Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya, Lahadi, 23/02/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sassan duniya kai tsaye, Lahadi, 23/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad da Isiyaku Muhammed

  1. Ƙasashen Sahel sun ƙaddamar da tutar ƙawance

    AES

    Asalin hoton, Burkina Faso Presidency

    Gamayyar ƙasashen Sahel da suka haɗa da Mali da Burkina Faso da Nijar sun ƙaddamar da tutar ƙawancen ƙasashen a birnin Bamako na Mali.

    Wannan matakin ya biyo bayan amincewar da shugabannin ƙasashen ƙungiyar suka yi a ranar 22 ga watan Fabrairu.

    An gabatar da tutar ce a wajen wani taro na ministocin ƙungiyar da aka kammala a yau Lahadi 23 ga wannan wata da muke cikin.

    Ministocin na AES ne suka ƙaddamar da tutar mai launin kore da kuma tambarin ƙungiyar a tsakiyarta.

  2. Zan iya haƙura da shugabancin Ukraine domin a samar da zaman lafiya - Zelensky

    Ukraine

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya haƙura da kujerar shugabancin ƙasar idan haka ne zai zama silar samar da zaman lafiya a ƙasarsa.

    Zelensky ya bayyana haka ne a daidai lokacin da aka cika shekara uku ana gwabza yaƙi tsakanin Ukraine da Rasha.

    "Idan kuna so in sauka daga mulki, zan amince. Amma ina so ƙasata ta shiga ƙungiyar Nato," in ji shi a lokacin da yake amsa tambayoyi a wani taron manema labarai.

    Wannan jawabin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya kira shi da "mai kama-karyar mulki ba tare da zaɓe ba."

    "Maganarsa ba ta ɓata min tai ba," in ji Zelensky wanda aka zaɓa a watan Mayun shekarar 2029.

    Zelensky ya ƙara da cewa tabbatar da zaman lafiyae ƙasar ne a gaban shi, amma ba ya tunanin daɗewa a mulkin ƙasar.

    Majalisar Ukraine ce ta dai yi dokar hana zaɓe a ƙasar tun bayan da Rasha ta faɗa mata da yaƙi a watan Fabrairun 2022.

    Shugabannin ƙasashen turai da na wasu ƙasashen za su yi taro a birnin Kyiv na Ukraine domin nuna goyon baya, tare da haɗin kansu ga ƙasar.

  3. Wanda ake kyautata zaton zai zama shugaban Jamus ya yaba da zaɓen ƙasar

    Jamus

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutumin da ake kyautata zaton zai zama shugaban gwamnatin Jamus na gaba ya yaba da nasarar da jam'iyyarsa take samu a zaɓen ƴan majalisar dokokin ƙasar.

    Friedrich Merz ya buƙaci a gaggauta kafa gwamnati, bayan ƙuri'ar jin ra'ayin jam'a ya nuna jam'iyyarsa ta Christian Democrats da ƙawarta ta Bavaria ke kan gaba da kusan kashi 29 cikin ɗari.

    Ƙuri'ar ta nuna cewa jam'iyyar Alternative for Germany a matsayin ta biyu, da kaso mafi girma na ƙuri'u da ta taɓa samu a zaɓen ƙasar, inda take da kusan kashi 20 cikin 100.

    Da alama za ta doke jam'iyyu biyu da ke cikin ƙawancen marasa rinjaye a halin yanzu --Jam'iyyar shugaban gwamnati Olaf Scholz ta Social Democrats da Jam'iyyar Greens.

    An samu fitowar jama'a da dama da suka kaɗa ƙuri'a a zaɓen, bayan yaƙin neman zaɓe da ya janyo rarrabuwar kawunan al'umma a ƙasar.

  4. Gwamnatin Sudan ta ce ta ƙwace iko da birnin El-Obeid

    Sudan

    Asalin hoton, AFP

    Sojojin Sudan sun ce sun kawo ƙarshen farmakin da dakarun RSF suka yi na kusan shekara biyu a Birnin El-Obeid, hedkwatar lardin Kordofan ta Arewa.

    An ga sojojin gwamnati suna murna bayan buɗe babbar hanyar shiga birnin, wanda aka fara kai wa hari tun bayan da yaƙin basasa ya ɓarke wata 22 da suka gabata.

    Wakilin BBC ya ce manazarta dai na ganin wannan farmaki a matsayin gagarumar nasara ga sojojin ƙasar da ke ci gaba da samun galaba a cikin ƴan makonnin nan.

    Rikicin dai ya raba ƙasar Sudan biyu, inda sojoji ke riƙe da yankunan arewaci da gabashin ƙasar, sannan ƙungiyar RSF ce ke riƙe da mafi yawan yankunan Darfur da kuma wasu sassan kudancin ƙasar.

  5. Gwamnatin jihar Sokoto ta fara biyan malaman firamare mafi ƙanƙantar albashi

    Sokoto

    Asalin hoton, Others

    Makonni uku bayan wani rahoton da BBC ta yi game da ƙorafin da malaman makarantun firamaren jihar Sokoto suka yi na rashin biyansu sabon albashi mafi ƙanƙanta na naira 70,000, gwamnatin jihar ta biya su, har ma da yi musu ƙari.

    Malaman makarantun firamaren sun shaida wa BBC irin farin cikin da suka ji game da alƙawarin da gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya cika, na biyansu sabon albashin kamar kowa tare da sauran ma’aikatan gwamnatin jihar da suka hada da na kananan hukumomi 23.

    Mai magana da yawun gwamnan jihar, Abubakar Bawa, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ta saurari ƙorafin da ma’aikatan suka yi ne, shi ya sa ta cika alƙawarin da ta ɗaukar musu tun da farko.

    A watan Yulin shekarar 2024 ne, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da ƙara albashi mafi ƙanƙanta ga ma'aikatan ƙasar daga naira 30,000 zuwa 70,000.

  6. Wane ne Aristotle shahararren masanin falsafa na duniya?

    Aristotle

    Asalin hoton, Getty Images

    Shin a iya cewa Aristotle ne mutumin da ya fi tasiri da aka taɓa gani a doron ƙasa? Wani fitaccen malamin falsafa ɗan Birtaniya, John Sellars na ganin haka.

    Ya ce ana iya ganin tasirin masanin falsafar ɗan asalin Girka a fagage da dama da irin yadda ya taimaka da tunaninsa a fannoni daban-daban na rayuwa.

    Kama daga fagen siyasa da kimiyya, rubuce-rubuce zuwa tunani da dabaru, ana iya ganin tasirin Aristotle a ko'ina.

    Ya yi nazarin ilimin halittun cikin ruwa, wani abu da ya haifar da ilimin 'Biology'.

  7. An yi jana'izar tsohon shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah

    Nasrallahi

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Gawarwakin Nasrallahi da Safieddine

    Dubban mutane ne suka hallara domin jana'izar tsohon shugaban ƙungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah, wanda Isra'ila ta kashe a birnin Beirut na ƙasar Lebanon a watan Satumban bara, da Hashem Safieddine, wanda zai maye gurbin Nasrallah ɗin, amma shi ma aka kashe shi kafin ya fara aikin jan ragamar ƙungiyar.

    An gudanar da taron jana'izar ne a wani filin wasa na Camille Chamoun Sports City mai cin mutum dubu 50 da ke gefen birnin a yau Lahadi.

    Nasrallah, wanda ya shugabanci ƙungiyar Hezbollah na sama da shekara 30, yana cikin mutanen da ake ganin suna da matuƙar tasiri a yankin Gabas ta Tsakiya .

    Awanni kaɗan kafin a gudanar da jana'izar ne Isra'ila ta kai wani hari ta sama a kudancin Lebanon, inda ta ce ta kai harin ne kan wasu rokokin Hezbollah.

    Ɗaya daga cikin waɗanda suka halarci jana'izar, Umm Mahdi mai shekara 55 ya bayyana wa kafar AFP cewa jana'izar ce "abin da za mu iya yi masa," saboda yadda "ya sadaukar da komai," domin wannan fafatuka.

  8. Isra'ila za ta tura ƙarin sojoji yankin Jenin na Falasɗinawa

    IDF

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta sanar da shirinta Na faɗaɗa aikin sojinta a yankin gaɓar yamma da tekun Jordan da ta mamaye.

    Daga ciki wuraren da za ta tura tankokin yaƙi har da Jenin wanda yanki ne na Falasɗinawa.

    Wannan ne karon farko a cikin sama da shekara 20 da Isra'ila ta aika tankokin yaƙi zuwa yankin Jenin ɗin duk da yaƙin da ake gwabzawa.

    A cewar sanarwar rundunar sojin Isra'ila ta IDF ta fitar, ta ce tuni sojojin suka fara tafiya zuwa ƙauyukan Jenin a wani shiri da ta kira yaƙi da ta'addanci.

  9. Ɗan arewacin Najeriya da ya shiga kundin Guinness saboda ɗaukar hoto

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

    AbdurRahman Sa'idu, ɗan asalin jihar Yobe, da ke arewa maso gabashin Najeriya ya ce ya shiga gasar samun wannan kambi na bajinta na Guinness ne saboda a Najeriya musamman yankin arewa akwai abubuwa da dama na tarihi da ilimantarwa da ya kamata duniya ta gani ta sani amma ba a yin hakan, tare kuma da sanya wa matasa sha'awar sana'ar ɗaukar hoto.

    Ya ce ya gamu da ƙalubale wajen shirya wa shiga wannan gasa, da ya ɗauki hotuna 897 a cikin sa'a ɗaya inda ya yi wajen shekara ɗaya, tun daga 2023 zuwa watan Satumba na 2024, yana shirin yadda zai shiga.

    Matashin ya ce bayan wannan bajinta da ya yi a yanzu zai yi ƙoƙarin inganta sana'ar tashi ta yadda zai yi ƙoƙarin shiga harkokin ɗaukar hoto a duniya domin ƙara ciyar da likkafarsa da ma ta Najeriya musamman arewaci gaba.

  10. Minista ya yi barazanar barin APC idan ba a sauya shugabancinta na Kano ba

    Ata

    Asalin hoton, Sanata Bashir Lado/Facebook

    Minista a ma'aikatar gidaje, Yusuf Abdullahi Ata ya yi barazanar cewa shi da magoyansa za su iya ficewa daga jam'iyyar APC a Kano, matuƙar ba a canja shugabancin jam'iyyar a jihar ba.

    Ministan ya ce furucin jagoran jam'iyyar ne ya jawo faɗuwar jam'iyyar a zaɓen da ya gabata na 2023, kamar yadda ya bayyana a wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafofin sadarwa, wanda aka ce ya yi a taron masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumarsa ta Fage a jihar Kano.

    Ata ya ce, “muna faɗa wa kowa, idan aka mayar da irinsu, duk irinmu fita za mu yi."

    Ya ƙara da cewa, "mu an mana tarbiya, mun san waye malami, mun san waye babba. Saboda haka ba za mu sauka daga turbarmu ba. Idan suka dawo da shi, mu za mu fita, kuma na rantse da Allah sai jam'iyyar ta sake faɗi zaɓe," in ji shi.

    "Dole a canja, dole a nemo mutanen kirki masu mutunci a ba su saboda ya zama tare da mu, ya yi sha'awar ya sake ba mu."

  11. Mutum huɗu sun mutu goma sun ji rauni a wata motar bas da ta ƙone a jihar Jigawa

    Motar bas na cin wuta

    Asalin hoton, NPF

    Mutane huɗu sun ƙone ƙurmus wasu goma kuma sun ji raunuka yayin da wata mota ƙirar bas (Hummer) ta kama da wuta a garin Gwaram da ke jihar Jigawa.

    Lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 4 na yamma, a jiya Asabar a kusa da makarantar sakanadare ta haɗaka ta gwamnati ta 'yammata da ke garin na Gwaram (Government Girls Unity Secondary School )

    Wata sanarwa da kakakin 'yansanda na jihar SP Lawan Adam ya fitar a yau Lahadi ta nuna cewa motar ta tashi ne daga ƙaramar hukumar Zaki ta jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke ƙaramar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa.

    Sanarwar ta ce, ''motar na ɗauke ne da fasinja 44, da suka haɗa da manya 25 da yara 19.''

    Kakakin 'yansandan ya ce, wutar ta kama ne sakamakon katifa da aka ɗaure a bayan motar da ke kusa da salansa.

    Sanarwar ta ƙara da cewa mutum goma da suka ji rauni an kai su asibitin Gwaram yayin da sauran aka yi nasarar tserar da su daga motar ba tare da wani rauni ba.

    Waɗanda suka rasun kamar yadda sanarwar 'yansandan ta nuna su ne Zuwairah Hassan, mai shekara 40 da Fatima Hassan, mai shekara 5 da Iyatale Hassan mai shekara 3 da Halima Muhammad mai shekara 10, dukkanninsu daga ƙauyen Saldiga da ke yankin ƙaramar hukumar Zaki.

  12. Ƙungiyar RSF ta ƙulla yarjejeniyar kafa kishiyar gwamnati a Sudan

    Tawagar ƙungiyar RSF da abokansu a wajen taro a Nairobi

    Asalin hoton, Reuters

    Manyan shugabannin ƙungiyar RSF da ke yaƙi da sojojin Sudan, sun ce sun ƙulla yarjejeniya da suka sanya wa hannu, tare da ƙungiyoyin siyasa da masu gwagwarmaya da makamai da tasu ta zo ɗaya, don kafa gwamnatin hamayya.

    Kungiyar ta RSF ta kai kusan shekara biyu tana yaƙar rundunar sojin Sudan, wadda a da tare suke.

    Yaƙin ya yi sanadiyyar mutuwar dubban jama'a da raba miliyoyi da muhallinsu.

    Waɗanda ke da hannu a yarjejeniyar sun sheda wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, yarjejeniyar ta tanadi kafa gwamnatin zaman lafiya da haɗin kai a yankunan da ke hannun RSF da ƙawayenta.

    An soki shugaban Kenya sosai saboda bayar da damar zaman ƙulla yarjejeniyar a babban birnin ƙasarsa, Nairobi.

  13. Afirka ta Kudu ta sake faɗawa matsalar ƙarancin wutar lantarki

    Wani mutum da wutar kyandar a cikin duhu

    Asalin hoton, Reuters

    Kamfanin samar da wutar lantarki na gwamnatin Afirka ta Kudu mai fama da bashi, Eskom, ya sake komawa matsalar ɗauke wuta har sai abin da hali ya yi.

    Da sanarwar hakan yanzu miliyoyin masu amfani da wutar lantarkin za su riƙa rasa ta, bayan kusan shekara ɗaya suna samun wutar ba tare da wata matsala ba.

    Kamfanin ya ce lalacewar kayansa a wasu tashoshin samar da wutar guda uku ce ta haddasa matsalar.

    A dalilin hakan yanzu wasu yankunan sukan kai kamar sa'a takwas ba tare da wutar lantarkin ba.

    Eskom yana samar da yawancin wutar ne daga na'urorinsa ma su amfani da kwal, waɗanda sun tsufa.

    Kamfanin ya gamu da matsala ta shekara da shekaru ta rashin zuba jari da bunƙasa shi da kuma rashin alkinta dukiyarsa.

  14. Isra'ila ta kai hare-hare Lebanon sa'o'i kafin jana'izar shugaban Hezbollah, Nasrallah

    Wajen harin Isra'ila da ya kashe Hassan Nasrallah

    Asalin hoton, Joel Gunter/BBC

    'Yan sa'o'i kafin jana'izar marigayi shugaban ƙungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah, a Beirut, Isra'ila ta kai hare-hare ta sama a kudancin Lebanon.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta hari makaman harba rokoki ne , waɗanda ta ce an matsar da su daga inda suke abin da ta ce ya saɓa wa yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta ta shekarar da ta wuce.

    A Beirut ɗin babban birnin na Lebanon, dubban jama'a ne masu makoki suka taru, ciki har da wata babbar tawaga daga Iran, babbar mai tallafa wa Hezbollah, domin jana'izar ta Nasrallah.

    A watan Satumba ne Isra'ila ta kashe Nasrallah a wani babban hari da ta kai ta sama.

    Tsawon shekara talatin yana jagorantar ƙungiyar ta Shia, inda ya bunƙasa ta, ta zama mai ƙarfin gaske a ɓangaren soji da kuma siyasa.

  15. An kashe mutum ɗaya da raunata 'yansanda a harin wuƙa a Faransa

    'Yansanda da 'yanjarida a wajen da aka kai harin wuka

    Asalin hoton, Getty Images

    An kashe mutum ɗaya tare da raunata 'yansanda uku a wani harin wuƙa da aka kai a birnin Mulhouse na gabashin Faransa.

    An kama wani ɗan ƙasar Aljeriya mai shekara 37 a wajen, kuma mai gabatar da ƙara ya buɗe bincike kan laifin ta'addanci saboda an ji wanda ake zargin na ɗaga murya da cewa "Allahu Akbar".

    Mutumin ya ji wa 'yansanda biyu rauni sosai, ɗaya a wuya ɗayan kuma a ƙirji.

    Sannan wani ɗan ƙasar Portugal mai shekara 69 da ya nemi kai ɗauki, ya mutu bayan da maharin ya caka masa wuƙa.

    Wanda ake zargin na fuskantar fitarwa daga ƙasar ta Faransa saboda sunansa na cikin waɗanda ake ganin suna da alaƙa da ta'addanci, in ji mai gabatar da ƙara da birnin.

    Shugaban ƙasar Emmanuel Macron wanda ya bayyana ta'aziyyarsa ga iyalan wanda ya mutu da jajanta wa waɗanda aka ji wa rauni ya ce ba shakka wannan hari ne na masu tsananin kishin Islama.

    Kuma ya ce ba za su sassauta ba wajen kawar da ta'addanci a ƙasarsu.

    An kai harin ne jiya Asabar da ƙarfe uku na rana agogon GMT a kusa da wata kasuwa da ke tsakar hada-hada a birnin na Mulhouse, da ke kusa da iyakar Jamus da Switzerland.

  16. Hamas ta zargi Isra'ila da neman gurgunta yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta da gangan

    Falasɗinawa na zaune

    Asalin hoton, Getty Images

    Hamas ta zargi Isra'ila da neman gurgunta yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta hanyar kin sakin Falasdinawa fursunoni da gangan bayan ita Hamas din ta saki 'Yan Isra'ila shida daga cikin wadanda take garkuwa da su jiya Asabar.

    Wata sanarwa da Hamas din ta fitar daga Ezzat El Rashq, mamba a cikin majalisarta ta siyasa ta ce, abin da Isra'ila ta yi saba yarjejeniyar ne karara.

    Isra'ila ta dakatar da sakin Falasdinawan 602 da aka tsara musayarsu da 'yan Isra'ila shida a jiya Asabar, har sai abin da hali ya yi.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya yi suka ga abin da ya kira dabarar amfani da sakin wadanda aka yi garkuwa da su domin farfaganda, da kuma taro na nuna cin zarafi.

    Gwamnatinsa ta ce ba za ta sake sakin Falasdinawa fursunoni ba har sai an ba ta tabbacin sakin 'yan kasarta na gaba.

  17. Ana zaɓe mai zafi a Jamus wanda ya ɗauki hankalin Turai da Amurka

    'Yansiyasar Jamus

    Asalin hoton, Reuters

    Masu zaɓe a Jamus sun fara hallara domin kaɗa ƙuri'arsu a zaɓen ƙasar bayan yaƙin neman zaɓe mai zafi da aka yi wanda batun koma-bayan tattalin arziƙin ƙasar da kuma wasu jerin hare-hare da aka yi suka sa bataun ɓaki da shige da fice suka ɗauki hankali sosai fiye da komai.

    Friedrich Merz, mai shekara 69 kuma mai ra'ayin riƙau shi ne ake ganin zai iya yin nasara ya zama shugaban gwamnatin Jamus ɗin ta gaba, a wannan zaɓe da Amurka da Turai suka zuba wa ido.

    Mista Merz ya yi alƙawarain gyara komai a cikin shekara huɗu - a ƙasar da ita ce mafi ƙarfin tattalin arziƙi a Turai, wadda kayayyakin jin daɗin jama'a suka yi baya.

    Idan har jam'iyyar Merz wato Christian Democrats (CDU) ta yi nasara, to zai buƙaci ya yi haɗaka da aƙalla jam'iyya ɗaya, wataƙila ta Olaf Scholz, Social Democrats, wadda gwamnatinta ta ruguje a shekarar da ta wuce.

  18. Buɗewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Lahadi 23 ga watan Fabarairun 2025.

    Za mu kasance da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu da sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo, har ma ku yi muhawara.

    Mu fara da wannan karin maganar - Wanda ya ɗau babban kashi ba ruwansa da gyara