai an samu nasarar cafke shi.

    Lokacin da take yanke hukuncin, mai shari'a Aileen Cannon ta ce babu wani hukunci da ya kamata a yanke wa mutumin illa ɗaurin ra-da-rai.

    Sai dai, lauyan Routh, Martin Ross ya ce za su ɗaukaka ƙara.

    Ryan ya yi watsi da tuhumar da ake yi masa, inda ya zaɓi tsayawa kansa yayin shari'ar wadda aka fara ranar 8 ga watan Satumba.

  10. Gwamnan jihar Sokoto ya umarci a kama mutanen da suka ƙona bishiyoyin gwamnati

    ...

    Asalin hoton, SSGOV

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya umarci jami'an tsaro su kama mutanen da suka ƙona bishiyoyin da aka shuka domin hana kwararowar hamada a ƙaramar hukumar Wurno da ke jihar.

    Gwamnan ya bayar da umarnin ne a yau Alhamis bayan wata ziyara da ya kai ƙaramar hukumar domin ƙaddamar da sayar da takin zamani kan farashi mai rahusa ga masu noman rani.

    ...

    Asalin hoton, SSGOV

    A cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar ta hannun shugaban sashen yaɗa labarai da kafafen sadarwa ya ce: "Babu wani dalili da zai sa a sare bishiya ba tare da dalili ba, kuma duk wanda aka kama da laifin hakan zai fuskanci fushin hukuma".

    Sanarwar ta ƙara da cewa "gwamna Aliyu ya jaddada buƙatar ganin jami'an tsaro sun gano waɗanda suka ƙona itatuwan, ta yadda za a hukunta su domin su zama darasi ga wasu".

    ...

    Asalin hoton, SSGOV

    Sokoto na daga cikin jihohin Najeriya da ke iyaka da hamadar Sahara, inda take fuskantar barazanar kwararowar hamada.

    A shekarar 2009, gwamnatin jihar Sokoto ta sanar cewa, za ta samar da shingen bishiyoyi mai tsawon kilomita 46 tare da haɗin gwiwar ƙananan hukumomin jihar.

  11. Ukraine da Rasha sun amince da musayar fursunonin yaƙi bayan tattaunawar zaman lafiya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Tattaunawar kwanaki biyu tsakanin Ukraine da Rasha da kuma Amurka, da nufin kawo ƙarshen yaƙin da Moscow ke yi da Kyiv ta ƙare da musayar ƙarin fursunonin yaƙi.

    A Sakamakon tattaunawar, za'ayi musayar Fursunonin yaki sama da 300 da aka kama a tsakanin Rasha da Ukraine.

    Dukkanin ɓangarorin biyu sun bayyana tattaunawar da aka yi a Abu Dhabi a matsayin mai amfani.

    A ranar Juma’ar da ta gabata ne, wakilin Amurka na musamman Steve Witkoff ya ce tattaunawar za ta kasance mai amfani, sai dai har yanzu akwai aiki mai yawa a gaba.

    Amma duk da haka, babu wata alama da ke nuna cewa Rasha ta sauya ra’ayi kan batun yankunan da ake takaddama a kai.

  12. Nnamdi Kanu ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin ɗaurin rai-da-rai da aka yanke masa

    Nnamdi Kanu
    Bayanan hoto, Nnamdi Kanu

    Shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya shigar da ƙara a gaban kotun ɗaukaka ƙara kan hukuncin ɗaurin rai-da-rai da kotun tarayya mai zamanta a Abuja ta yanke masa bisa zargin ta’addanci.

    Alƙali James Omotosho ne ya yanke wa Kanu hukuncin a ranar 20 ga Nuwamba, 2025, bayan da ya same shi da laifi a dukkan tuhume-tuhume guda bakwai da gwamnatin Najeriya ta gabatar a kansa.

    Alƙalin ya kuma yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bisa laifin kasancewa mamba da kuma jagoran wata ƙungiya da gwamnatin Najeriya ta ayyana a matsayin ƙungiyar ta’addanci.

    Haka kuma, an ƙara masa hukuncin ɗaurin shekaru biyar bisa zargin shigo da na’urar watsa shirye-shiryen rediyo cikin ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

    A cikin ƙarar da ya shigar, Nnamdi Kanu ya bayyana wa Kotun ɗaukaka ƙara cewa akwai kurakurai da dama a cikin hukuncin da Alƙali Omotosho ya yanke.

    Bisa ga waɗannan kurakurai da ya ce kotun shari’a ta aikata, Kanu ya yi kira ga ƙotun ɗaukaka ƙara da ta soke hukuncin da aka yanke masa kan dukkan tuhume-tuhume guda bakwai da aka same shi da laifi a kansu.

    Haka kuma, ya buƙaci kotun da ta soke hukunci da azabtarwar da aka fara yanke masa, tare da buƙatar a sake shi gaba ɗaya daga dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.

  13. An kashe ƴan Road Safety fiye da 100 a shekarar 2025 - Shugaban FRSC

    ...

    Hukumar kiyaye haɗurra ta Najeriya FRSC ta ce an kashe jami’anta fiye da 100 yayin da suke bakin aiki a shekarar 2025 da ta gabata.

    Hukumar ta bayyana cewa ƙaruwa a yawan mutuwar jami’anta ya sa ta fara kira ga gwamnatin tarayya da ta ba ta damar bai wa jami’anta makamai domin kare kansu, tare da ƙara musu kwarin gwiwa yayin gudanar da aikinsu a kan hanyoyi.

    Shugaban hukumar FRSC, Shehu Mohammed ya shaida wa BBC cewa direbobi ne yawanci suke buge jami'an yayin da suka kan bakin aikinsu.

    “A shekarar da ta wuce mun shiga juyayi na rasa kusan jami’anmu 127, kuma kusan dukkansu direbobi ne suka buge su suna kan aiki lamarin da ke ci maana tuwo a ƙwarya,” in ji shi.

    Ya ce abin da ya fi tayar musu da hankali shi ne yadda wasu direbobi ke buge jami’ansu ɗin duk da cewa suna tsaye ne a gefen hanya.

    “Abin takaici shi ne wani direba zai buge jami’anmu alhali suna kan gefen hanya. Wasu lokutan ma kamar da gangan ake yi. Wannan ne ya sa kullum muke ƙara faɗakar da direbobi su guji shan giya ko wani abu mai sa maye kafin su zauna kan tuƙi,” in ji shugaban hukumar.

    Shugaban hukumar ya ƙara da cewa bai wa jami’an FRSC damar riƙe makami zai zama wata hanya ta rage irin waɗannan haɗurra.

    “Shi ya sa muke ta kira da a bar jami’anmu su riƙe makami. Wannan zai bayar da kwarjini, zai ƙara musu ƙarfin gwiwa, kuma direbobi za su ji tsoron yin wani abu da zai cutar da su,” in ji shugaban.

    Sai dai ya jaddada cewa idan aka amince da batun riƙe makami, horo mai tsauri shi ne abu mafi muhimmanci dsa za su fifita.

    “Idan aka ba mu dama mu riƙe makami, horo ne zai zama na farko. Horo ne zai kawo hankali, zai sa a bi doka, kuma zai sa jami’i ya fahimci haƙƙin ɗan Adam, ta yadda ba zai yi amfani da makami wajen cutar da wani ba,” in ji shi.

  14. An ceto mutane 166 da aka sace a Kajuru

    ...

    Asalin hoton, Uba Sani/x

    An ceto ɗaukacin mutane 166 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su daga wasu majam'iu a ƙauyen Kurmin Wali na jihar Kaduna, da ke arewa maso yammacin Najeriya a cewar Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).

    Shugaban ƙungiyar, reshen arewa, Reverend John Hayab ya bayyana cewa duk waɗanda aka sace sun koma gida lafiya, ba tare da biya kuɗin fansa ba.

    Shugaban CAN a Kaduna, Reverend Caleb Ma’aji, ya tabbatar da sakin waɗanda aka sace ga BBC.

    Ya ce gwamnan jihar ne zai tarbi mutanen a gidan gwamnatin jihar.

    Hukumomin gwamnatin Najeriya ba su yi magana kai tsaye game da sakin waɗannan mutane ba.

    Wannan harin na daga cikin jerin garkuwa da mutane da ke kara matsa lamba kan gwamnatin Najeriya.

    Najeriya ta fuskanci suka daga Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya zargi ƙasar da kasa daƙile abin da ya kira da "kisan Kiristoci."

    Rundunar Amurka dai ta kai hari kan abin da ta bayyana a matsayin matsugunan ‘yan ta’adda a ranar 25 ga watan Disamba.

    Gwamnati ta ce tana aiki tare da Amurka wajen inganta tsaro

  15. 'Jinkirin fitar da sunayen ƴan takara na iya haifar da rikici a Kano'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar zaɓe ta INEC a jihar Kano ta bayyana cewa ba ta da hurumin yin karin bayani kan takaddamar da ta kaure tsakanin jam’iyyun APC da NNPP kan gabatar da sunayen ‘yan takara guda daya a zaɓen cike gurbi na ‘yan majalisar dokokin jihar.

    Shugaban hukumar zaɓe reshen jihar, Ambasada Abdu Zango, ya ce, “hedikwatar INEC ce kaɗai ke da damar wallafa sunayen ‘yan takara da jam’iyyarsu,” inda ya bayyana cewa ba zai iya bayyana sunayen da jam’iyyun suka gabatar ba a wannan mataki.

    Ambasada Abdu Zango ya ƙara da cewa babban aikin reshen hukumar shi ne tattara bayanan ‘yan takara, haɗa rahoto, sannan a miƙawa hedikwatar hukumar don wallafa su.

    Ya ce nan gaba kaɗan, INEC za ta fitar da sunayen ta intanet domin jam’iyyun siyasa da al’umma su samu cikakken bayani.

    Masu sharhi kan harkar siyasa sun nuna damuwa cewa wannan jinkirin wallafa sunayen na iya haifar da karin rikici tsakanin jam’iyyun, musamman yayin da lokacin shirye-shiryen kamfen ke ƙaratowa.

    Wasu ‘yan siyasa na ganin INEC na bukatar ta hanzarta wallafa sunayen domin tabbatar da gaskiya da adalci a zaɓen cike gurbi.

  16. Jami’an LASTMA sun ƙwace motoci 27 a Legas

    ...

    Asalin hoton, Lastma/X

    Hukumar kula da harkokin zirga-zirga ta Jihar Legas, wato LASTMA, ta ce jami’anta sun ƙwace motoci 27 saboda abin da ta bayyana a matsayin ƙeta dokokin tuƙi da ke barazana ga tsaro a kan hanya.

    LASTMA ta ce matakin na zuwa ne domin daƙile yawaitar ɗora kaya fiye da kima a kan motoci, lamarin da ta ce ya zama ruwan dare kuma yana da haɗari.

    Hukumar ta ƙara da cewa ta shafe lokaci tana jan kunnen direbobi ta hanyoyi daban-daban kafin ɗaukar wannan mataki.

    A cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da wayar da kai na hukumar, Adebayo Taofiq, ya fitar ranar Alhamis, ya ce an gudanar da samamen ne da sassafe, inda jami’an suka kama motocin haya da na masu zaman kansu da aka samu suna karya dokokin ɗora kaya da ƙa’idojin tsaro.

    Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne sakamakon ƙarin damuwa game da haɗarin da motocin da aka ɗora wa kaya fiye da kima ke haifarwa, musamman a manyan hanyoyi da kuma titunan cikin birni da ke cike da cunkoso.

    Binciken da hukumar ta yi ya nuna abin da ta kira yanayi mai tayar da hankali, inda direbobi, musamman na motocin haya, ke ɗora wa motoci kaya iri-iri ba tare da la’akari da tsaro ba.

    Janar manajan hukumar, Olalekan Bakare-Oki, ya ce irin wannan ɗora kaya ya saba wa dokokin zirga-zirgar ababen hawa na jihar Legas, kuma yana jefa fasinjoji da sauran masu amfani da hanya cikin mummunan haɗari.

  17. 'Mahara sun turo wasiƙa kafin kai hari a Kwara'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura bataliyar soji zuwa sassan jihar Kwara, bayan mummunan harin da ya yi sanadiyyar kisan gomman mutane a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar.

    Shugaba Tinubu a wata sanarwa da kakakinsa Bayo Onanuga ya fitar ranar Laraba da dare ya kuma naɗa kwamandan da zai jagoranci rundunar sojin da za a tura jihar Kwara, wadda za ta gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya da aka yi wa laƙabi da 'Operation Savanna Shield'.

    Gwamnatin Najeriya ta ɗauki wannan mataki ne bayan harin da aka kai wa ƙauyen Woro, inda rahotanni ke cewa an tattara gawarwakin mutane 78 da maharan suka kashe.

    Hon Sa'idu Baba Ahmed, ɗan majalisar dokokin jihar Kwara ne, kuma ya shaidawa BBC cewa sun yi jana'izar sama da mutane 70 daga cikin waɗanda maharan suka kashe.

    Ya ce ''abin da dai na gani, waɗanda muka yi wa sallah, mutum 78 ne amma akwai waɗanda aka ƙone a cikin gidajensu, ba mu san adadin su ba tukun. An hallaka mutum zai kai 170.''

  18. Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta sake tura tawagar sa ido zuwa Tigray bayan ɓarkewar rikici

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta sake tura tawagar sa ido zuwa yankin Tigray na Habasha, bayan sabbin arangama tsakanin dakarun gwamnatin tarayya da mayaƙan Tigray, lamarin da ya tilasta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa yankin.

    A cikin wata sanarwa, sashen harkokin siyasa da zaman lafiya da tsaro na ƙungiyar ya tabbatar da cewa ƙwararru ƙarƙashin tsarin sa Ido da tabbatarwa da bin ƙa’ida sun koma birnin Mekelle domin ci gaba da sa ido kan aiwatar da Yarjejeniyar Pretoria.

    An rattaɓa hannu kan yarjejeniyar Pretoria a watan Nuwamban 2022 tsakanin gwamnatin tarayyar Habasha da ƙungiyar TPLF, domin kawo ƙarshen yaƙin Tigray da ya shafe kusan shekaru biyu, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da barnata dukiyoyi a yankin.

  19. Musulmai 75 aka kashe a harin Kwara - AbdulRazaq

    ...

    Asalin hoton, Kwara State Government

    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce "musulmai 75 ne aka kashe a harin da aka kai al’ummomin Woro da Nuku na jihar," yana mai bayyana cewa masu tsattsauran ra’ayin addini ne suka kai harin, ba ‘yan bindiga ba.

    Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X bayan ya kai ziyara yankin a daren Laraba.

    Ya ƙara da cewa Shugaba Bola Tinubu ya tura bataliyar sojoji zuwa jihar domin mayar da martani ga harin da kuma ƙarfafa tsaro a yankin.

    Hukumomin Najeriya sun kuma ɗora laifin harin kan ƙungiyar Boko Haram.

    A cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar domin miƙa ta’aziyya, ta la’anci abin da ta kira “mummunan hari na rashin imani.”

    Sanarwar ta buƙaci ƙarin haɗin kai tsakanin hukumomin tarayya da na jihohi domin tallafa wa al’ummomin da abin ya shafa, tare da tabbatar da cewa waɗanda suka aikata kisan gillar ba za su tsira daga hukunci ba.

    Ta ce "Shugaba Bola Tinubu ya nuna matuƙar fushi da alhini kan kisan da aka kai wa mutanen da aka yi ƙoƙarin tilasta musu tsattsauran ra’ayin addini. "

    Sanarwar ta ce" waɗanda aka kashe dukkaninsu musulmai ne."

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ma ta yi Allah-wadai da harin, tana mai cewa dole ne hukumomin Najeriya su gudanar da bincike mai zaman kansa da adalci, tare da ƙara ƙoƙari wajen kare rayukan jama’a.

    Yankin tsakiyar Najeriya na fuskantar ƙaruwar hare-hare a baya-bayan nan, ciki har da jihohin Neja da Kogi.

    Najeriya na fuskantar barazanar tsaro da dama a lokaci guda. A wani hari na daban a jihar Katsina da ke arewacin ƙasar, wasu ‘yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 21, a cewar mazauna yankin da ‘yan sanda.

  20. MDD ta yi gargaɗin barazanar nukiliya yayin da yarjejeniyar Amurka da Rasha ke ƙarewa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa ana tunkarar wani lokaci mai matukar haɗari ga tsaro, da zaman lafiyar duniya, yayin da yarjejeniyar sarrafa makaman nukiliya tsakanin Amurka da Rasha ke daf da ƙarewa.

    Antonio Guterres ya buƙaci Washington da Moscow da su gaggauta cimma matsaya kan sabuwar yarjejeniya, yana mai cewa ana cikin wani lokaci da haɗarin amfani da makamin nukiliya ya wuce ko wanne lokaci, cikin shekaru da dama da suka gabata.

    Yarjejeniyar ta iyakance kowace ƙasa ga samar da makami mai linzami mai cin dogon zango 1500.

    Rasha ta ce yanzu tana ɗauka cewa babu wata doka da ta iyakance ta, amma duk da haka, za ta yi abun da ya dace.

    Shugaba Trump ya riga ya ce yana son sanya China cikin kowace irin yarjejeniya a nan gaba.